DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL


Sati Daya

Wasanmu kawai muke nida Amal, bamu da wata damuwa ko kadan, ina matukar jin dadin zaman gidan. Wajen yanayin jikina kuwa sosai magungunan da nake sha suka taimaka min wajen samun lafiya ta. Har na murmure abu na, kaya kuwa na Amal nake sawa kafin nima a karo min nawa kamar yadda Dada tace. Muna zaune a falon Amal na karanta mana wani story book duk da ba gane wa nake ba, idan ta karanta sai ta fassara min da hausa. Sosai hakan ke min dadi. Shigowa yayi fuskar sa babu walwala kamar ko yaushe ya wuce, duk ya rame yayi baki, ina ji dai ranar Dada na masa fadan ya saukaka wa kansa, damuwa babu inda zata kai shi, duk da hakan be chanja ba. Kullum yana aikin waya, a rana sai ya kira Daddy sau nawa ba tare da ya kosa ba duk da hakan baya dagawa, daga karshe ma sai ya sashi a blacklist.

Har ya gifta mu sai kuma ya dawo da baya ya tsaya a gaban mu. Duk muka kalle shi a lokaci guda dan ba kasafai yake shiga harkar mu ba.

“Me kuke yi?”

Ya tambaya yana zaman a hannun kujerar ta gefen da nake. Mika masa littafin Amal tayi tana matsowa

“Story book muke karantawa.”

“Kuna son mu fara lesson?”

Da sauri muka amsa, murmushi yayi ya mika mana littafin

“Shikenan anjima zamu fara idan nayi bacci na tashi.”

Murna muka hau yi ya wuce ya bar mu yana girgiza kai. Bayan wani lokaci sai gashi ya fito cikin shigar kananan kaya, yanzun ma wayar ce a kunnen sa suna magana da wani, zama yayi yana wayar yana kallon in da muke, har ya gama be dauke idon sa daga kanmu ba, tashi yayi ya wuce dakin Dadah, yau duk wunin ranar a daki tayi saboda ciwon kafarta da ya matsa mata,daga mu sai masu aiki sai yanzu da Ya Farouk ya dawo. Jim kadan sai gashi ya fito dauke da mukullin mota yana jujjuya shi.

“Kuzo muje ku rakani.” Yace yana yin hanyar fita, da gudu muka yi daki, muka sako takalmi muka fito, yana tsaye jikin motar suna magana da driver, muna fitowa ya bude mana baya muka shiga shi kuma ya zauna a gefen me zaman banza driver ya data motar muka fita daga gidan. Tunda nazo yau ce rana ta farko dana fita, murna sosai nake ina jin kamar muyi ta dawwama a irin yanayin da muke ciki a yanzu, kadan kadan nake tunawa da yan gidan mu shima ba ko yaushe ba, yawanci nafi tunawa dasu idan Amal tayi bacci ta barni. Bani da sauran matsala komai muke so mukeyi, sai nake jin kamar nafi kowa sa’a a duniya.
  Fita daga kauyen namu mukayi baki daya muka shiga cikin gari, a bakin wani babban shago muka tsaya,ya Farouk ne kaɗai ya fita ya bar mu a motar, chan ya dawo da kaya ya zuba a booth sannan muka nufi wani shagon, haka mukayi ta yawo daga nan zuwa nan wani wajen ya shiga damu wani ya bar mu a mota. Bamu muka dawo ba sai yamma likis cike da gajiya dan Amal tun a hanya tayi bacci ta barni.

****Tun daga ranar muka fara karatu da Ya Farouk, kullum da abinda zamuyi, chan baya muke tafiya mu saka babar darduma mu baje sai mun gaji sosai yake kyale mu musamman ma ni, dan mafi ya yawan lokuta ni yake wa karatun dan ita Amal ta wuce wajen.
  Muna cikin wannan yanayin Daddy ya turo aka tafi da Amal, ranar nayi kuka sosai nace lallai sai an maida ni gidan mu, da kyar shi da Dada suka shawo kaina na hakura na zauna, amma bani da wani kuzari tun bayan tafiyar ta ta wadda Dada tace min sun koma makaranta ne kuma ba nan kusa bane. Haka dai na hakura na cigaba da daukar karatu da yanzu yafi min komai a rayuwata.

