DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ba zaki gane ba, dalilin baki san yadda yaya suke a zuciyar iyayensu ba, ni kam gaskiya ba zan iya ba, nayi nadamar abinda kika sani na aikata, yanzu zuwa zakiyi ki bani addireshin su, na je na same su a warware komai, na maida musu da yar su, tun kafin ranar da nadama ta ba zatayi min amfani ba.”
Wani banzan kallo Harira tayi mata
“Amma dai kamar ba a hayyacin ki kike ba ko? Kar ki manta su waye mutanen da kike cewa zaki je, kina tunanin zasu tsaya sauraren ki? Bayan haka ma wacce hujja kike da ita da zaki nuna musu?”
“Jini ba karya bane Harira, wallahi suna ganin Aminatu ko ba’a fada ba zasu gane tasu ce, bayan haka kinsan dai ina da hoton mijin dana matar da muka dauka a saman file din asibitin su.”
Dariya Harira ta saka sosai hadda tafa hannu
“Lallai Innaro, bansan ma kwata kwata tunanin ki baya ja ba sai yau, kinsan kuwa me kike shirin yi? Ina tabbatar miki da kina zuwa zasu kamaki su rufe ki, daga ke har zuri’ar ki kuwa babu wanda zai tsira.”
“Ki fuskance ni, akwai matsala ne idan aka cigaba a haka, wadda zamu shiga sai tafi ya yanzu wallahi, idan muka samu yaron nan ya tsinke igiyar auren, sai mu tattara mu mayar musu da yar su, in yaso ita matar data tsara komai sai su kare chan, nidai Buri na d’ana ya dawo, rashin sa ya fara tabani. Nayi nadamar komai wallahi.”
“Da kika gama kafa kanki da kudin da kika karba ba, ke fa wallahi san kanki yayi yawa, wato kinci moriyar ganga ko, toh bari kiji in fada miki gaskiyar magana, bansan in da suke ba, bansan aina za’a same su ba, rabona da su tun sanda muka rabu a asibiti, na yagi rabona, bayan wannan bansan komai akan su ba, ke wallahi ko sunan su ban sani ba, na sai tuna sanda Hajiyar take fada mana sunan da take so a sawa jaririyar, Aminatu MD. Daga wannan bansan komai akan su ba.”
Wani irin kukan kura Inno tayi ta damki wuyan Harira, tuni kokawa ta rikice tsakanin su. Farouk dake tsaye a gefe yayi mutuwar tsaye tun sanda ya fara jin komai har zuwa sanda abubuwan suka dau zafi. Sosai maganar ta taɓa shi, wani irin mugun tausayin ta ya kara dirar masa fiye da wanda yake ji a baya, an cuci rayuwar ta, an raba ta da gatan ta, sai dai ya kasa gane dalilin daya sa suka aikata hakan, kenan babu sanin mahaifanta, toh wacece wannan data zabi rayuwar yarinyar ta lalace akan wani banzan burin ta mara tushe. Ya kasa gano hakan sai dai ya dau alwashin sai ya tabbatar da duk ya warware wannan daurin, ko da kuwa hakan na nufin….
Jin yadda suke abu kamar yara ne yasa shi magana cikin tsawa dan ba karamin bata masa rai sukayi ba.
“Ku dakata!”
A firgice suka juyo, wani irin bugawa kirjin Inno yayi, ta ɗora hannu a kanta kamar zata fasa ihu
“Yanzu kune kuke kiran kanku matsayin iyaye? Masu tarbiyyar yayan su? Tir daku wallahi.”
“Faruku… Tsaya kaji, duk ba abinda kake tunani bane wallahi, yaudara ta akayi…” Katse ta yayi cikin tsananin bacin rai
“Babu sauran girmamawa ko mutuntawa a tsakanin mu. A dah ina miki kallon uwa ne, wadda tasan ciwon kanta dana ya’yan ta, ina ganin girman ki,a matsayin wadda ta kawo Aminatu duniya. Sai dai a yanzu babu ɗaya daga cikin wannan da zai sa na cigaba da ganin girman naki, ki sani a yau ni Farouk, ni zan zame wa Aminatu uwa, uba da dukkan gatan ta, har zuwa lokacin da zan hada ta da iyayen ta, babu kuma daya daga cikin ku da ya isa ya raba auren mu, ƙaddara ce ta haɗa mu, kuma babu wani mutum da ya isa ya raba.”
Yana kaiwa nan ya juya a zafafe ya bar wajen, kwala masa kira take cike da tashin hankali, amma babu alamun zai tsaya balle ya saurare ta,kallo Harira tayi cike da tsana tace
“Sai kin yi dana sanin abinda kika aikata min.”
