DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Uban waye kai da zaka ture ni, kuma…” Maganar sa ta makale sakamakon wandon daya fara cin karo dashi bayan ya dago. Cikin in da in dah yace

“Me nayi maka?”

Farouk be tanka ba, sai kafa daya sa ya tardes shi, tuni ya baje a wajen bakin sa ya fashe, hannu yasa ya hau zare belt din jikin sa, da sauri na balle murfin motar na fito, na isa wajen, rike shi nake kokarin yi, ya juyo a fusace ya nuna min mota

“Wuce ki koma ciki.” Yadda yayi maganar da yanayin fuskar sa, yasa naji yan hanjin cikana sun juya, da gudu na koma na zauna ina rawar jiki. Be wani tsaya bata lokaci ba ya shiga laftawa Garbati belt din nan, ihu yake yana magiya amma sam yaki sauraran sa, Dukan sa yake da dukkan karfin sa, tuni abin ya fara bani tsoro, ganin yadda ya koma kamar ba Ya Farouk ba, ya juye gaba daya ya zama kamar wani horror, kuka na soma a hankali ina daga zaune a motar, sai daya tabbatar yayi masa laga-laga sannan ya ture shi ya nufo motar, da bayan hannu na, na shiga share hawayen fuskar ta. Be ko kalle ni ba, ya tada motar muka dau hanya, ta gefen ido nake satar kallon sa, yadda kirjinshi ke kaiwa da komowa. Sosai nayi mamakin tsananin zuciyar shi. Muna zuwa kofar gida nayi saurin kama kofar motar zan fita, naji ya riko hannu na.

“I’m sorry.” Ya furta yana kallon ido na, daga mishi kai nayi ina sake kokarin bude kofar dan har ga Allah na tsorata da yanayin sa.  Lock din kofar ya danna, ya matso daf dani, da sauri na kulle ido na zuciya ta na harbawa, tsoro na daya kar nima ya jibgen,  a hankali naji saukar light kiss a saman goshi na, sake runtse ido nayi na kankame jikina.

“Ohh shit.” Ya daki steering motar,

“Kinga, pls karki ji tsorana, i can never harm you, shi wanchan kuwa zan masa fiye da wannan, wannan somin tabi ne, saboda haka kar na sake jin kinyi kuka idan ina abu makamancin wannan.”

“Toh.” Nayi saurin cewa.

“Zan tafi.” Na nuna masa kofar motar. Dan karamin tsaki yaaja ya bude min da sauri na fita ina yin hanyar zauren gidan. Sai dana shiga sannan yaja motar ya tafi.
  Sallama nake tayi a tsakar gidan namu, baki daya komai ya sauya, sosai gidan ya sake tsufa, duk kofofin sun lalace, dakin Inno na kalla naga an dan turo kyauren alamun bata nan, Yalwati ce ta fito daga dakin Baba, da mamaki take kallo na, sai kuma ta fadada fara’ar fuskar ta.

“Wa nake gani kamar Aminene?”

Dariya na saka na karasa ciki.

“Ah laillai, maraba da yan makaranta.”

Kasa na tsuguna na gaishe ta, ta amsa sosai, kafin tace

“Shiga wajen Baban naku, Inno dai ta je hayi karbo magani, kinsan duk ba dadi suke ji ba ita da shi.”

“Allah ya sauwake.” Nace ina tura kofar dakin, yana kwance daga gani yana jin jiki, kallo na yake har na isa gaban sa na zauna.

“Sannu Babah.” Na gaishe shi cike da tausaya wa, hannun sa daya naga ya daga min, alamun na matso, matsawa nayi sosai na rike hannun sa ina jera masa sannu. Yalwati ce ta shigo rike da kofin silba cike da ruwan randa.

“Tsautsayi ya gamu dashi ai, faduwa yayi a banɗaki shikenan barin jikin sa daya ya shanye, kin gashi nan baya ko magana.”

Kwalla ce ta zubo min cike da tausayin baba, mutum me sauƙin kai da hakuri, bashi da ta cewa kowanne lokaci sai abinda Inno ta gindaya masa, yau shine rayuwa ta juya wa baya haka, da ido yake min alamar nayi shiru, kasa kasa na cigaba da kukan nawa ina masa addu’ar samun sauki. Ban fito daga dakin ba, sai da Inno ta dawo. Tana gaban dakin ta ta baza ledar magungunan gargajiyar data karbo na fito, da ido ta kafe ni cike da mamakin gani na.

“Yaushe kika zo.?” Tun kafin na gaishe ta ta watso min tambayar, murmushi nayi kawai dan hausawa sunce me hali baya fasa halin sa.

