DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina kwance kamar wadda aka zare wa dukka kashin jikin ta, cikina ke ta ya mutsawa kamar kayan cikin shi zasu fito, a wahalce nake fitar da numfashi ina murkususu. Budo kofar akayi na zuba musu ido, principal ce a gaba sai Inno da Nura, ganin su yasa na saki kukan da nake ta kokarin tsaida shi, da sauri suka ƙaraso wajena Inno tayi kokarin sani jikin ta.
“Sannu kinji.” Principal tayi maganar tana ajiye takardun a gefe na. Da sauri na runtse ido na ina jin kamar ta ajiye garwashi tunawa danayi da abinda ke ciki. Ina ji ta hau yi musu bayanin komai,
“Naji dadin zuwan naku, dama muna ta tunanin yadda za’a yi, tun da kunzo sai asa hannu ku tafi da ita, Allah ya kara lafiya.”
“An gode Allah ya saka da Alkhairi.”
“Amin, dan Allah a kula da ita sosai, akwai karamin ciki a jikin ta, damuwa zata iya haifar mata da matsala, duk tsanani yana tare da sauki, komai zai zamo tarihi in Sha Allah.”
Da kallo Inno ta bita, ta kasa magana sai daga kanta kawai da take a hankali, har principal din ta juya ta fita.
“Ni Nura a takardar nan ba yace babu abinda ya shiga tsakanin su bane?” Tayi tambayar tana kallon sa
“Tabbas haka yake a rubuce.”
“Allah ya kyauta.” Kawai tace tana kokarin tashi
“Ki daina kuka kin daiji me firincifal ɗin tace ko?”
Shiru nayi suka tattare komai da magunguna na Nura yasa hannu muka dau hanya.
***Tun da muka soma tafiyaa na jingina da kujerar motar, na lumshe ido na kamar mai bacci, babu wanda yayi min magana a cikin su har muka isa kauyen namu, sanda muka iso daidai gidan Bature, na bude ido na, jikina ya hau rawa na kura wa babban gate din gidan ina ganin kamar zai bude, gani nake kamar zai fito, kamar zan ganshi tsaye yana daga min hannu, sai dai kash, har muka wuce babu motsin kowa, babu alamun ma akwai mutane a ciki. Muna isa gida Inno ta gyara min hijabi na ta riko ni, ta taimaka min na fito, hannun ta cikin nawa muka shiga gidan, da sauri Yalwati ta taso, tana mana sannu da zuwa. Amsawa Inno tayi ta bude min dakin ta.
“Jeki kwanta.” Kawai tace ta rataye mayafin ta saman igiya ta nufi dakin Baba. Ina shiga na tarar da Karime da jaririnta, ta sauri ta taso ta rungume ni,sai a sannan naji wani sabon kuka ya taso min, kukan muka saka baki daya a tare, babu me yunkurin rarrashin wani, sai da mukayi me isarmu, sannan muka samu waje muka zauna, sai a lokacin Inno ta shigo, kallon mu tayi kadan ta wuce wajen daukar abu,har zata fita sai kuma ta tsaya tana duba na
“Taso ki watsa ruwa kafin magriba tayi, ke Karime miki min yaron nan a goya shi magriba ta gabato.”
“Toh.” Muka amsa a tare, ta karbi jaririn ta fita, cikin rashin kwarin jiki na mike, na rage kayan jiki na, na fito tsakar gidan, ruwa me dumi na tarar a bandakin na watsa na fito. Kayan Karime na saka na sake kwanciya a saman gadon Inno, har aka kira sallah sannan na tashi nayi na sake kwanciya, gaba daya bani da karfin jiki dana ruhi, komai baya min dad’i. A gefe na Karime ta zauna tana jijjigen yaron, kallon ta kawai nake ina hasaso hakan akai na.
“Ya sunan shi?” Na tambaye ta ina mika mata hannu ta bani shi
“Abubakar aka sa masa, amma saddiku za’a dinga ce masa.”
Shafa kansa nayi wasu hawaye suka zubo min, nima haka zan haifi abin ciki na, na raine shi ni kadai ba tare da uba ba, bansan wanne irin rayuwa kuma zan sake yi nan gaba ba, hannu na dora a saman shafaffen ciki na bayan na mika mata shi don ta bashi nono. Na shiga tunanin kalar rayuwar da zanyi. Abinci Inno ta kawo mana, na d’an ci kadan dan har lokacin cikina babu dadi, na haye gadon na kwanta ina fatan bacci ya dauke ni
***Cikin dare na kaasa bacci juyi kawai nake, na rasa abinda yake min dadi, har aka kira sallah na mike da kyar na je nayi alwala,. Bayan na idar na zauna saman abin sallar ina fadawa Allah damuwa ta, nasan shine kadai zai kawo min sauki a dukkan al’amari ne. Sai da gari yayi haske sosai sannan na kwanta, bacci ya dauke ni a take. Ina cikin baccin ne naji hayaniya sosai kamar a tsakar gidan mu, da sauri na mike zaune, Karime na gani a zaune gefe na tayi wanka tana cin dumanen tuwo.
