DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Gashi nan, tun da kalar rayuwar daka zaba ma kanka kenan.”

Da sauri ya kalli daddyn, sanin hakan me yake nufi ne yasa ya hau rokon sa

“Daddy dan Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi ban aikata abinda ake zargi na dashi ba.”

Da wani mugun kallo ya dube shi

“Ni sa’an ka ne Farouk? Ko ka fara shaye-shayen ne dai da gaske?”

“Wallahi ban taba shan komai ba, ka saurare ni kadai nayi maka bayani, wallahi bani da laifin komai.”

“You must be a fool, nace baka da hankali sam, idan har kana ganin zan tsaya sauraran ka bayan da kanka ba wani ya matsa bakin ka ba ka amsa laifin ka a gaban kowa, sannan yanzu kazo min da wani banzan zancen ka, toh kayi karya wallahi.”

Riko ƙafafuwan sa yayi da sauri yana sake sakin kuka

“Wallahi ban aikata ba, bansan me ya hau kaina ba na amsa, dan Aallah Daddy kar kuyi min haka.”

Buge hannun sa yayi ya janye ƙafarsa yana matsawa.

“Idan ka gama haukan naka zamu wuce.”

“Daddy ka taimaka min, maganar karatuna fa dan Allah, wallahi ban aikata abinda kake tunani ba, taimakon ta kawai nayi, wanda na dauke ta tamkar Amal.”

Tsaki Daddy yaja, ya gaji da jin wannan shirmen nasa, bashi da lokacin da zai kara batawa ya saurare shi, duk wata hujja tasa bata da amfani tun da be kawo ta a lokacin da ya kamata ba, ko a gaban alkali ne to Tabbas ya tabbata mai laifi tun da har yayi saurin amsawa. Duban shi yayi, baya so ya karya masa zuciya, saboda haka ya nuna shi da hannun sa

“Kai yanzu ai na gama da kai, ba zan iya tsayawa sauraren shirmen ka ba. Maganar karatu kuwa in kana so zaka iya neman admission ka soma karatun anan, kar dai ka manta akwai responsibilities na matar ka kanka, so you have to be very careful.”

Hannu ya watsa baya ya juya cikin takun kasaita ya fada mota, Amal ce suka fito da Dada tana kuka sosai akan dole ba zata tafi ba, da sauri ya rarrafa gaban Dadan yana sakin kuka me tsuma rai.

“Dada kiyi min rai dan Allah, Daddy ya dau zafi sosai yaki saurarata.”

Dago shi tayi ta bude kofar falon ta tura shi ciki ta rufe, motar ta nufa rike da hannun Amal, daddy na ganin haka ya fito.

“Ka barta ta zauna tare dani har zuwa lokacin da za’ayi resuming makarantar su, sai azo a tafi da ita dan Allah.”

“Duk yadda kika ce haka za’a yi, mu zamu wuce.”

“Allah ya kiyaye hanya, ka kara nazari akan hukuncin da ka yanke wa Babana, duk abinda ka shirya sai ka sanar min a waya.”

“Shikenan in Sha Allah.”

Matsawa baya sukayi motocin suka fice daya bayan daya, ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannun Amal suka juya ciki.

Kaiwa kawai yake da komowa a tsakiyar falon, yana jin an bude yayi wajen ta da sauri ya fada jikinta yana sakin kuka. Bata hana shi ba, tasan zuciyar sa a cunkushe take kukan kadai zai rage masa radadin da yake ji. Ya dau lokaci sosai yana kokawa da zuciyar sa, yana jin kamar ya hadiye ta ya huta da radadi da zafin da take masa, a hankali ta fara sanyi sakamakon addu’ar da yaji Dadan na tofa masa, da sauri shima ya kama yana karanto innalillah wa inna ilaihi raji’un. Sosai hakan yayi masa tasiri kwarai, zamewa yayi ya zauna akan tiles yana sauke kansa kasa.

“Babana…”

“Tashi ka shiga kayi wanka ka gyara jikin ka, dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma komai zai warware cikin ruwan sanyi. Ka cigaba da addu’a.”

Be musa ba, illa mik’ewa da yayi yana nufar dakin sa cikin tafiyar da tafi kama da wanda ya kwanta jinya me tsawo.

