DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Idan suka tambaye ki sunanki, kice Aminatu Farouk MD kinji?”

Kafin nayi magana mutumin ya sake shigowa, zama yayi ya umarci ya Farouk ya ɗan jira a waje, fita yayi ya rufo mana kofar, kujerar kusa dashi yace na dawo, ya shiga yi min tambayoyi, da yawa ban san amsar ba, musamman bangaren turanci da lissafi, duk da na kan fuskanci wani abun saboda dan zaman da nayi da Ya Farouk da karatun da yake min dukka da turancin yake min su, sai dai ba komai ne nake ganewa ba duba da yanayi da makarantar da nake yi a dah. Tashi yayi ya leka ya sake kirawo shi.

“Mr Farouk, mun mata interview sai dai fa she’s left far behind, ya zata iya catching kuwa? I doubt so.”

Folding hannun sa yayi yana duban ya Farouk, murmushi yayi ya ce

“Sir munyi duk maganar nan da principal, zamu biya kudin extra lesson da za’a dinga mata har Allah yasa tayi picking, and bani da doubt zata kamosu, tana son karatu sosai so ina da hope akan ta.”

“Ok Good, if that’s the case, sai muyi komai yanzu, next week Monday ta zama full student, ina ga hakan zaifi.”

“Hakan ma yayi, thank you very much.”

“It’s our pleasure.”

Tashi yayi yace ya mu biyo bayan sa, muka bishi wasu offices, duk wasu formalities bamu bar school din ba sai da muka gama su, a ranar aka bani komai har da uniform, murna da farin cikin da nakeyi ba’a magana, haka muka dawo gida ina rungume da komai kamar wani ne zai raba ni dasu.


Dukkanin satin a cikin shiri muka karasa shi, sosai akayi min provision na dukkan abinda zan bukata, wannan karon Dada da kanta take tsaye akan komai, da ita aka gama shirya min komai. Sai dai ina lura kamar su ɗin ma hada kayan su suke tayi waje daya,sai dai ban kawo komai ba, na dauka ko wani abun dai zasuyi kawai, ana gobe tafiya makaranta dana matsu ina ji kamar na jawo ranar Dada tasa mai aiki ta rakani gidanmu. Gaba daya Inno tayi laushi kamar ba ita ba, ta rame sosai babu alamun walwala a tattare da ita. Kasa shiru nayi har sai dana tambaye ta ko bata da lafiya ne, ta bini da ido kawai ba tare da tace komai ba. Da muka zo tafiya ta dauko wata leda ta bani wai na makaranta ne, na karba nayi godiya na bawa mai aikin ta rike min, zamu tafi ta sake kirana daki ta hau min nasihar da bazan ce ga musabbinta ba, duk yawanci akan kula da karatu na ne, nidai kawai amsawa nake cike da mamaki, ban taba tunanin Inno zata min kwatankwacin hakan, duk sai naji babu dadi bana so na barta, da muka zo tafiya kuwa har da sharar kwalla ta cike da tausayin Inno da abinda yake damunta da bansan ko menene ba.
Washegari da wurwuri na shirya tsaf cikin uniform d’ina sababbi kal, na zauna zaman jiran Ya Farouk, ina zaune shima ya fito, dan tsayawa yayi da baya yana kunshe dariyar sa, hatta jakar da komai na ajiye a gefe, zaman jiran sa kawai nake, karasawa yayi ya zauna yana dauke kansa. Ban gaishe shi ba, kawai na fara maganar tafiya, kin amsa min yayi ya wuce Kitchen ya hado tea ya fito.

