DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kiran ki ake a bayan garden din chan.” Tace tana nuna min da bakin ta

“Ni kuma, wake kira na?” Nayi tambayar cike da mamaki

“Kije zaki gani.” Ta amsa min tana wucewa abin ta, cike da mamaki na zuba wa hanyar garden din ido, mamakin me kira na nake, har zan wuce hostel sai kuma na fasa na juya zuwa hanyar da zata sadaka da dan karamin garden din makarantar, ina isa na shiga wurga ido na ko zan ga wanda yake kirana, ban ga kowa ba, tsaki naja kadan na juya da nufin barin wajen. Kamshin turaren sa ne ya daki kofofin hanci na, da sauri na juyo, ido na suka sauka akan sa, sanye yake cikin shigar Kufta baka, wadda tasha aiki sosai da bakin zare ɗinkin three quarter , kansa babu hula sai dai yana rike da ita a hannun sa. Cikin wani irin yanayi yake takowa gareni, na kasa ko da kwakwaran motsi balle nayi tunanin abin yi. Ya chanja kwarai, ya zama babban mutum, me cike da kwarjini da tsari, tsananin nutsuwa da tsagwaron hutu sun nuna kansu a tattare dashi, bayan wadannan abubuwan babu abu daya daya chanja a tattare dashi d’in, shine dai Farouk d’ina, wanda nake ganin sa a matsayin rayuwa ta, komai na.
Hannun sa yasa ya murda a saman fuska ta ya bada sauti, da sauri na shiga kokarin boye fuska ta, tsananin kunyar sa ce naji ta rufe ni lokaci daya, wadda ban taba jin hakan ba sai yau din, wanda nake kyautata zaton hakan na da nasaba da yadda zuciya ta ke kara jaddada min matsayin da yake dashi a cikin ta.

“My Destiny…” Ya kirani da sunan da dukkannin bangarorin jiki na sai da suka karbe shi, kasa daga kai nayi balle ya sa ran zan kalle shi, ina jin shi yana sakin dariya kasa kasa, kallon tsaf yake mun tun daga sama har kasa, a yau ya sake tabbatar da cewa Aminatun sa ta kai, ta isa dukkanin yadda yake da muradi.

“Yau ni yar Aminene take jin kunya?” Ya furta yana dariya

Da kyar na harhada kalmomin gaisuwa waje daya na furta

“Ina… Wu..ni?”

“Ah laillai, na yarda yau Aminatu na ta girma, kunya Aminatu? Ya farouk dinki ne fa, this is unbelievable!”

“But I like it.” Ya fad’a yana kawo bakin sa daidai kunne na. Da sauri na ja baya, hakan yayi daidai da zamewa ta, cikin zafin nama ya tare ni da dukkan karfin sa, ido na shiga zarewa kamar zan fita da gudu, hannun sa ya saka cikin nawa ya jani zuwa jerin kujerun dake zagaye a harabar wajen, banyi musu ba, na shiga bin sa, ina fatan abinda nake ji a yanzu ya zame min wani tsani da zan sake takawa na rayuwa, sai dai kash!.

Rano: ONAR TASFAH
               11

©️®️HafsatRano

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????


Hannun sa ya sabule daga jikin nawa ya zauna yana nuna min kusa dashi, a kunya ce na zauna, kafe ni yayi da ido na kasa koda kwakkwaran motsi, duk da hakan be dauke kansa daga kaina ba, yana so lallai sai yaga tasirin da idanun sa suke min, hannu nasa na kamo karshen hijabin nawa na shiga wasa dashi, bin hannun yayi da kallo yayi murmushi.

“AMINATU… Wai Menene hakan ne? Kunya ta kike ji? Akan me?” Duk a lokaci daya yayi min wannan tambayar, ni kaina mamakin kaina nake ji yadda tsananin kunyar sa ta mamaye ni, na kasa kwakkwaran motsi, kwarjinin sa ne duk ya cika wajen, duk yadda naso na sake dashi na kasa, ina jin sa yana magana nayi kus kamar bana wajen, tashi naga yayi, ya zura dukkan hannayen sa cikin aljihun rigar sa, cikin jin haushi yace

“Tun da haka ne, bari na tafi kawai tun da ba’a son gani na.”

Da sauri na rike hannun sa,

“Dan Allah karka tafi.” Hannun nasa ya kalla sannan ya kalle ni, ya kwashe da dariya, da sauri nayi kokarin zare hannu na amma sai ya rike

“Baki isa ba ai, ana so ana kaiwa kasuwa.” Dariya muka sa a tare baki daya, duk kunya ta sake kamani. Komawa mukayi muka zauna muka hau hira, mafi akasarin hirar shine yake min, duk da na dan sake kadan kar yace zai tafi. Acikin hirar ne na daure na tambaye shi karatun sa, wayar sa ya bude ya shiga gallery ya mika min, baki bude nake bin jerin hotunan nasa da suka gama bayyana irin karatun da yayi, no wonder na ganshi ya sake zama babba, ko ina na jikin sa ya murje, irin na ingarman namiji.