***Ina kwance yau ma kamar ko yaushe tun barowar mu asibiti bana iya aiwatar da komai sai abinda Inno tace, komai yimin ake abinci ma sai ta bani a baki, shigowa tayi tana tura kyauren dakin namu, gefen da muke ajiye kayan mu ni dasu Karime ta nufa, ta jawo ledar kayana ta fito dasu, set uku ne an wanke su sai hijabi daya da mayafi yellow, wata ledar sabuwa da alamun ita ta shigo da ita ta bude ta zuba kayan, takalmi na guda daya samfurin sukwal ta jawo shima ta saka min, sai dan kunne da sarka duk suma na sallah ta ne, ina kallon ta har tapp gama tana jan tsaki.

“Tashi kije ki watsa ruwa maza.”

Mik’ewa nayi na amsa da toh na nufi bayin dake tsakar gidan mu, su Hanne na gani da su Karime sun cin kwalliya sun sa sababbin kayan su na sallah, kamar na tsaya yi musu magana sai kuma na fasa na shiga wankan. Mintuna kadan na fito na sake wucesu na shige ciki, da hannu Inno ta nuna min kayan dake ajiye a gefen tabarmar dakin. Dauka nayi na saka na koma na zauna ina tunanin inda zamu ake ta wannan shirin. Fita tayi ta barni a nan, ina ta jiyo hayaniyar yaran gidan sama sama, da gudu naji karime ta shigo gidan tana kiran Inno

“Ga motar chan tazo Inno.”

“Naji me bakin aku.”

Ta katse ta tana hararar ta, mamaki ne ya kamani, yau Inno ce ke cewa karime me bakin aku, lallai ba karamin bacin rai take ciki ba. Shigowar ta dakin ne yasa nayi saurin kallon ta

“Tashi maza ku kama hanya, saura inji ko in gani, ba dadewa zakiyi ba zaki dawo.”

Da sauri nace

“Ina zani Inna?”

“Ban sani ba, tashi nace ki wuce suna jiran ki.”

Tashi nayi jiki a sanyaye na fito tsakar gidan, Yalwati da Babar su Hanne na gani a tsaye duk sun sha lullubi, kamoni sukayi muka nufi kofar fita daga gidan. Motar dake ajiye a waje aka bude mana muka shiga, sai a lokacin naga Hanne da Karime a gaba, ajiyar zuciya nayi na ɗan ji sauki tun da bani kadai bace. Ina ji aka tashi motar muka dau hanya. Wannan tafiyar tana daya daga cikin shafukan rayuwa ta da bazan taba mantawa ba.

Rano ????   ©️®️HafsatRano

ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                    (7)

***Tafiya kadan mukayi muka isa gidan, da mamaki nake kallon gidan, gidan da nake da muradin zuwa a koyaushe, murna na hau yi Yalwati tayi saurin hararata, da sauri na nutsu, aka bude mana bayan motar ta gama daidaita a harabar gidan da nake wa kallon aljannar duniya. Tsallen murna su Karime suka hau yi Yalwati ta daka musu tsawa, sum sum sum suka dawo bayan ta suka makale, kofar dake kallon mu wanda ya kawo mu ya nuna mana.

“Bismillah hajiyan na ciki ai.”

Sake riƙe ni gam sukayi muka nufi kofar, kafin mu karasa aka budo kofar aka fito, matar nan ce ta asibiti, da fara’a ta tarbemu,tayi mana iso cikin falon, wani irin azababben sanyi me hade da sanyayyen kamshi ya kaiwa kofofin hancin mu ziyara, ina kallon Babar su Hanne na sake bude kofofin hancin ta sosai tana shaƙar iskar da tayi mana maraba, duk muka rabe a kasa nida su Karime, aka shiga gaisawa cikin mutuntawa. Nidai ina ta son kallon ko ina a falon amma babu dama saboda yadda Yalwati ke kara rufa min fuskata, bansan dalilin da yasa take min hakan ba, bayan na ga su Karime da Hanne an bar su suna ta shan kallon su. Ina ta hasashen ina ma nice na more kallon nan. Chan na kurawa katotuwar talabijin din dake girke a bango ido ta cikin mayafin duk da ba wani sosai nake gani ba, wasu mutum biyu babba da yar matashiya suka shigo dauke da manya manyan farantai, ina kallo suka dire gaban mu aka sake gaisawa sannan suka juya suka fice.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button