DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO
SHAFI NA DAYA (1)
©️HAFSAT RANO
ALKALAMI TV
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
WATTPAD: HafsatRano
MAFARIN KOMAI.
A guje ta fito daga dakin jikin ta cikin shigar kayan ma’aikatan jinya, da sauri duk suka mik’e ganin ta nufo su
“Ta sauka Dr!” Suka tambaya a rude kuma a tare
“Ina maigidanta?” Ta maida musu ba tare da ta amsa tambayar tasu ba.
Matsowa yayi da sauri yace
“Gani.”
“Ok muna so ka saka hannu ne, ba zata iya haihuwa da kanta ba dole sai dai ayi mata aiki.”
“Innalillahi, aiki kuma Dr?” Ya tambaya a kideme
“Shine kadai abinda zamuyi mu ceto rayuwarta data abin cikin ta. Kayi hakuri babu lokaci.”
“Shikenan, Allah sa ayi a sa’a.”
Bin bayan ta yayi, suka je ya saka hannu sannan ya dawo wajen sauran ya tsaya yana kaiwa da komawa.
Bayan shafe tsawon mintuna arba’in da shigar su ta sake fitowa, wannan karon akwai alamun nasara a tattare da ita. Kafin ta k’arasa garesu sukayi saurin isa, fuskar su dauke da alamun tambaya, hannun ta ta mika alamun abata tukwuici kafin tace
“Congratulations Your highness, an yi nasarar ciro muku dan saurayi.”
Da sauri ya kalle ta kamar be ji me tace ba, gid’a masa kai tayi alamun gamsarwa, maida kallon sa yayi wajen sauran da duk fuskokin su ke cike da farin ciki yace
“Alhamdulillah ya ALLAH!” Ya furta da karfi
A duniya bashi da wani buri da ya wuce yaga an haifa masa d’a namiji, yau sai gashi Allah ya cika masa burin sa, ba ma shi ba, duk wani makusancin sa yana masa sha’awar haka. Duba da irin tarin dukiyar da Allah ya bashi. Ya hakura ya barwa Allah zabin sa, sai gashi ya bashi a lokacin da beyi zato ko tsammani ba.
A take wajen ya kaure da murna, babu wanda ya tsaya tambayar lafiyar mahaifiyar, tuni kowa ya hau kokarin kiran waya domin sanar da yan’uwa da abokan arziki.
THE ONE AND ONLY HEIR To MARWAN DIKKO FAMILY IS BORN.
A daidai lokacin Inno na kwance a gadon asibitin, babu tazara tsakanin dakin da take da babban dakin da aka ajiye Matar Alhaji Marwan, saboda haka tana jiyo hayaniyar mutane me cike da tsantsar farin ciki, kallon jaririyar dake kwance kusa da ita tayi, zuciyar ta tayi rauni, anya? Anya bata zalunci yarinyar ba kuwa? Kallon gefen ta tayi taga jakar da aka hado mata tare da jaririyar, soyayyar ta da kudi abu ne me girma, babu abinda ba zata iya aikatawa akan su ba, sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo gaba, gashi babu ko digon soyayyar yarinyar a zuciyar ta. Abu daya ta sani shine rayuwar jaririnta, rayuwa me inganci da tsananin gata da zai taso da ita. Idan ta tuna wannan sai ta ji ta samu sauki, sai dai fa tana da kudurin komai daren dadewa sai ta karbo shi.
Shigowar su Yalwati da sauran jama’a ne yasa ta ɗan saki ranta, suka shiga daukar jaririyar kowa yana yaba kyawun ta, ita dai Inno jin su kawai take ba tare da ta tanka ba, ganin zasu cigaba da chaja mata kai da hayaniyar su yasa ta rufe idon ta alamun bacci take yi, hakan ya bata damar cigaba da yin tunanin da take akan wannan babban al’amari ne cike da tarin matsaloli a gaba.
Hmm
AMINATU
Kowacce rayuwa cike take da kalubale, sai dai ni tawa rayuwar da wani salon na sarkakiya tazo min.
Rayuwa ta cike take da abubuwa masu yawa. Duk da haka bazan ce nafi kowa shiga matsin rayuwa ba, sai dai ina da tabbacin ina cikin sahun farko na mutanen da za’a kirasu da wanda rayuwa tayi Daurin Goro.
Eh daurin da nake tunanin babu wani mahalukin da zai iya warwareshi, na riga na sare, na barwa Allah ikon sa, ina kuma kyautata zaton zai kawo min yankewar sa kafin barin numfashi na. Ajiyar zuciya na sauke ina bitar Rayuwa ta daki-daki kamar a lokacin komai yake faruwa.
