DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Jiya wasu mata sunzo har nan sun same mu, sun gabatar da takardar sakin Aminatu daga wajen mijinta Farouk, bayan nan suka dora da bayanin su kafin sukayi sallama suka tafi. Toh bayan tafiyar su, nasa an karanta min abinda takardar ta kunsa, daga nan na yanke shawarar kiran mahaifin yaron, dan jin abinda yake faruwa, tunda ance ta inda aka hau ta nan ake sauka. Toh bayan kiran shi ne yake nuna min shi sam be san da maganar ba, hasalima shi rabon shi da yaron an kwana biyu, sai dai ya bani hakuri da alƙawarin zai samu lokaci ya shigo. Toh kuma yau sai ga maganar juna biyu ta riskeni, sai na sake komawa baya abinda yake rubuce a takardar nan da suka kawo, in da yaron ya nuna babu wata alaƙa data shiga tsakanin su, shine abin ya daure min kai, na bukaci naji daga gareku, kafin zuwa Mahaifin yaron ko yaron, mu san abinda ake ciki.”

Runtse ido na nayi ina karanto duk addu’ar datazo baki na, idan har Farouk be zo ba, be kuma ƙaryata abinda ya rubuta ba, ana nufin za’a sheganta min abinda ke cikina kenan? Wannan wacce irin masifa ce ta kunno min?

“Aminatu…” Maigari ya kira sunana, ban iya amsawa ba sai dagowa da nayi kawai ina goge fuskata.

“Abinda mijinki ya rubuta shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba?”

A hankali na bude baki na cikin tsananin kukan da ya soma cin karfi na nace

“Ba… gaskiya bane.”

Gid’a kansa yayi cikin gamsuwa yace

“Shikenan, in Sha Allahu komai zai warware kinji, kiyi hakuri.”

Da kai na amss kawai, ya karasa bayanin sa sannan ya sallame mu.


Ransa a matukar bace yake kutsa kansa falon, tana zaune hannun ta rike da babban tasbah tana ja, tana ganin shi ta fadada fara’a ta

“Soja mazan fama.”

Yake yayi kawai ya ƙaraso ya samu waje ya zauna

“Dadah, me yaron nan yake so ya zama?”

Ya ambata yana jan karamin tsaki

“Wanne yaro hala? Ja’afaru ko wa?”

“Farouk!”

“Toh me kuma Babana yayi ehe?”

Cire hular kansa yayi ya ajiye yana goge gumin kansa

“Wallahi wai ya saki yarinyar nan.”

Da sauri ta dafe kirjin ta

“Innalillah wa inna ilaihi raji’un! Saki!!! Yaushe?”

Tsakin ya kara ja yana duban kofa

“Dazu maigari ya kirani wallahi, kuma abin takaice wai aikawa yayi da takardar,ba shine da kansa yaje ba, gashi duk numbobin sa na kira a kashe balle nasan ta ina zan fara, ni rabona ma dashi tun zuwan da yayi karshe yace an tura shi wani aiki.”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, yau me zanji, wanne irin abu ne wannan? A lafiyar sa kuwa? Kai da sake gaskiya, bana jin Babana zai aikata makamancin wannan.”

“Dadah dan yau fa, halin su sai su.”

“Duk da haka Kabiru, sam ban yarda Farouk zai aikata ba, aikuwa ba dan dare yayi ba a yau zan bar garin nan, amma tabbas gobe da izinin Allah ina chan, hankali na ba zai kwanta ba sai na ji komai, ka cigaba da kiran wayar tasa ko zaka samu kaima.”

“Allah ya kaimu, nima zuwan ya kamani, ina ganin ki fara zuwa sai na biyo ki jibi, dan akwai ayyukan da zan karasa goben, amma idan na koma zan shiga gidan Aboki, zan sanar masa abinda yake faruwa, shine me yabon faruk yanzu sai yasan abinda ya sake aikata bayan na dah, idan yaso sai mu tafi taren musha kunyar a tare, dan bazan iya kallon mutanen nan ba wallahi, da kunya ana ganin mutuncin ka.”

“Duk yadda kayi yayi, amma ni kam gobe zan isa da izinin Aallah.”

“Allah ya kaimu, sai ku tafi Ja’afar da driver ko?.”