“Sannu da tashi, ya karfin jikin?.” Tace tana min murmushi
“Da sauki, ya kwanan Saddik?”
“Alhamdulillah.”
“Su waye nake jin hayaniya a waje?” Na tambaye ta ina sake kasa kunne na sosai, tabe baki tayi kafin tace
“Dan iskan Garbatin nan ne yazo zai wa mutane hauka, amma Inno tayi maganin su ma ai, bashi da hankali wallahi sam.”
Gabana ne ya fadi nayi saurin lek’awa, lokacin suke fita daga gidan, hannu naga Inno tasa ta goge fuskar ta, ganin ta nufo dakin yasa nayi saurin komawa na zauna. Shigowa tayi tana maganganu kasa kasa, chan sai ga Nura yayi sallama a dakin.
“Wai kina kirana ko?” Yace yana zama kasa.
“Waye yayi maganar juna biyun da take dauke dashi? Kasan dai ni dakai kawai muka san maganar.”
Zaro ido yayi cikin rashin gaskiya
“Wallahi dazu ne da asubah muke maganar dawowar Aminatun da su Iro(sauran samarin gidan) shine nake basu labarin abinda ma ya faru.”
“Toh gashi nan zance ya fita gari, har mutane sun zo neman ba’a si.”
Dafe kirjin sa yayi da sauri
“Toh waya fitar da maganar kenan?” Ya tambaya yana zaro ido
“Kaine, da baka fada ba ya za’ayi har a yada, tashi kaje ni kana abu kamar ba namiji ba.”
Sum sum ya tashi ya fita, Inno tayi tsaki ita ma ta bar dakin. Kallo na Karime tayi cikin son karin bayani
“Me ya faru Aminatu? Bayan sakin akwai wani abu ne?”
Share hawayen fuska ta nayi na zauna sosai zuciya ta na min daci, a hankali na ce
“Bansan wacce kaddara ce ke tunkaro ni ba Karime, a lokacin da na gama tabbatar wa kaina da tsananin soyayya da nake ma Ya Farouk, a lokacin ya datse igiyar alakar dake tsakani na dashi, ya ruguza dukkan tanadin da mukayi wa juna. Kinsan bayan sakin har cewa yayi babu wani abu daya shiga tsakani na dashi? Bayan a daidai lokacin gwaji ya tabbatar min da ina dauke da ciki har na sati bakwai, Karime ya zanyi da rayuwata da abinda yake ciki na, bayan wanda zai tsaya min ya tabbatar da cewa babu abu tsakanin mu, ina kenan na samo cikin jikina? Wa zai karbe ni dashi?”
Kuka yaci karfin mu dukka, tasowa tayi ta zauna daf dani tana sharen hawayen fuskata
“Kiyi hakuri, tabbas ba’a kyauta miki ba, kuma an zalunce ki, amma bak’ya tunanin akwai sa hannu wani a cikin wannan al’amarin? Kina ganin Farouk zai miki haka kuwa?”
Girgiza kai na nayi cikin kuka nace
“Idan ma sharri akayi masa, yana ina yanzu? Me yasa be zo ya wanke kansa ba? Bayan haka rubutun dake jikin takardar nashi ne, rubutun sa ne Karime, ya kike tunanin bazan yarda ba?”
“Duk da haka, ya kamata ayi bincike sosai.”
“Babu wani bincike da za’ayi, aikin gama ya riga ya gama, abu daya na kasa ganewa, laifin me nayi masa da har zai min wannan hukuncin? Menene matsalata?”
Share hawaye nayi na mike ina komawa jikin tagar dakin,
“Amma ba komai, na gode masa sosai da dukkan sadaukarwar sa gareni, hakika ba zan taba mantawa dashi a cikin jerin mutane masu matukar muhimmanci a rayuwata ba, ina jin kamar nunfashi na zai bar gangar jiki na Karime, zuciya ta tana min zafi.”
“Kiyi hakuri, karki tsananan ta damuwa ko dan abinda ki cikin ki.”
Sosai Karime ta shiga rarrashi na da ban baki, haka dai nake bin ta da ido kamar mutum mutumi, bata hakura ba har sai da saddiku yayi kuka sannan ta kyale ni. Wanka na fara yi na sha kunu wanda shi kadai ne zai iya zama a ciki na a halin yanzu. Wajen azahar sakon kiran maigari ya riske mu. Sai da akayi la’asar sannan Inno tasani a gaba tare da k’anin Baba muka tafi, duk inda muka wuce sai munga ana kallon mu ana magana kasa kasa. Haka muka isa wajen, daga gefe muka zauna muka gaida maigari sannan ya soma magana cikin dattaku.”