“Jeki nemi abu kici.” Yace yana zama cikin kujerun falon, ganin fuskar sa babu wasa yasa na tashi tsam nayi Kitchen din, tea din nima na hado na dauko bread na fito, kamar magani haka nake ci cike da daukin tafiya, yana ta kallo na ta gefen ido har zuwa sanda ya gama ya maida komai Kitchen yazo ya fice, sauri sauri nayi na karasa na sake gyara komai na zauna ina kallon kofa. Chan sai gashi ya dawo dauke da wasu ledoji, a saman kujerar ya watsa su ya wuce dakin Dadah, jim kadan suka fito a tare itama ta shirya alamar tare zamu tafi. Da fara’a ta na gaishe ta, daga nan muka rankaya waje muka shiga mota ina ta murna kamar bakina zai yage. Uffan be ce min ba, yana dai noticing duk motsina. Haka nan yaji ba dadi, ko ba komai akwai matukar shakuwa tsakanin mu, amma hakan shine mafita ga dukan mu. Sanda muka isa makarantar sai naji duk babu dadi, Ina labe a bayan Dadah har aka gama komai, tuni fuska ta ta chanja dana ji an kirawo wata an ce ta tafi dani, da sauri na kankame Dada ina sakin kuka, dariya suka saka baki dayan su, hakan ya kara tunzura ni, hannu na ta kama cikin harshen turanci tace “muje ko?” Kwace hannu na nayi na sake saka kuka ina kallon Ya Farouk, shi dinma ni yake kallo, hannu yasa ya kirawo ni, da sauri na tafi gareshi, maimakon yayi min magana sai yaja hannu na muka fita daga office din, chan baya wajen wasu shuke-shuke ya kaimu, yana zuwa ya cika hannu na yana ja da baya.

“AMINATU…” Ya kira sunana yana saka idon shi a cikin nawa, raw raw na sake yi da idon zan cigaba da kukan, da sauri ya furta

“Ohh Ya Salam! Baki son makarantar ne?” Girgiza masa kai nayi na cigaba da kuka na.

“Toh menene, kin fasa karatun ne?” Nan ma girgiza kai nayi

“Bude baki ki faɗa min kinji.” Ya fada yana sake matso wa sosai kusa dani, cikin muryar kuka nace

“Ni ba tafiya zakuyi ku barni anan ba.”

Dan murmushi yayi kadan, yasan kwanan zance, lallashi na ya hau yi cikin son gamsar dani muhimmancin hakan, tare da alƙawarin zuwa duba ni kowanne lokaci, da kyar na sa kaina na amince, sai dai ban bar kukan ba, haka ya sani a jikin sa yana shafa bayana a hankali, lamo nayi na kasa kwakkwaran motsi, ina jin shi yana kokarin raba jikina da nashi jin takun tafiya, Dadah ce ta iso wajen tana nazarin mu.

“Babana sallamar ta isa haka nan, karka manta fa muna komawa…” Kallon danayi mata ne yasa ta gimtse maganar tana yin gaba

“Kuyi sauri dai ina mota ni, Aminatu Allah ya bada abinda aka zo nema, banda kawayen banza.”

Daga haka ta bar wajen dukkanninmu muka bi bayan ta da kallo babu ko kiftawa, a hankali ya kamo hannu na, ya ciro dan karamin akwati ja me masifar kyau daga aljihun sa, bude ta yayi dan karamin zoben azurfa ya bayyana, ya kama ring finger na ya zura min, yana kallon fuska ta. Babban harafin D cikin wata irin kwalliya shi ya karawa zoben kyau da kawa, kura ma hannun nawa ido nayi cikin tunani me tsawo da bansan me nake son tunawar ba. A hankali cikin wata iriyar magana ya furta…

“Alk’awari kaya ne Aminatu, ki rike Alk’awari, nima zan rike, kiyi karatu, kiyi karatu har sai kin ji kamar kwakwalwar ki xata fashe, a sannan zan tabbatar da buri na ya cika, ina so ki zama cikakkiyar lawyer saboda wani kudiri nawa.”

Daga kai kawai nayi ina cigaba da kuka ganin da gasken tafiya zasuyi, gaba yayi kawai nabi bayan shi da sauri, haka muka jera har gaban motar, da wani irin sauri ya fada ba tare da ya sake kallon bangaren da nake ba, ina ji ina gani suka fice daga cikin makarantar.

Jan kafafuwa nayi na wuce ina jin kamar wani babban bangare na rayuwa ta ya bar ni.