Wata na hudu cif a gidan, sau biyu su Karime suka zo ita da yan gidan mu suka wuni, suka tafi, anan ne suke fada min ai aure akayi min shiyasa nake zaune anan, kuma Inno ce take hanasu zuwa shiyasa. Ban dauki zancen nasu da muhimmanci ba, haka na tattara na cigaba da sabgata saboda ba karamin sabo nayi da Ya Farouk ba, gashi kusan kullum sai ya kira min Amal da daddare munyi waya.
   Ranar da bazan taba mantawa da ita ba, nayi bacci na tashi kenan, dakin ya Farouk na nufa da sauri na ina tunanin ko ya zo tashi na ya ga ina bacci ya gudu bayan yayi min alkawarin yau zai kaini gidan mu har na wuni, kwana yace zanyi na fafure nace sai dai yini, yayi ta min dariya yana tsokana ta, ban damu ba,dan zama na anan ɗin yafi min dadi musamman ma saboda karatun da nake yi.
  Tura dakin nayi na shiga bayan na kwakwasa ya bani izini, Yana lullube a bargo ya rufa har kansa, kiran sunan sa na fara yi ina k’arasa ciki. Cikin muryar bacci ya amsa min, dariya nayi na haye kan gadon ina jan bargon dan nasan ba bacci yake ba, mafiya yawan lokuta ya saba yi min hakan. Rike bargon yayi yana ja ina ja har na samu na bude masa fuskar sa.

“Laaa bacci karya fa kake ya Farouk.” Nace ina dariya, bude idon sa yayi cikin yanayin bacci ya zuba su a kaina

“Bacci nake fahhh…” Ya fada cikin wata irin murya kamar ba tasan ba, jan bargon yayi ya sake rufawa nayi saurin janye wa ina sake yin dariya

“Ni dai ka tashi, ba kaine kace zaka kaini gida yau ba.”

“AMINATU pleaseeeeee…, bacci anjima zan kaiki.”

‘Dage kafada nayi na sake janye bargon ina bubbuga masa damtsen hannun sa. Da wani irin karfi nayi ya riko ni, gaba daya na shige cikin jikin sa, ya jawo bargon ya rufa akanmu. A tsorace nake kallon sa, idon sa a kulle ya sake maidashi ya rufe, zura wa fuskar sa ido nayi kamar wadda ta fara ganin sa, na kasa kwakkwaran motsi, balle na yi yunkurin tashi. Takun tafiya naji yana tunkaro dakin, hade da karar abu kamar ana jan wani abu, janye bargon nayi daga saman fuskar mu na zuba wa kofar shigowa dakin ido tun da dama dana shigo ban rufe ta ba ina sauri. Cikin wata irin shiga ta alfarma, me cike da haiba tayi wa kofar dakin tsinke, tsaye take janye da yar karamar jakar matafiya, sai handbag din ta dake sakale a sangalalin hannun ta. Cikin mintuna da basu gaza biyar ba nayi mata kallon tsaf, yadda naga ta buda idon ta sosai akanmu ya ɗan tsorata ni, cikin tsananin mamaki naji ta kira sunan sa da d’an karfi.

“Son!”

A firgice ya dago idon sa ya sauka a kanta, yayi wani irin tashi da dukkan karfin sa har yana ture ni daga jikin sa, cikin sakin bakin ya furta

“Mom!”

DAURIN GORO????????????????????

ZAFAFA BIYAR

KAUNAR MU: MAMUH GEE

ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA

GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL

DAURIN GORO:HAFSAT RANO.

IGIYAR ZATO: MISS XOXO

LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500

ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????

2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK

saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863

GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????

09032345899

Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????
©️®️HafsatRano

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                    (8)


Kallon mu take babu ko dauke ido cikin wani yanayi, ranta a matukar bace, da sauri ya isa gaban ta yana mika hannu zuwa wajen jakar kayan ta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button