Dariya ta saka harda tafa hannu tace
“Ko ke kiyi dana sani ba, uwar yan son zuciya ai nice maganin irin ku.”
Ranoa: Hafsat Rano
(10)
Rai a bace ya shigo gidan, muka bishi da kallo nida Dada, be tanka ba, dan ko sallama a ciki ciki yayi ta yayi saurin wucewa dakin sa, yana zuwa ya maida mukullin kofar ya rufe, shiru mukayi baki daya babu wanda yayi motsi, ni a raina mamakin abinda ya sashi wannan tsananin fushin haka nake, ita kuwa Dadah ina kyautata zaton tasan tabbas koma menene akayi mishi ba karami bane. Har dare be fito ba, naje na buga dakin nasa yafi sau nawa baya budewa, duk na rasa ina zaka saka raina. Komawa nayi na shige cikin kujera nayi lamo na kasa ko cin abinci. Ina kwance na fara kuka kasa kasa, bansan dalilin kukan nawa ba, kila hakan na da na saba da yunwar da ke nukurkusata ne, jin karar bude dakin sa yasa nayi saurin tashi, shi dinne ya fito cikin shigar kananan kaya, fuskar sa tayi fayau kamar wanda yayi ciwo, tashi nayi na zauna sosai ban bar hawayen dake zuba a fuskata ba ya karasa sauka. Da sauri ya ƙaraso gareni ya zauna yana leka fuska ta
“Kuka?” Ya tambaya yana mamaki.
Daga masa kai nayi ina sake matsar kwallar.
“Menene?” Ya furta yana matsar da hannu na daga fuskar tawa, goge min hawayen ya shiga yi yana girgiza min kai.
“Karki kara kuka kinji? Babu abinda zai sake faruwa.”
Daga masa kai nayi ba tare da na gane abinda yake nufi ba, matsawa nayi baya kadan na sake kwanciya ina kokarin kama cikina da naji ya murda.
“Kince abibci?”
“Umm umm.”
“Ok Ina zuwa.”
Ya tashi tsam ya nufi Kitchen din, chan sai gashi da abinci a tray da ruwa, zama yayi a kasa ya tankwashe kafarsa ya nuna min kusa dashi
“Oya…”
Da sauri na sauko dama abinda nake jira kenan, tare muka shiga ci yana bani labarin makarantar da yaje, nan danan na ware na shiga yi masa hira nima, ni na kwashe kayan na mayar na dawo na zauna ina duban wayar sa dake saman kujera..
“Dan kira min Amal dan Allah na bata labari.”
Girgiza min kai yayi yana cewa
“Karki fada mata, ki bari kawai sai dai tazo ta ganki da uniform.”
“Tohm shikenan.” Nace ina murmushi. Mik’ewa yayi ya nufi kofar fita yana cewa
“Kije ki kwanta kinji, gobe da safe zamu fita.”
“Toh.” Nace ina mik’ewa dá sauri nayi daki.
***Da safe shine ya tashe ni, ya taimaka min na shirya muka fito, dakin Dadah muka wuce yana rike da hannu na, tana ganin mu ta riko ni tana sani a jikin ta, kallon shi naga tanayi cike da tsantsar tausayi. Girgiza kai kawai yayi yace “Zamu wuce Dadah, ayi mana addu’a.” Hannu ta ɗora a kaina ta yi min addu’a, sannan ta rike hannun shi shima ta haɗa waje daya da nawa..
“Dan Allah Farouk karka yi wasa da abin da mukayi magana akai jiya, zan iya cewa kwana nayi ban runtsa ba ina tunanin komai.”
“In Sha Allah.” Ya amsa mata
Sakin hannun tayi tace muje Allah yayi mana albarka. Haka muka fito yana rike da hannun nawa har mota, wannan karon bayan shima ya shiga tare dani maimakon gaba, driver yaja muka dau hanya. Har muka isa makarantar be daina amsa waya ba, bansan da wa suke maganar ba amma tabbas maganar me matukar muhimmanci ce, lokaci zuwa lokaci yakan kalle ni ya sakar min murmushi. Sai daya ga mun doshi cikin makarantar sannan ya ajiye wayar, waje muka samu muka zauna har aka fara zuwa, ina ta kallon komai kamar almara, dandazon daliban dake kaiwa da komowa a cikin makarantar su suka fi jan hankali na, uniform dinsu ma kawai abin kallo ne, cikin tsafta da tsantsar nutsuwa. Sai wajajen goma da rabi sannan wani mutum yayi mana umarni da muka shigo, shiga mukayi muka zauna ya ɗan fita ya barmu. Kallo na ya Farouk yayi yace