****Suna isa gida suka sauke Dadah, kai tsaye gidan su Aminatu ya wuce, Inno na zaune tana kulla kayan miya aka sanar mata da isowar sa, sai da gaban ta ya fadi, amma ta dake tace a shigo dashi dakin ta, shiga yayi ya zauna yana karewa ko ina kallo, a matukar sanyaye ta shigo dakin, bayan tasa Karime ta kawo masa ruwa, zama tayi daga chan gefe tana tunanin ta in da abubuwan zasu fara.

***Rayuwa na shiga yi sosai a makarantar, bani da wani lokacin kaina sai ka karatu, kawata daya ce Asma’u, tare muke karatu muyi komai, bani da wata matsala sai ta rashin Ya Farouk da nake matukar jin sa a jinin jikana. Lokacin visiting nayi sai gashi yazo, shi kadai yazo nayi ta murna, dariya kawai yake ina bashi labarin makaranta da wahalar karatun da nake, tun da ni kullum akwai wani extra lesson da ake min bayan normal lesson da muke yi baki dayan mu, hakan yasa nake shan wahala sosai, wani lokaciin ma sai naji kamar na sare, sai na tuna kalaman sa na ƙarshe, su ne suke sake zaburar dani dan ganin na cika masa burin sa kamar yadda yace.
Lokacin da akayi hutun makaranta, sabuwar principal din da aka sake wadda na lura da zuwan Ya Farouk na karshe sun jima suna magana da bansan ta mecece ba tasa aka kirani, ta tabbatar min da ni bazan je gida ba, anan makaranta zan zauna wajen ta na cigaba da extra lesson d’ina, ranar wuni nayi ina kuka, haka ina ji ina gani kowa ya watse ya bar ni. Rayuwa ta haka ta cigaba da tafiya, ina iya kar kokari na wajen ganin nayi karatu, maganar zuwa gida hutu kuwa na rasa dalilin da yasa bana zuwa ɗin, tun ina damuwa har na hakura bayan munyi wata doguwar waya da Ya Farouk da wayar headmistress din, tun daga nan na watsar da komai na cigaba da karatu na ka- in- da-na- in.
Lokacin da mukaje aji uku ne, akayi hutu sai ga mutanen da ban taba tsammanin ganin su ba, Ya Farouk ne tare da Amal, Dadah sai Inno da Karime, karamin hauka ne kawai banyi ba, amma tabbas zan iya cewa na jima banyi farin ciki irin wannan ranar ba, abu daya na kasa gane kansa, shine yadda Inno tayi laushi sosai, ta zama wata shiru shiru, duk in da nayi tana bina da kallo kawai, wani lokacin ma sai na ga kamar tana sharar kwalla, ban kawo komai ba, na cigaba da nan nan dasu, har suka zo tafiya, sosai naji son bin su, amma kuma nasan hakan ba me yiwu wa bane. Haka suka tattara suka tafi suka barni da tarin kewar su. Tun daga nan karatu na ya kara daukar zafi, babu wanda ya kuma leko ni, sai dai lokaci zuwa lokaci ya Farouk kan kira a wayar principal ta bani, kullum maganar sa daya nayi karatu, haka na cigaba da dagewa sosai. Zuwa lokacin zuciya ta ta gama sanin menene so, menene kauna, abinda nake ji game da Ya Farouk wani yanayi ne da zuciya da ruhi ne kadai zasu iya tabbatar dasu, baki na yayi kadan ya fasalta yanayin da nake ji game dashi din. Har muka shiga Ss2 be sake waiwayo ni ba, kiran da yake min sam ya daina, sai na dauki hakan a matsayin yana son yaga na yi karatu ne, aikuwa na sake jajircewa.
Exams muka fara ta karshen Ss2, wadda zamu shiga ajin karshe, hakan ya sa na kara zama serious, bani da lokacin komai sai na karatu, sosai kuwa nake jin dadin exams din, ranar da mukayi final exams ne na fito ina tafiya a hankali, iska ake kadan kadan, yammaci ne me cike da ni’ima akwai alamun za’a iya ruwa kowanne lokaci, tafiya nake ina tunanin shi, iya sanin da nayi masa nasan shi mutum ne me matukar son yanayi irin na damuna, jin kamar ana min magana ne yasa na dan dakata ina juyowa, wata yarinya ce yar junior session, hannun ta rike da tarin littattafai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button