“Amin, yayi hakan.” Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba, ina alkawarin da yayi mata na cewa duk ranar da Aminatun ta gama karatu zai dawo da ita wajenta, su zauna tare har zuwa lokacin da shima zai nemi transfer ya dawo nan ɗin, me ya faru da babban alkawarin da yayi na taimaka mata wajen hada ta da dangin ta? Kai akwai lauje cikin nad’i, tabbas wannan makirci ne aka shirya, sai dai kai tsaye Mum ce ta fado mata arai, tasan zata iya aikata fiye da hakan ba, amma dai koma menene, zata je taji.


Alhamdulillah, nagode kwarai da addu’oin ku ???????? Allah saka da Alkhairi.

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
 
                 
: ©️ HAFSAT RANO

    THE HEART BREAK????????????????

                (14)

***Dauke nake da Saddiku ina dan jijjigashi, rabi da kwata na hankali na yana kan tunanin abubuwan dake faruwa dani, sallama Karime tayi daure da zanin wanka ta lullube saman kanta da wani, kallo na yayi ganin yadda nayi firgigit jin sallamar ta.

“Tunanin dai ko Aminatu, kifa saukaka ma ranki kar ki jawo wani ciwon kuma.”

Yake nayi wanda aka ce yafi kuka ciwo na zauna sosai ina kwantar da Saddiku, zaman tayi itama ta hau shiryawa bata sake min magana ba, tashi nayi na fito, nayi fitsari na dan leka dakin Baba, yana kwance idanun sa a bude, na k’arasa na tsuguna gaban sa

“Sannu Baba.” Nace ina maida kwallar ido na, bina yake tayi da ido babu halin magana, shiru nayi ina tunanin yadda mutum zaiyi rayuwa a haka, tabbas ba karamin jin jiki yake ba, gashi babu wanda zai taimaka masa da  zuwa asibiti, Farouk ne ya fado min, na tuna da yananan yanzu, xan iya neman alfarmar sa ya taimaka masa. Na jima a dakin ina zaune dashi har saida Inno ta kwala min kira, da sauri na tashi na fito, sai nayi turus ganin Dadah na kokarin shiga dakin Inno, gani na yasa ta dakata, ganin haka yasa nayi saurin isa gareta, bansan sanda na fada jikinta ba, na saka kuka sosai. Rike ni tayi muka karasa shiga dakin har lokacin kukan nake, gaishe ta Karime tayi ta tashi ta fita don bamu waje. Tabarma Babba na dauko na shinfida mata, na fita da sauri na debo mata ruwa na ajiye a gaban ta sannan na zauna ina sauke kaina kasa.

“Aminatu, sannu kinji.”

Hakan data fada yasa naji zuciya ta ta sake yin rauni, tabbas ni ɗin abar a tausaya min ce,

“Sannu da zuwa Dadah, ina wuni?”

“Lafiya kalou Aminatu, mun same ku lafiya?”

“Alhamdulillah.”

Nace ina wasa da hannu na. Inno ce tayi sallama ta shigo Yalwati na bin bayanta, a mutunce suka gaisa kafin su tashi su fita. Muskutawa tayi kadan tana dubana sosai.

“Aminatu me yake faruwa? Me ya hada ki da Babana.”

Ta jeho min tambayar ta na riga nasan da ita, kallon ta nayi zan cigaba da kukan da nake ta dakatar dani,

“Kul kina kuka, akan me? Fada min gaskiya me ya faru, kunyi fada ne ko kin masa wani laifin ne?”

“Allah banyi masa komai ba, hasalima rabona dashi tun ranar daya maida ni makaranta, yace sai ranar da muka gama exams zai zo, toh kuma ni tun bayan nan sau biyu mukayi waya, daga nan bamu sake magana ba.”

“Zaki iya dauko min takardar da aka kawo miki?”

“Eh.”

“Toh bani na gani.”

Tashi nayi na bude jakar da nazo da ita na dauko, na fito da takardun guda biyu, kura musu ido nayi a tare, sai kuma na juya na mika mata su dukka ina jin wani iri, karba tayi ta bude ta farko me dauke da sakamakon test result dina, a fuskar ta naga yanayin da take ciki, sosai naga ta sake sakin fuskar fiye da yadda take a baya, ninkewa tayi ta ajiye ta bude dayar, ta jima tana dubawa kamar ne son gano wani abu kafin ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button