DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sakon ki ne inji Farouk.”
Karba nayi hannu na na rawa, na bude ido na ya sauka akan abinda ke rubuce baro baro cikin manyan harafi. A take naji kaina na juya min, na fara ganin komai biyu- biyu, dafe kaina nayi da dukkan hannu na na kwalla kara da ta cika makarantar baki daya. Daga nan bansan me kuma ya sake faruwa dani ba.
Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
***Daurin Goro
13
©️ Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
Da kyar na bude idanuna da sukayi min matukar nauyi,na fara bin ko ina da kallo, kwance nake a dakin asibiti, hannu na daure da ruwan drip dake sauka a hankali. Fankar saman dake juyawa kadan kadan na kurawa ido ina son tuno me ya faru dani. Cikin yan dakiku ƙwaƙwalwa ta shiga dawo min da komai, kuka nasa da karfi zuciya ta na matukar suya. Me yasa zai min haka? Me nayi masa? Abinda na shiga tambayar kaina kenan ina kuka sosai. Shigowar principal ne da wata mata yasa na rage kukan da nake, har gaban gadon ta ƙaraso tana min kallo me cike da tausaya wa
“Sannu Amina, kiyi hakuri kinji? Duk tsanani yana tare da sauki.”
Ban iya motsawa ba, sai hawayen da suka cigaba da sauka a saman fuskata kamar masu gasar tsere, a yau na sake tabbatarwa da sabon shafin rayuwa ta ne ya sake budewa, shafin da ban shirya masa ba, ban taba tunanin zan riskeni a irin wannan lokacin ba. Juyawa nayi ina runtse ido na ganin duk yadda na juya abinda ke rubuce a takardar nan nake gani,
“Ni Farouk Kabir Shagari, na saki matata Aminatu, babu sauran wata alaƙa a tsakanin mu, sannana babu wani abu daya shiga tsakani na da ita. Idan ta samu wani mijin, tayi aure.”
Tabbas rubutun sa ne, tun yana koya mana karatu na haddace zubin rubutunsa, kawo yanzu da ya zama duk wasu muhimman takardu na rubutun nasa ne akai. Hannu biyu nasa na rike kaina gam dake barazanar rabewa biyu saboda tsananin ciwo, tun ina yin kuka da hawaye har ya koma sai na zuciya kawai nakeyi. Duk maganganun da principal suke na gaza daukar daya a ciki, ina ji suka juya suka fita. Jim kadan wata nurse ta shigo dauke da ruwan allura, da kallo na bita kawai dan bani da wani karfin hana ta, duk kuwa da tsananin tsoron da nake wa allura yau sai ya zama na nafi tsoron kaina da rayuwar da zanyi akan komai. Ina jin ta tayi min, ban ko motsa ba, cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ne da karfin gaske. Wanda nake da tabbacin yana da alaka da allurar da tayi min, dan bana jin akwai wani abu da zai iya sani runtsawa a halin da nake ciki.
Ban farka ba sai da safe, na tashi da tunanin abinda ya faru, kukan na cigaba kamar jiya, dan ina ganin shine kawai zai rage min radadin abinda nake ji. Da taimakon matar jiya na samu nayi sallah, ina sallah ina kuka wiwi, zama tayi a gefe tana jiran na idar, da kyar na samu na kawo sallolin da ake bina,dan tuni jikina ya fara rawa, zuciya ta ta riga tashi, da gudu na fada dan karamin toilet din dake manne a dakin na shiga kwarara amai, babu komai a ciki sai ruwa, a galabaice na gama na fito bayan ta taimakin da ruwa. Kwanciya nayi jikina ya dau rawar sanyi, wani mugun zazzaɓi da ban taba jin irin sa ba ya dirar min a lokaci daya.
Tsaye take a gaban desk din ta, wayar tace a hannun ta tana faman juyata,
“Ya zamuyi da yarinyar nan ne? Sam wayar mijin nata bata shiga wallahi, tun jiya nake gwadawa, gashi babu wata hanya da zamu nemi iyayenta.”
Tayi maganar tana sake dialing number tasa a karo na ba adadi.
“Akwai tashin hankali, ga saki gata dauke da juna biyu, maza basa kyautawa sam wallahi, wannan wane irin rashin adalci ne.”
