DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

A fili yayi maganar, sannan ya juya cike da karshashi ya bar dakin, sallah ya fara gabatarwa kafin ya nemi driver su tafi dauko ta.
***Ina zaune Inno na gefe tana ta aikin lissafin Kudi,yadda ta tsare ni a dakin gaba daya ya sa naji duk na gaji, tun Karime na tayani hira har itama ta gudu ta barni, gashi Inno ta kafa ta tsare ko ina, ina jin su suna wasa a tsakar gida kamar inyi ihu. Sai data gama ta tattare kan kudaden ta bude inda take ajiye wa tayi musu kyakkyawan boyo, har ta rufe sai kuma ta sake budewa da jawo wata jaka, bude cikin ta tayi ya dudduba sannan ta mayar ya rufe, ina kallon ta, ganin zata juyo yasa nayi saurin janye ido na, kallo na kuwa tayi tana juyawar.
“Bacci kike?” Ta tambaya tana matsowa
“Wasa nake son zuwa nayi nida su Karime dan Allah.”
“Ba zaki ba.” Kawai tace tasa kai ta bar dakin, kuka na saka cike da jin haushi, duk sai naji dama ban zo ba, kallon tagar dakin nayi naga duhu ya fara zuwa alamun dare kenan, Ya Farouk be zo ya tafi dani ba, duk sai naji ina son tafiya. Addu’a na fara yi Allah yasa yazo. Jin shiru shiru yasa na kwanta lamo ina jin haushin kowa, da haka bacci ya fara fisgata. Sama sama naji Inno na taba ni.
“Keeee…ke.” Ta bubbuga min jiki na
A gigice na tashi
“Ya Farouk!” Na ambata ina mik’ewa, kallo na tayi kawai cike da mamaki.
“Na’am.”
“Tashi maza ku wuce, kin hangame baki kina bacci ko tuwon baki ci ba.”
Da sauri na mike, na yayimi mayafi na na fito, a kan tabarmar gidan daidai kofar Baba na hange shi, kallo na yayi nayi saurin jan kafata zan karasa wajen, ji nayi an riko ni, Inno ce ta banka min harara, da sauri nayi kasa da kaina.
“Ku wuce dare nayi.” Tayi magana tana kallon bangaren su Baban. Tsam ya mike, yayi sallama da Baban sannan y fita, sai a sannan ta sakar min rankwashi a kai sannan tace su Karime su rakani.
“Uwar rawar kai.”
Ta ambata tana jan tsaki. Daki ta fada cike da tunanin abin da zatayi. Ga maganar da yazo da ita wai makaranta zai sata ta kwana, kenan babu ranar da zai sake ta, bayan Harira ta karbi kudin ta tace ko wata biyu auren ba zai ba, sai gashi ana maganar wata biyar, idan tayi sake kuwa sai dai taji ana maganar suna. Dolen ta gobe ta koma taji in da aka kwana, ba zai yiwu ta zuba ido haka nan ba.
***Tun da muka fita bamu wuce gida ba, zakayi kawai muke tayi har bayan sallar isha’i, a mota suka barni suka yi sallah sannan ya je ya siyo mana tsire, sanda suka dawo har na fara bacci, tashi na yayi ya bani naman, ina ci na sake komawa na kwanta. Bansan yaushe muka koma gidan ba, ashe baya so mu hadu da Mummy ne shiyasa yayi ta jan komawar. Ban san me ya faru ba, nidai na farka naganni a dakin Dadah, tashi nayi na koma daki na na sake maida kai na cigaba da bacci na cikin kwanciyar hankali. Wajen bakwai da rabi na sake farkawa, sallah nayi na kwanta akan carpet din na cigaba da bacci. A hankali aka turo kofar, kallon gadon ya fara yi sannan ya hange ni a kasa. Banji takun tafiyar sa ba, kawai sai ji kayi an daga ni sama, dan karamin hijabin danayi sallah ya shiga kokarin cire min, na sake runtse ido na kamar me baccin gaske, ina ji a cire ya ajiye a gefe ya kwantar dani a gadon, ido na ne ya fara rawa alamun baccin karya ne. Murmushi yayi me sauti ya mintsine ni a hannu na
“Wayyo.” Na bude ido na ina kokarin yin kuka
“Baccin karya ko?”
“Na gaske ne fa, kaine ka tashe ni.”
“Umm amma idon ki yake ta rawa.”
Dariya nayi na tura baki gaba, kallo na naga ya tsaya yanayi sosai, babu ko giftawa, hannu nasa naja gashin idon sa cika da tsokana.
“Ouch, kai kika min haka?” Ya tambaya yana taba idon nasa
“Abu zan cire maka fah.”
“Karya ne.”
