DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru mukayi dukkannin muna sauraron saukar ruwan da karfi a nutse babu hayaniya, irin ruwan da za’a iya kiran shi da peaceful rainfall, babu tsawa babu tsananin iskar nan, hakan ya haifar da wani yanayi a tsakanin mu. Shirun da mukayi kowa da abinda yake ayyanawa, a daidai lokacin Ya Farouk na fama da zuciyar shi akan abinda take kokarin bijiro mishi dashi, duk kuwa da alkawari ne ya dauka wa kansa, amma a yadda yake ji yanzu, tabbas baya jin zai iya cika shi, yadda zuciya da ruhin sa ke azalzalar sa, da ingiza shi zuwa abinda ba haramun bane, sai dai shi din daya haramtawa kansa, bisa wani dalili nasa da yake ganin hakan shine daidai. Sake mirginawa yayi yana kokawa da zuciyar tashi, kaso saba’in cikin dari na tsarin zuciya da ruhin shi sun aminta da abinda yake ji ɗin, yana ganin ba zai iya kuma bata wasu dakiku ba tare da aiwatar da abinda suka riga suka yanke masa ɗin ba.
“Princesssssss?” Ya kira ni yana sake matsowa.
“Kina jina?” Ya sake maimaitawa yana lalubar hannu na. Runtse ido na nayi ina jin yadda numfashin sa ke sauka bisa saman fuskata.
“Uhum.” Nace ina kauda fuskata gefe yadda yage faman zagaye hannun sa a saman fuskar tawa.
“Alhamdulillah.”
Ya ambata a chan kasan makoshinsa wanda ba karamin me kunne ne zai jiyo shi din ba.
“I can’t hold it anymore.” Yace yana kokarin chanja karatun dana sani wanda na riga na gama dauka a wajen sa zuwa wani sabon shafi na daban.
Tuni kwakwalwata ta tsaya tsak, ta daina aiki, komai ya shiga chanjawa, a hankali komai yake tafiya har zuwa sanda abubuwan suka sauyawa baki daya. Shafin rayuwa ta na baya ya sake maimaitawa kansa a karo na biyu a siga ta daban.
****Yar karamar ƙwaƙwalwa ta ta gaza aike min da komai zuwa ilahirin sassan jiki na, baki daya bani da kuzarin aiwatar da komai, na gaza tantance abinda nake ji a halin yanzu, karar kafuwar hakora na kawai ke tashi waje daya, tuni zazzafan zazzaɓi me cike da ma’anoni da yawa yayi min rufdugu, ina jin shi yana magana, da dukkan kalmar da zata zo bakin sa, kokari yake yaga ya fahimtar dani komai, bana fahimta, ba kuma zan fahimta ɗin ba. Kalma daya kawai nake iya tantancewa “hakuri” kalmar da yake ta nanatawa kamar a bakin sa aka halicce ta. Da kyar na bude baki nace
“Zan sha ruwa.” Da sauri ya tashi ya kawo min, ya taimaka min nasha, sannan ya gyara min kwanciya ta yana kara nanata kalmar hakuri. Bansan sanda bacci ya dauke ni ba, bacci me dauke da ma’anoni da yawa. A yau na sake taka wani mataki na rayuwa, matakin da ba zan iya sanar daku da yanayin da yazo min ba, abu daya na sani, yana cikin manyan matakan rayuwata dana gaza mantawa.
***Komawa ta makaranta ta ruguje, babu wanda ya tuna da hakan tsakaninmu, zuwa da safe naji dama dama, da taimakon sa na samu na sake komawa bacci a karo na biyu, wanda ban samu farkawa ba sai da rana ta daga sosai. Da fuskar sa na fara tozali, yana zaune a gefe na cikin shigar sabuwar shadda fara kal tana sheki , kansa babu hula kamar ko yaushe, yayi kyau ainun, da sauri na maida ido na na kulle.
“Good morning My Dee.” Ya ambata yana min peck a saman kuncina, dariya na saka ina rufe fuska ta da tafin hannu na. Tashi yayi ya fita, hakan ya bani damar saurin fadawa toilet, na sake gyara jikina da ruwa me dumi, kayan jikina na mayar na dora hijabi akai na fito, yana zaune gaban sa da babban tray, wuce wa nayi na dau doguwar rigar atamfa me karamin hannu na sake komawa toilet din na saka na dauro dan karamin mayafi a saman kaina na fito. Breakfast din ya tura min gabana yana ciro wasu jerin magunguna daga cikin leda. Sosai naci abincin ya bani maganin nasha na koma saman gado na kwanta. Shi ya tattare kayan ya fita dasu sannan ya sake dawowa dakin.