“Hmm abun dai kam sai dai Allah ya kyauta, ina ganin jira zamuyi kawai ta ɗan ji karfin jikin ta, idan yaso sai a sata a motar makaranta a kaita gida, nasan tabbas zata san gidan iyayenta ai, in ba hakan ba bansan yadda zamuyi ba, kuma kinga ai ba zamu cigaba da rike yarinya a wajen mu ba.”
“Gaskiya dai, hakan kawai shine mafita.”
Shiru sukayi kowa da tunanin abinda ya ke, takardun biyu principal ta nannade ta hadusu waje daya, ta kwashi abubuwan da zata bukata suka fito.
Ƙarar motar data tsaya a kofar gidan yasa yaran lekowa, ganin motar yasa suka hau tsallen murnar ga Aminatu, ga Aminatu, sanin su cewa ita kadai ɗin ake kawowa a mota, dan karamin yaron Yalwati ne yayi jikin motar da sauri, bude motar akayi, duk suka zuba ido suna kallo, a gadarance ta fito, ta tsaya tana karewa gidan kallo, yatsine fuska tayi ta shiga takawa a hankali har cikin gidan. Yalwati na gaban murhu tana gyara wuta, ruwan wankan jego ne akai da za’a yi wa Karime, ta dago da sauri jin takun tafiya haɗe da wani irin kamshin turare daya riga ya game dukkan lungu da sako na gida.
“Maraba.” Tace tana goge hancin ta da yayi shabe shabe da majina, kallon tsaf matar tayi mata batare data amsa ba.
“Kece mahaifiyar Aminatu?” Tayi tambayar tana matsowa ciki. Sai a lokacin Inno ta fito, rik’e da kofin kunun kanwar da ta gama matsawa Karimen tasha.
“Lafiya?” Inno tace tana kallon Yalwati da matar.
“Wajen ki tazo wai.” Ta amsa tana nufar dakin ta, tabarma ta dauko da sauri ta shimfida a yar inuwar wajen tana nuna mata
“Bismillah ga waje.” Kallon banza matar tayi mata sannan ta kalli Inno ta nuna ta da hannu
“Kece mahaifiyar Aminatu kenan?”
“Nice, me ya faru?”
“Dama zuwa nayi na sanar muku, kuje ku dau yarku a makaranta dan yanzu babu wata alaƙa tsakaninta da d’anmu, asirin da akayi masa ya warware sai abi wani sarkin, saki ne ya riga ya sake ta, dawainiyar da yayi da itaa ya isa haka.”
Da sauri Inno ta matsa jikin bangon dakin ta, ta kasa cewa komai, kallo kawai ta shiga bin matar dashi har ta zaro takardar dake ninke a yar karamar jakar hannun ta ta yar a tsakar gidan, ta juya cikin takun ta na kasaita bayan ta tofar da yawu ta fice daga gidan.
Da sauri Yalwati ta dauke takardar tayi wajen Inno tana mata magana ganin kamar bata hayyacin ta.
“Lafiya Yaya? Ko jikin ne?” Ta fada cikin kulawa.
Da kyar ta bude baki tace
“Innalillah wa inna ilaihi raji’un.. Na shiga uku na lalace.”
Da sauri ta sa hannu ta karbi takardar, sannan ta juya ciki, Karime na zaune tana hawaye, bayan ta gama jin abinda ya samu Aminatu
“Inno…” Tayi maganar tana kallon ta
“Bari naje Karime, idan ruwan yayi Yalwati zata yi miki.”
Daga kai kawai tayi, tana share hawayen tausayin yar uwarta. Mayafinta ta dauka, ta dauka yan kudaden ta tayo waje, yara tasa suka kira mata Nura, suka nufi in da zasu samu mota. Har suka isa makarantar bata bar sake-sake ba, wani irin tausayin ta take ji, tabbas tasan ita ce Ummul abaisin halin da Aminatun ke shiga, sai dai tayi nadama, duk da nadamar bata da amfani, amma tabbas tayi dana sanin abinda ta aikata, gashi Baba tun lokacin daya ji komai ya kwanta ciwo, saboda tsabar kaduwar da yayi take barin jikin sa ya shanye, ko a iya haka Allah ya barta ta gane kuskurenta, ballantana tasan akwai wasu sakamakon masu zuwa nan gaba.