Zaune nake a faffad’an tsakar gidan mu wanda ke dauke da dakuna hudu falle falle sai madafi daga gefe, randunan ruwa manya, daga dayan bangaren rijiya ce babba da makewayi a gefenta, gidan gidane babba daya hada da mutane da yawa sai dai kowa yana ɓangaren sa inda babban zauren gidan shi ya haɗa kowa da kowa.
Dakin farko ya kasance dakin Baba, sai dakin Inno daga chan gefe, dakin yara matan gidan ne a kusa dana inno, daga dayan barin dakin Yalwati ne sai dakin samari dake daura da hanyar fita daga shashen namu.
Tsintar shinkafa nakeyi tun kafin rana ta fito gashi har ina neman makara ban samu na gama ba, a gurguje nakeyi saboda lokacin makaranta kar na makara, cikin sa’a na kammala nayi saurin zubawa a ruwan waken dake ta tafasa bayan na tabbatar da dahuwar waken saboda gudun abinda zai je yazo. Gyara wutar nayi ganin ta fara zarewa na karasa gaban rijiya domin yin kwaskwarima. Cikin sauri sauri na zura uniform d’ina wanda duk ya tsofe wani wajen ma ya yage na sake fitowa, lokacin har yaran gidan sun fara fitowa ana layin alwala. Haka dabi’ar gidan mu take, tun tasowa ta kawo yanzu hakan bata chanja zani ba, kafin su gama alwalal sai sunyi fada kashi dari. Murmushi kawai nayi na fada dakin Inno dan gaishe ta, a tsaye na ganta tana kokarin daura dankwali tana ganina ta tsaya.
“Ina kwana Inno.?” Na durkusa har kasa kamar ko yaushe. Bata amsa ba sai kallon kayan jiki na da tayi kadan kafin tace
“Kin gama aikin naki ne da zaki wuce makaranta?”
“Eh.” Nace ina kallon ta.
“Kin zuba ko kin gama?”
Iya sani na Karime ke karasa wa idan na zuba, tun da ita ba makarantar take zuwa ba, a darare nace
“Na zuba karasawa kawai zatayi a kwashe Inna.”
Dan bata fuska tayi tana yatsine baki kafin tace
“Jeki jira ta karasa yau babu me karasa miki Karime bata jin dadi.”
“Toh.”
Kawai nace na mike jiki a sanyaye na koma bakin dakin mu na zauna ina kallon yadda rana ta d’aga sosai alamun na makara, ina nan zaune kowa ya fito aka hau hada-hadar shan koko, ban bi ta kai ba ni dai buri na na ganni a makaranta. Sai bayan wajen rabin awa sannan na kammala na sake dauraye kafata na fice daga gidan da sauri kafin Inno ta ankare ta kawo abinda zai hana ni zuwa duk kuwa da na kan yi mamakin dalilin da yasa inno take bari na zuwa makaranta, bayan haka bama kowa ne a yaran gidan ke samun zuwa makarantar ba.
A babban zauren gidan naci karo da Nura, da alama lokacin zaiyi sallah, gaishe shi nayi na wuce ba tare da jiran amsar sa ba.
Tafiya ce mai tsawo kafin ka isa makarantar guda daya jallin jal dake a kauyen, Kamar kullum babu malamin daya shigo har nazo, haka dabi’ar makarantar take, a rana sai ka samu malami daya ne kawai zai shiga duk suna zaune a staff room suna hira, a haka dai muke dan samun abinda muke samu wanda bamu da tabbacin daidai suke koya mana sai dai saboda ba gane wa zamuyi a lokacin ba yasa muke binsu a haka. Musamman ma ni da na taso da son karatu da kuzun zama wani abu a kauyen namu tun bayan ganin da nayi wa jikokin mama Ladi makociyar mu dake zaune a birni, sun kawo mata ziyara, tun daga lokacin na sawa raina zama kamar su, sai dai hakan ba mai yiwuuwa bane duba da irin gidan dana taso.
Haka rayuwa ta cigaba da garawa, babu abu daya daya sauya na daga al’adun gidan mu, tun da na taso nasan Inno ita ke ciyar da gidan mu ko nace shashen mu, shiyasa ko babanmu baya mata musu, Yalwati kuwa ta zama kamar ba kishiiyar ta ba, dan bayan na gama girkin shinkafa da waken da karime take fita dashi wajajen sha biyun rana, Yalwati ce zata dora alala, sannan tayi dambu da wake shima a sake fita dashi, duk kuma jarin na Inno ne.