“Soja Ya Farouk!”  Na faɗa ina kallon sa.

Daga min kai yayi yana dariya

“Burin both Daddy da Mom ne, sannan kuma burin Farouk dinki ne, saboda wani babban dalilin sa.”

Jinjina kai nayi ina sake kallon sa.

“Ni da nake tsoron soja kuma…”

“Sai ka mijin ki soja ba, sai ayi yaya? Karki manta fa ance… A wife of a soldier…”

“Can never be a soldier.” Nayi sauri amsa masa ina dariya. Dariyar shima ya saka ya kai hannu ya dungure min kai

“Sarkin wayo, toh ba haka karshen yake ba.”

Muka kara saka dariya a tare. Hira muka cigaba ba dayi har zuwa sanda aka kira magriba, tashi yayi yana nannade hannun rigar sa.

“Ya za’ayi?” Ya daga min kira sama,

“Uhum.” Nace ina tashi nima.

“Kinga ba’a rufe makaranta ba sai gobe, wannan ma dan dai principal din ta hannun damar Mummy ce, kar mu shiga dokar makaranta, zan wuce, amma zan dawo gobe, kinsan da maganar zana waec dinki a Ss2 ko?”

Daga masa kai nayi

“Ok zamu je gida sai kiyi sati daya…

Dagowa nayi da sauri, murmushi yayi min yace

“Daga nan sai a dawo makaranta, kinga ba za’a dade ba zakiyi exams, kina gama wa…”

Be karasa ba, yayi shiru yana sake fad’ad’a fara’ar fuskar sa

“I can’t wait ranar nan tazo, duk plans d’ina na ranar ne, Allah dai ya kaimu, zaki yi mamaki sosai.”

Bude baki nayi zanyi magana yayi saurin katse ni

“Karma ki tambayi me zai faru ranar, kedai kawai ki shirya mata, it’s going to be the biggest day of our lives.”

“Shikenan.” Nace ina matsawa gaba.

“Ba sallama?” Ya marairaice murya yana bude min hannayenku sa, sarai na gane me yake nufi, dariya nayi, na kara yin gaba, sosa kansa ya shiga yi yana kallo na, sai dana tabbatar nayi nisa daga in da yake sannan na daga mishi hannu ina masa gwalo, da hannu yayi min alamar zai kamani ne.


Washegari tun da wuri na tashi, ina nan da d’abi’ata ta dauki idan zanyi abu na tashi da duku-duku na hau shiri, ina ji aka kad’a kararrawar assembly da ake yi a duk ranar da za’a rufe makaranta, a gurguje aka gabatar da komai da ranar da za’a dawo makaranta, kasancewar akwai sauran wajen sati uku kafin a fara Waec yasa aka bawa yan Ss3 hutun sati daya, sai kuma a dawo a fara karatun jarabawar kafin lokacin ta ya zo. Da haka kowa ya hau watse wa cike da farin ciki zuwa gida. Ina tsaye a saman barander classes dinmu na kafa wa gate ido naga shigowar shi, ji nayi kamar zan zame, haka dai na daure na nufi wajen motar, ina zuwa yana fitowa, idanun mu suka sarke waje daya, da sauri na janye nawa na hau gaishe shi, murmushi kawai yayi ya wuce wajen da aka signing, a gaggauce yayi signing din ya taimaka min na dau yan kaya na muka dau hanyar kauyen mu. Sanyin Ac da kamshin turaren da ya bulbula ne suka cika motar, lamo nayi jikin kujera ina jin wani yanayi ne wuyar fassara, magana yake min kasa kasa wanda zaka rantse ba dani ɗin yake ba, idon sa na kan titi sai dai hannun sa daya na rike da nawa yana murzawa a hankali. Har muka isa gida na kasa sakat, shi kuwa babu abinda ya dame shi, sha’anin gaban sa kawai yake cike da tsantsar farin ciki da ya kasa boyuwa a saman fuskar sa.
  A kasalance na fito daga motar bayan ya tsaya, gaba nayi kawai dan Allah Allah nake na isa ciki na samu sauƙin abinda nake ji, ina shiga daki yana turo kofar, tsaye yayi kamar yadda ya saba a wanchan lokacin, hannayen sa jingina da makarin kofar, idanun sa na zagaya wa lungu da sak’o na dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button