“Sannu da zuwa, ina wuni?” Na bagarar da tambayar da tayi min na maye gurbin ta da gaisuwa, amsawa tayi tana cigaba da duba kayan data zo dasu kamar bata damu da zuwan nawa ba. Dakin nata na shiga, duk yayi kacha-kacha, ajiye hijabi na nayi na shiga kokarin ganin na gyara. Ina cikin gyaran ne nazo kan jakar da nake yawan ganin tana ciro ta, ta duba. Hannu nasa da nufin bude jakar ta shigo.

“Kee!” Ta daka min tsawa, da sauri na saki jakar ta sabule daga hannu na

“Me kike yi haka?”

“Um.. um.. dama gani nayi dakin..um yayi datti shine nake sharewa.”

Zuwa tayi gabana ta dauke jakar ta bude sip dinta ta saka.

“Yi sauri ki karasa sharar ki fito zaku gaisa da mutane.” Daga haka ta fice ta barni, sauri sauri na karasa na fito, na shiga sauran gidajen dake cikin gidan namu. Bayan na dawo ina ta tunanin ina yan matan gidan suke, chan dai na tambayi Inna, sai a sannan nake sanin ashe duk an musu aure. Hanne ta haihu ma Karime kuma ta kusa. Sosai nayi mamaki, naso a ranar na samu me rakani, ana la’asar sai ga kiran Ya Farouk a waje, ban so ba, haka na shiga dakin Baba nayi masa sallama sannan na fadawa Inno yazo zan tafi. Shiru tayi kamar me nazari, sai kuma tace

“Kice masa dan Allah yazo ina son magana dashi.”

Da toh na amsa mata na fito nayi wa sauran sallama. Waya yake yanzun ma, ina bude kofar yayi sallama yana dage min kira sama.

“Ina wuni?”

“Lafiya lou, kin gama ai ko?”

“Eh na gama.”

“Ok.”

Ya hau kokarin data motar,

“Dama inna tace na fada maka tana son magana da kai wai.”

Da sauri ya kalle ni

“Kunyi wata magana ne?” Ya tambaye ni

“A ah bamuyi ba.” Na amsa. Ajiyar zuciya naji ya sauke kafin yace

“Shikenan zan zo gidan gobe, yanzu ana jirana ne.”

Bance komai ba yaja motar muka bar kofar gidan.


Tsawon satin haka mukayi shi, babu abu d’aya, daya chanja, kullum zamu kwanta kamar yadda muka fara a ranar farko, tun ina nokewa har na saki jikina ganin babu abinda ya faru, sai dan abinda ba za’a rasa ba.???? Naje gidan Karime da Hanne, sannan na koma gidan mu sau biyu na sake duba Baba, bansan ko yaje sunyi maganar da Inno ba, ba ta kara dai yimin maganar yazo ɗin ba, sai kawai na share ban tambaya ba.
Daren ranar da zan koma makaranta dukkan mu bamu da walwala sam,sai nace har gwara ma ni ina dan daurewa, amma shi ƙarara ya nuna damuwar sa, hira nake masa da son ganin ya ɗan saki ransa, amma fafur yagi, shinkafa da miya nayi mana a daren ranar, na samu yaci ba laifi dan tun rana be sa komai cikin sa ba. Da wuri yace muje mu kwanta, ranar babu petir a inji be fita ko nan da chan ba. Haka muka yi shirin kwanciya bayan na tabbatar da na gama hada komai nawa a waje daya. Wanka na fara yi saboda yadda garin ya hade rai alamun za’a yi ruwan sama, babu iska ko kadan sai kugin hadarin kawai kake ji. Ina fitowa daga wankan naji garin ya ɗan fara saki, doguwar rigar bacci kawai na zura na haye gado na kwanta, ina kwanciya ya shigo yana haska wa da torchlight ɗin wayar sa, rufe ido na nayi da sauri alamun bacci, wucewa yayi gaban mirror ya shafa roll on dina ya hawo gadon ya jawo ni jikin sa. Muna nan kwance babu wanda yayi wa wani magana, aka soma yayyafi, saki na yayi ya tashi ya bude windows din sosai iska ta shiga zagaye lungu da sako na dakin, yana tsaye ya zura hannayen sa yana kama yayyafin dake sauka kadan kadan. Cikin dan kankanin lokaci dakin yayi sanyi, ruwan da aka farayi da karfi yasa ya sake rurrufe glasses din windon ya saki curtains din. Da sassarfa ya hawo gadon ya kwanta yana ware hannuwansa.

“Alhamdulillah, ni’imar Allah ta sauka.” Ya furta yana mirginowa waje na.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button