DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Welcome Ma. Ashe kina hanya.”
Kallon banza tayi masa, ta wuce shi ta shigo dakin, har in da nake, bina ta cigaba da yi da kallo tana tabe baki kafin tace
“Yanzu akan wannan ka zabi ka katse rayuwar ka, ka hakura da komai ka anan, yaushe ka zama haka Farouk?”
Ta fada tana buɗe idon ta sosai akan sa
“Mummy Please, ki huta sai muyi magana.”
“Naki na huta ɗin, kana son ka kashe rayuwar ka abanza kana cemin ma huta, saboda kai kafi kowa tausayi a duniya ko? Abin da kuma nazo na tarar fa, ko shima tausayin ne? Kuna kwance tare amma a waya kana nuna min kai kawai kana son taimaka mata ne.”
“Ya Salam… Mummy bafa abinda kike tunani bane.”
“Toh mene?” Ya fada a harzuke
Kallo na yayi ganin yadda nake ta binsu da ido kamar na samu tv yace
“Jeki dakin ki Aminatu, anjima sai na kaiki gidan ko?”
Zumburo baki nayi cikin jin haushi na tashi na bar dakin, sakin baki tayi tana dubanshi.
“Farouk!”
“Mummy dan Allah, here me out, idan kika ji komai sai ki yanke min hukuncin da kika ga ya dace dani.”
“Farouk wanne abu kuma zanje bayan wanda ka fada min, Ja’afar ya fada min, akwai wani sauran point ne da ban ji ba?”
“Ja’afar…?” Ya ambata cike da mamaki
“Ban isa ya fada min ba ne ko me? Ina chan ni sam hankali na ya kasa kwanciya kai kana nan kana baccin ka da yar yarinya karama, toh wallahi an gama, munafukar kakar taku sai tazo ta warware wannan kullin da tayi, ko da bana gidan naku amma ido na na kan duk wani motsin ku, kuma wannan karon bazan yarda ba wallahi.”
Dafe kansa yayi ya juya mata baya da sauri, matsalar mahaifiyar su kenan, ya rasa dalilin da yasa a komai take blaming Dadah, bayan babu wani abu da tayi mata, shi yasa yayi ta iya kokarin sa na ganin ya kwantar mata da hankali amma sai da Ja’afar ya kai mata gulmar, yana jin ta tana sababi kafin ta nemi waje daya ta ajiye kayan ta tana zaman gefen gadon.
Dakin ya bari ya nufi wajen Dadah dan sanar mata kar sai ta fito su hadu, tana zaune akan babbar darduma da alama ta gama sallar walaha kenan, tana dan bitar karatun Alkur’ani, gefen ta ya zauna har ta kai aya ta rufe ta juyo tana murmushi
“Babana an tashi kenan.”
“Uhum.” Yace yana tankwashe kafarsa
“Dama Mummy ce tazo.”
Ya fadi maganar kamar wanda baya so, shiru Dadan tayi cikin nazari, tabbas tasan zuwan nata ba zai zame musu Alkhairi su dukka ba, sai dai abu daya ta take tsoro shine yadda zata dauki maganar Aminatu, tasan ta sarai mace ce wadda take da son kanta, ba lallai ta fuskanci maganar ba, shiyasa take ta kokarin ganin Daddy yasauko ya bar su sun tafi baki daya, idan yaso Farouk sai ya koma makarantar sa ita kuma a sata a ko tasu Amal ce, sai dai hujjar daya bata na cewa wa’adin daya deba wa Farouk din be cika ba yasa ta hakura, sai dai zuwan mahaifiyar shi a yanzu yasa ta ɗan ji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk da haka ba zata shiga hurumin da bana ta ba, d’anta ne tafi kowa sanin ciwon sa.
“Ah sannun ta da zuwa, yaushe ta zo?”
“Yanzu.” Ya amsa yana kallon yanayin ta
“Madallah, sannun ta da zuwa.”
“Uhum.” Kawai yace ya tashi
“Dan Allah Dadah… Kinsan halin Mummy, karki bari tayi abinda ba dai-dai ba dan Allah.”
Kallon sa tayi ba tare da tace komai ba har ya juya ya bar dakin, tashi tayi ta koma saman gadon ta tana tunanin yadda abubuwan zasu zama.
Kwanciya na koma nayi ina jin haushin katse min zuwa gida da matar tayi, ido na a lumshe kamar ina bacci aka turo kofar dakin, da sauri na bude ina kallon kofar, yana tsaye ya rike hannun kofar yana kallon ciki, tashi nayi zaune ina saukowa da kafata kasa
“Ya Farouk wacece datazo?”
“Mamana ce.” Ya amsa min yana sakin kofar, ciki ya shigo ya zauna gefen gadon yana matso dani kusa dashi ssosai.
“Kina son ta ko?” Ya tambaye ni yana kallon fuska ta, da sauri na girgiza masa kai alamun a’ah, ware idon sa yayi gaba daya akaina.
“Are you serious! Mamana ce fa.”
“Eh ni bana son ta.” Na faɗa cike da yarinta
Da sauri ya rufe baki yana harara ta
“Kar na sake ji kin fada, kice kina son ta.”