Kwana biyu muka yi a haka, komai shi yake mana, sosai nake jin kunyar sa, shi kuwa babu ruwan sa, budirin gaban sa kawai yake, a kwana na ukun ne aka matsa masa da kira, dole ya fara shirin tafiya nima na hau nawa shirin dan ma tuni yayi waya da principal dinmu.
A tare muka fito gaba daya, muka dau hanyar makarantar mu, har muka isa hannun sa na cikin nawa, da kyar ya kyale ni na tafi bayan doguwar sallamar da muka tsaya yi.
Sanda na dawo har sun fara wasu subjects din, haka na yi joining aka cigaba dani, kullum dare da tunanin sa nake kwana, dashi nake tashi, duk da hakan ban bari ya shafi karatu na ba, dan ina so yayi alfahari dani. Munyi waya sau biyu a wayar principal, daga ranar ban sake magana dashi ba. Bayan sati biyu muka fara Waec, tuni kaina ya dau zafi na ajiye komai, sai dai kullum da matsanancin ciwon kai nake kwana, nake tashi, a haka nake daurewa nake karatun. Wata guda muka dauka da yan kwanaki muna jarrabawar, a ranar da mukayi ta karshe ne jikina ya kara rikicewa, ban iya fitowa daga examz hall ba, sai da wasu seniors suka taimaka min zuwa clinic din makaranta. Tashin farko ta sani zuwa nayi fitsari na kawo a yar wata container, haka nayi fitsarin na kawo, ta rubuta min wasu magunguna tace su rakani hostel, gobe kafin mu tafi gida sai nazo na karbi result. Haka na koma hostel na kwanta, ban iya aiwatar da komai ba, sosai nake jin jiki, a daddafe nayi bacci har gari ya waye, wata roommate dina ce ta taimaka wajen karasa hade min kayana waje daya.
A nutse nake tafiya har na isa clinic din, Ina zuwa na samu waje na zauna dan bata ƙaraso ba. Can ina zaune tazo, tana gani na ta sakar min fuska
“Shigo ciki ko.”
Ciki na shiga ta ban kujera na zauna, envelope ta ciro ta mika min
“Test ɗin da akayi miki baya wani daukar lokaci, ina so dama nayi magana da principal ne shiyasa nace ki dawo yau, toh munyi magana ma kuma dai babu wata matsala tunda dama ashe kina da aure ko?”
Daga mata kai nayi ina juya takardar hannu na.
“Ok Masha Allah, Kinga sai kiyi rainon cikin ki a gida cikin kwanciyar hankali.’
Kaina ne naji yayi wani gingirin, na bita da kallo kamar wadda bata jin Yaren da take min.
“Yes! You are pregnant.” Ta fada tana murmushi, wani yar naji tun daga kaina har tsakiyar kafata. Ni kuma? Ciki? Ikon Allah. Tashi nayi na mata godiya na dau magungunan data bani na fito. Sai na rasa ina zanyi, nayi ta zagaye saman barander daga farko zuwa karshen ta, ina kallo ana yayewa daya bayan daya, har ya zama na kowannne dalibi ya tafi, saura ni kadai. Tun ban fara damuwa ba, har abin ya fara damuna, ina tunanin abinda ya tsaida Ya Farouk, bayan yasan yau ne ranar, ranar dani dashi muke jira, ranar da yayi min alkawari da dama akan ta. Waje na samu daf da kayana na zauna ina kallon kofar. A hankali aka zuge gate din, wata bakar mota ta shigo, baka ganin komai na cikin ta saboda glass din ta me duhu ne. Tsayawa naga anyi daf da security man din dake tsaye daura da gate din. A hankali glass din motar ya shiga sauka, hannu ne ya fito, rike da wata farar takarda, hannun na mace ne, dauke da jerin awarwaraye masu matukar kyau da sheki. Takardar da mika wa security man din tare da sanar dashi wani abu. Ina kallo ta maida glass din motar ta rufe, ta juya ta fita daga cikin makarantar da mugun gudu. Ganin security man din ya nufo ni yasa na tashi ina sake riƙe takardar result d’ina, yana zuwa ya mika min takardar cikin harshen turanci yace