“Da gaske.” Na saka dariya ina matsawa. Riko ni yayi ya dawo dani kusa dashi.
“Kina son kiyi karatu ko?”
Da sauri na daga masa kai na
“Good… Zan saki a makaranta. Kina so?”
“Ina so wallahi.” Na faɗa cike da murna
“Ok Tam, zan saki amma sai kinyi min alƙawarin zaki yi karatu sosai, sosai.”
“Zanyi Allah.”
“Good.”
“Toh yaushe zaka sani, kuma aina makarantar take.”
Shafa kansa yayi alamar tunani kafin yace
“Yau zan fara zuwa neman makarantar, in Sha Allah zanyi kokarin ganin an samu, duk da ma anci term daya amma hakan zaki shiga ciki, sai kiyi kokari sosai ki kamo su.”
Murna na hau yi sosai kamar zanyi rawa, hannun sa ya rataye a saman kirjin sa yana kallo na, sauka nayi na jawo littafan da muke karatu dasu na fara jera su daya bayan daya. Be yi magana ba, sai murmushi kawai yake. Chan ya mike da sauri yana dafa kai, shaf yaso mantawa da tafiyar Mummy, abinda ma ya tashe shi da wurwuri kenan. Fita yayi yaja min kofar na cigaba da hada littafan cike da farin ciki.
***Har airport ya rakata, ba zatayi tafiyar mota ba wannan karon wai Lagos zata wuce akan wani kasuwancin ta, dole sai dai driver nata yabi bayan ta a mota ya koma gida, sanda suka isa ta kara jaddada masa alkawarin su, amsa mata yayi da toh da haka sukayi sallama. Be koma gidan ba, sai kawai ya bazama neman makarantar da zatayi daidai da Aminatun sa, makaranta yake so me kyau me tsada wadda zata taimaka mata kwarai wajen cikar burin ta, be damu da ko nawa za’a kashe ba, kudin da ya karba wajen Mummy da wanda yake dashi dana Daddy zasu ishe shi komai. Shi dai kawai ya samu ya tabbatar yayi wa dukkan su abinda suke so ba tare da ya fifita daya ba. Sai yamma sannan ya samu ya gama wasu abubuwan, duk da ba dukka ya gama ba amma yaci karfin komai, ya samu makarantar da tayi masa, har ma sun bashi damar ya kawo ta interview. A gajiye ya shiga gida, sallah kawai yayi yaci abinci ya sake shiryawa ya fita, gidan su ya wuce kai tsaye dan yana so su sake magana da mahaifiyar ta, a kafa ya taka a hankali kunnen sa sakale da earpiece suna magana da Ja’afar, har ya kusa karasawa gidan suna magana yana fada mishi yadda komai yake tafiya a gida. Daga nesa kadan yaga ta fito, cikin zulumi, kallo daya zakayi mata kasan ba a nutse take ba, da sauri ya kashe wayar yana kokarin tsaida ta yaga ta kara sauri, har zai juya sai kuma yayi tunanin ko babu lafiya, da sauri yabi bayan ta don tabbatar da babu wata matsala dan yanayin ta kawai ya nuna ba kalou ba. Tafiya take tayi hakan kuma shima be fasa bin nata ba, kamar daga sama ta hango Harira tana nufo ta, ja tayi ta tsaya jikin wata bishiya har ta ƙaraso, ganin haka yasa yayi kokarin juyawa, sai dai kalmar da yaji yasa shi dakatawa yana kokarin ganin yaji komai
“Wai Menene wannan kiran haka, kinga fa shiyasa kawai na yanke shawarar fitowa mu hadu a hanya dan yan gidan ma har sun fara zargin wani abu. ” Hariran ta fada tana karasowa.
“Maganar Aminatu ce kin sani ai, fisabilillah bayan kin min alƙawarin ko wata biyu ba za’a yi ba zai sauta ta dawo gida, shiru kake ji gashi ana maganar watanni biyar, kinsan me hakan zai haifar nan gaba.”
“Toh nidai bansan ina matsalar take ba, a gabanki na dauki kudin na bawa malam Tsalha da zauren gidan mu, ya tabbatar mana da ba za’a dau lokaci ba, toh ni bansan ina matsalar kuma take ba.”
“Ni duk ba wannan ba, yanzu gaba daya bani da kwanciyar hankali wallahi, ni idan zai yiwu kawai ki nemo Hajiyar nan, ayi magana, ta in da ake hawa ta nan ake sauka, na fasa wallahi gwara su karbi yar su.”
“Kamar ya? Abinda aka yi yarjejeniya, da zarar yaron nan ya kai matsayin da ake so ya kai din, sai ayi komai cikin sauki, amma yanzu daga farawa kice kin gaji, me ma akayi?”