DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Bismillah ga abinci.” Matar ta fada tana nuna wa su Yalwati kwanukan da aka jere a gaban mu, wanda tuni kamshin ya fara sawa na manta yanayin dana baro, ina ji na kamar babu sauran damuwa ko takura a cikin rayuwa ta. Kamar su Yalwati ba zasu ci abincin nan ba, ina ta addu’a har sai dana ji matar ta sake musu magana, sannan suka sauko kowa ta hau diba dan dama nasan kawai kara sukayi wanda ni sam ban san su da ita ba.
“Amal!” Ta bud’e muryar ta tana kwala mata kira, da sauri ta shigo, turus tayi ganin baki taki karasowa
“Ƙaraso mana kika tsaya.”
Shigowa tayi tana sake kallon mu.
“Ga kawar ki nan rike ta ku shiga ciki.”
Hannu na ta kama, muka bar falon, mayafin na cire muna yin gaba, kallo na tayi tace
“Laaaaa Aminatu.”
“Na’am.” Nace mata ina murmushi
“Yaushe kika zo?”
“Yanzu muka zo, nan ne gidan ku ashe.”
Daga min kai tayi
“Zo muje kiga daki na.”
Da sauri na bita, muka shiga dakin nata, dan karamin gado sai single wardrobe da toilet, kan gadon muka fada muka saki dariya a tare.
“Dakin ki mai kyau.” Nace ina kallon ko ina, a raina ina raya dama nawa ne.
“Thanks.” Ta amsa tana murmushi
“Bari na kawo miki chocolate din da Ya Farouk ya siya min.”
Ta fita da sauri, tashi nayi na bude kofar toilet din, tsayawa nayi ina kallon mamaki, bansan ina ne nan ba, na dai ga alamun akwai ruwa a ciki. Rufewa nayi na koma gadon na hau, na mike kafata ina murmushi. A raina na shiga raya dama daki na ne dana more.
Dakin Farouk ta nufa tana kwala masa kira, yana zaune da waya a hannun sa suna magana da Ja’afar ta shiga, kallon ta yayi ya mata alamar tayi masa shiru, tura bakin ta tayi ta nufi in da ta bar kayan chocolate din nata ta dauka, har zata fita sai kuma ta dawo ta tsaya a gaban sa tana dariya
“Kawata Aminatu ce tazo, tana dakina.”
A dan rikice ya kalle ta
“Ina zuwa zan kira ka.”
“Me kika ce? Su waye suka zo?”
Ya fada yana mik’ewa
“Kawata Aminatu.”
Da sauri ya dafa kansa, da gaske kenan anyi aure, wani irin yar yaji tun daga kansa har tafin kafarsa, tunanin kalmar auren kadai na sa shi a wani yanayi. Ashe da gaske Daddy yak masa, kwata-kwata yarinyar nawa take, da har za’a yi mata aure. Gaban mirror ɗin dakin ya isa yana kallon kansa. He’s to young for that, idan be manta ba next month zai cika 22years chif.
“Ya Salam.” Ya furta yana fadawa gadon
“Me nayi wa rayuwa ta ne? Na daure kaina da kaina, yanzu idan Mummy ta samu labari ya zanyi?”
Da sauri ya tashi, farar singlet ce kawai a jikin sa, sai dogon wando, ciwukan jikin sa na nan musamman na fuskar sa, dakin Amal din ya nufa da dan saurin sa, ya bude kofar da karfi. Suna zaune sun baje a saman gadon suna kwasar chocolate. Tsaye yayi yana kare musu kallo, da sauri yaga ta rufe idon ta ta sauke kafarta kasan gadon, kallon kansa yayi ya sake kallon dakin
“Menene?” Amal ta tambaya tana kallon na.
“Tashi ki rakani wajen su Hanne, kar naje ana jirana zamu tafi.”
“Kai dan Allah, ki kwana mana.”
Make kafada nayi, takowa ya shiga yi har ya ƙaraso gaban gadon, ya sa hannu ya rike ni, zaro ido nayi ina kallon sa, sai kuma nayi saurin rufe ido na
“Tsoro na kike ji?” Ya fada yana kallon saman fuskata
Da sauri na daga kaina, dariya Amal ta kwashe da ita har da tafa hannu
“Tsoron Ya Farouk kike ji, ai baya suka fa.”
Bata fuskar sa naga yayi ya saki hannu na, be ce komai ba ya juya ya bar dakin. Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Amal din
“Ni dai muje ki rakani.”
Tashi taga nayi yasa ta mike itama ba tare da taso ba muka fito wajen Dada. Babu kowa sai ita kadai, kallon ko ina na hau yi da sauri alamun neman abu.
“Kuzo nan yarana, Aminatu me kike nema naga kina ta kalle kalle.?” Ta fada cikin son ta yi min wayo
“Ina su Hanne?”
Nayi narairai da fuska kamar zanyi kuka.
“Kinga ke anan zaki zauna ke da kawarki, kuyi wasa tare, kuyi komai tare har karatu zan sa ana koya muku, idan kika kwana da yawa sai ki koma gida.”
“Har karatu ma zamu dinga yi, kuma ba zanyi girkin shinkafa da wake ba ko??” Na tambaye ta ina kallon ta.