“Ni toh ba masifa take maka ba, ni bana son ta, ni kai kadai nake so sai Amal,sai yan gidan mu.”
Murmushi naga yayi, ya rike hannu na cikin nasa ya murza a hankali
“Ni kina so na ko?” Ya tambaye ni
“Eh mana, kana da kirki ai.”
“Toh idan kina son na, kiso mummy ma kinji.”
A cunkushe na amsa da toh
“That’s my girl.” Yace yana mik’ewa. A nutse ya juya ya bar dakin ina kallon sa har ya gama ficewa.
***Waya ce a rike a hannun ta sanda ya shiga, yanayin da take magana ya gane akan sa take wayar, kai tsaye wajen kayan sa ya nufa ya tattara abubuwan da zai bukata ya kai chan dakin su Ja’afar ya zuba sannan ya shiga Kitchen yasa masu aikin gidan suka bashi breakfast ya kai mata dan yasan bata karya ba. Ko da ya koma ta gama wayar tana dan dube dube a cikin iPad.
“Mummy gashi nasan baki yi breakfast ba, in Kika gama sai kije ku gaisa da Dadah pls tasan kinzo.”
Tabe baki tayi ta ja tray din gaban ta ta bude, juyawa zaiyi ta dakatar dashi
“Ka daina gudu dole muyi magana kaji da abinda nazo, ba zama nazo yi ba ina da abubuwan yi da yawa.”
“Watsa ruwa zanyi sai nazo muyi maganar, kiyi hakuri.”
“Yayi, ina jiran ka.”
“Ok.”
Yace ya nufi dakin Aminatu, budewa yayi ya ganta tana kokarin zuge zib ɗin doguwar rigar dake jikin ta, karasawa yayi ya taymaka mata ta cire sannan yace tayi wanka ya kaita, da gudu tayi toilet shi kuma ya nufi dakin su Ja’afar da ya zama nasa a yanzu.
A gurguje ya shirya ya fito dan baya so taje neman sa dakin sa, baya so sam su hadu ita da Mummy su biyu ba tare da shi din a tsakani ba. Aikuwa a hanya sukayi kicibis ta tafi dakin nasa, riko hannun ta suka juya zuwa hanyar fita murnar ta take tsayawa.
Babu driver da alama Dada ta aike shi, sai driver mummy shi kuma baya so ya nuna masa gidan dan be san abinda mummyn zata iya aikatawa ba. Kawai sai ya yanke shawarar su tafi a kafa tun da babu nisa. Fita sukayi a kafa hannun sa sakale cikin nata, tana tayi masa hira duk yawanci akan wayar su da Amal ne, sama sama yake sauren ta, hankalin sa ya tafi akan yadda zai ɓullo wa Mummy. Sun kusa isa gidan suka yi kicibis da Garbati da Ilu, da mamaki suke duban su, sam Garbati be yi tunanin abin a iya nan zai tsaya ba, wani haushi ne ya taso masa, yayi saurin shan gabansu, da sauri ta koma bayan Farouk din tana buya.
“Me hakan?” Farouk ya fada bayan ya haɗa girar sama data kasa.
“Babu komai, kawai dai ajiya ta ta wajen ka nake dubawa, naga alama kuma dai babu wata matsala.”
Haushi ne ya kama Farouk, sai dai ba zai biye masa ba, dan yaga alama sam Garbatin baya cikin jerin mutane masu ƙwaƙwalwa, hannun ta ya damke sosai suka raba ta gefen su suka wuce kawai ba tare da yace komai ba. Haushi sosai ya kama Garbati, yaji kamar ya jawo shi ya ta bugun sa ko zai huce, haka yayi ta zage zage Ilu na bashi baki suka wuce in da zasu.
A kofar gida ya tsaya ta shiga ciki ya tabbatar ta shiga sannan ya juya ya bar wajen.
A tsaye na tarar da Inno wajen in da take kiwon ta, tana gani na ta saka min ido cike da mamaki, da sauri nayi wajen ta ina murnar ganin ta, murmushi ta k’ak’alo wanda ya zauna iya saman fuskar ta, ta ajiye abinda take
“Ke kuma daga ina?” Ta tambaya tana yin gaba, bin bayan ya nayi lokacin su Karime suka ganni, ihu muka hau yi muka dane juna. Nan da nan aka fara shigowa daga cikin gidan namu zuwa gani na, hakan ya bata ran Inno ta kwala mana kira ni da Karime muka shiga dakin ta, waje ta nuna mana da hannun ta sannan ta fice ta bar mu a dakin bayan ta ja mana kunne akan karmu sake fitowa sai ta kiramu. Hakan da tayi ya rage masu shigowar dan sun sane abinda take nufi, hirar mu muka baje irin ta yarinta nida Karime ina ta bata labarin gidan Bature, murna take tana jin dama ita ce. Chan da azahar Inno ta kira Karime ta kawo mana dambu da wake, rabon dana ci irin abincin gidanmu an jima, ai kowa na saki ciki naci sosai harda k’ari, nasha ruwa nabi lafiyar katifar Inno na baje abina cikin jin dadi.