“Girki! A ah banda girki, ai kunyi kankanta sai an kwana biyu, sai share dakin ku kawai da wanke toilet, sai kuma sallah.”
Washe baki na nayi, cike da murna na ce
“Ni ba sai an maida ni gidan mu ba ma, ki barni ana kawai.”
Dariya suka sa gaba dayan su, nima na bisu mukayi ba tare da na gane dalilin dariyar ba. Abincin dazu aka zuba mana, muka hau ci muna kallo, tuni na manta da komai, muna gamawa Dada ta dauko magani ta bani na sha, sannan tace muje muyi sallah, bazan tuna rabon da Inno ta sakamu sallah ba, babu ruwan ta da munyi ko bamuyi ba, muna idar da sallar muka dora kallon mu, ranar gaba daya ji nayi kamar nafi kowa farin ciki a duniya. Sai gaf da magriba sannan muka koma dakin Amal da a yanzu ake masa lakabi da dakin mu.
Gidaje biyu ne manya manyan gaske wanda suka cinye kafatanin layin tun daga gaba har baya, iri daya ne sai dai daya yafi daya girma da komai. Da dukkan alamu mamallaka gidan akwai alaka me karfin gaske a tsakanin su, ko ta yan uwan taka ko ta abota. Gidan farko da yake dauke da tafkeken gate me matukar tsawo da fadi aka yi saurin wangalewa sakamakon karar horn, da sauri mutane biyun dake zaune akan dan bencin zaman maigadin gidan suka tashi suka nufi wajen motar. Babban mutum ne dogon gaske, cikin shigar alfarma ya fito daga ciki, hannun sa dauke da wayar sa yana amsawa, yadda yake magana kadai zaka gane yadda arziki ya samu babban matsuguni a wajen, rike yake da murfin motar har ya gama wayar kafin ya maida duban sa bakin yana murmushi
“Sannun da zuwa Alhaji.” Suka ambata a tare cike da girmamawa. Amsawa yayi yana duban chan hanyar gate din.
“Wai tun da mukayi waya kuke zaune kenan, sannun ku da zuwa, Bismillah.”
Gaba yayi suka bi bayan sa har kofar da zata sadaka da babban falon gidan, daya daga ciki ne yayi saurin bude masa, godiya yayi sannan ya shiga da sallama, babu kowa a falon nasa, sai sautin suratul bagra dake tashi daga cikin jerin speakers din da suka karawa falon kawa.
“Bismillah, Ina zuwa.”
Wuce su yayi ya haura corridor din da zai maidaka part din matar gidan. Yana shiga yaron dake kwance akan sofa yana kallo ya taso da sauri
“Daddy!” Ya rungume shi,
“Kamal, kana nan kana sana’ar taka ta kallo ko, yau babu islamiyya ne.”
“Malam ne yace yau ba zai zo ba zai je garin su.”
“Ah lallai, yau ranar hutawa ce.”
Kallon ko ina yayi kafin ya sake shi yana cewa
“Ina Mamyn taka ne? Naji gidan tsit.”
“Tana daki, wai kanta ne yake ciwo na dame ta da surutu shine ta koroni.”
“Toh zauna na dubo ta, kai ɗin ne watarana akwai zuba kamar…”
Buga kafa ya fara yi irin ta shawagabbun yara, dariya kawai yayi ya nufi dakin gimbiyar tasa. Tana kwance ta juya bayan ta ya shiga, yadda yaga yanayin kwanciyar ta ta yasa ya gane da gaske kan nata ke ciwo, dan dama gwanar ciwon kance, fasa tada ta yayi ya juya ya koma wajen bakin sa. Sun jima suna tattaunawa kafin su tafi, daga nan ya bada umarnin kar a bar kowa kuma ranar yana so ya huta sosai.
Watsa ruwa ya fara yi, yaci abincin da ke jere a saman dining din part din nasa, sannan ya nufi bangaren Hajiyar sa.
Gaba daya ran Inno a jagule yake, ta rasa yadda zata bullo wa al’amarin, gaba daya ji take dama bata amince da bukatar su ba, da tuni zuciyar ta na nutse bata da wani tashin hankali. Babban matsalar ta ma zuwa da tayi wajen Harira da ta tambaye ta labarin yaron ta, yadda ya amsa mata ya nuna cewa bata san komai akan halin da yake ciki ba. Tun bayan abinda ya faru da Aminatu, kullum bata samun isasshen bacci, bare yanzu da ta koma wani gidan sai take ganin kamar babu ita babu cikar burin ta. Duk da sunyi alkawari da Harira akan haka sai dai bata jin zata samu nutsuwa kenan har idan ba dawowa din tayi ba. Ita da zai yiwu ma da sun hakura da komai ta maida ta wajen iyayen ta, hankalin ta ya kara tashi ne saboda samun ainihin labarin waye iyayen ta, kuma dadin dadawa babu hannun mahaifiyarta ko mahaifinta a bin da ya faru, Harira ta rufe ta, ba ta sanar da ita duk wannan ba, yanzu idan suka ki yarda suka hada su dukka suka kulle su fa, bata tunanin duk duniya akwai wanda zai iya fito dasu. Haka zasu kare rayuwar su a ba wan ba kanin. Ita kam abubuwan sun mata yawa.