DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Waye ya kawo miki wannan?” Ta nuna takardar sakin
“Bansan waye ba nima, nasan dai wata mota ce ta shigo makarantar mu, ina kallo ta bawa security man din dake wajen shi kuma ya kawo min, sai dai tabbas mace ce dan naga hannun ta.”
“Baki ga fuskar ta ba kenan?”
Girgiza kai na nayi
“Ban gani ba, amma ance tazo gida ma bayan ta je makarantar.”
“Nan gidan?” Ta tambaya da sauri.
“Eh ance tazo, kuma maigari ma yace sunje chan wajen sa sun kai masa.”
“Good, kira min Maman taku.”
Tashi nayi tsam naje na kira Inno, a tare muka shigo na samu gefe na zauna.
“Ko zaki iya gane matar data zo dan Allah?” Tayi maganar tana kallon Inno
“Zan gane ta.”
“Yawwa.”
Ciro wayar ta tayi ta budo wajen hotuna ta fara nuna wa Inno, duk wadda ta nuna mata sai tace ba ita bace. Ajiye wayar tayi tana murmushi
“Aminatu samu yaro yaje waje ya kira min Ja’afar, suna nan a mota.”
Tashi nayi na fito, babu yaro ko daya duk Inno ta kora su waje, hijabin jikin Karime na karba na leka da kaina na kirawo shi. Gabana ne ya fadi da ya fito, sosai yayi min kama da Farouk, sai dai shekaru da Farouk zai fishi da girman jiki.
“Sannu, Dadah ke kiran ka.”
“Owk.” Yace yana biyo bayana, tsayawa yayi a tsakar gidan na shiga na fada mata gashi, Inno ce ta daga labule tace ya shigo, a gefen tabarmar da Dada ke kai ya zauna yana gaida Inno din, amsawa tayi kafin Dadah tace
“Kana da hoton Abidah a wayar ka ko?”
“Ina dashi.”
“Yawwa mu gani.”
Budowa yayi ya mika mata, ta kalla ta mika wa inno,
“Wannan fa?”
Girgiza kai Inno tayi tace
“Gaskiya ba ita bace.”
“Owk shikenan Ja’afar, zaka iya tafiya.”
Tashi yayi ya fita, Dadah ta cigaba da nuna wa Inno dukkan hotunan data ke tunani, amma sam Inno bata ga matar ba, a dole Dadah ta hakura da tunani shin wacece? Ganin ta kasa gane wacece yasa ta yi mana sallama bayan ta sa yara sun shigo da kayan data kawo min ta tafi, da nufin zata dawo gobe idan Allah ya kaimu. Har waje na rakata ina jin kamar na bita, sai dai nasan hakan ba mai yiwu wa bane.
Sosai Dadah ta shiga damuwa, babu abinda yafi daga mata hankali sama da abubuwan da takardun nan guda biyu suka kunsa, abubuwa biyu dake da alaƙa da juna da siga daban, idan har ya tabbata Farouk shine yayi sakin ya kenan za’a yi? Bin Ja’afar tayi da ido har ya karasa shigowa cikin falon.
“Wash.” Yace yana fadawa saman kujerar.
“Daga ina kake haka kai kuma?”
“Wallahi Dadah zagaye nayi a gonar nan, sai naga girman ta ya karu sosai fiye da dah, ko dan na jima banzo bane ba oho.”
“Sai dai hakan, amma ai yadda take haka take, kawai son jikine irin naka.”
“Yawwa kai, nace yaushe rabon ka da Babana ne wai?”
“Wai ya Farouk?”
“Bansani ba.”
“Sorry, a satin nan ma munyi magana ai.”
“Da gaske ko da wasa?”
“Wallahi, kinsan baya kasar sannan inda yake babu wani network me kyau, nima Amal ce ta bani number tasa lokacin da Mummy ta kirani akan bata samun shi a waya, shine na kirashi, wajen kwana huɗu ma ina gwada kiran kafin ta shiga.”
“Ina number, maza bani ita.”
“Owk bari na dauko wayata a ciki na barta.”
Mik’ewa sukayi a tare ya nufi dakin sa, a tsaye Dadah take har ya dauko ya dawo, hannun ta rike da wayar ta. Number ya karanto mata ta saka sannan tayi dialing, bugu daya ta shiga, zama tayi da sauri tana saka ta a handfree, sai dai har ta gama ringing din bai daga ba, cigaba tayi da kira, babu alamun za’a daga ɗin, haka ta hakura ta bari anjima ta sake gwadawa.
“Be d’aga ba.”
“Kila baya kusa ne, idan ya gani zai kira nasan.”
“Ina ita Abidar take, tana Kaduna ne ko Abuja?”
“Wai Mummy, ina ga tana Lagos, yanzu tafi zama a can ai saboda bussiness ɗin nata yafi a chan haka.”
“‘Owk yayi, ka gwada kira min shi zuwa anjima idan ya dauka ka haɗa ni dashi.”
“Ok Tam, bari na shiga na huta.”
Barin falon yayi itama ta wuce dakin ta tana samun magana da Farouk din kafin wayewar gari. Tun tana saka ran zai kira har ta hakura ta kwanta, da safe wajen karfe goma Daddy ya iso, dama shi akwai shi da sammako saboda yanayin abubuwan nasa, zuwa sha-daya suka isa gidan Maigari, ciki maigari ya shiga dasu ya tura kiran su Inno. Lokacin ina zaune muna yar hira da Karime sakon kiran yazo, Hjabi na kawai na dora a saman kayan jiki na muna tafi gabana na ta faduwa. Cikin gidan muka shiga, yanayin takalman da na gani a kofar dakin tasa jikina ya ɗan soma rawa, rike ni Inno tayi muka shiga da sallama, duk suka zubo mana ido, a darare na zauna gefen Inno kaina a kasa na gaishe su, sannan suka gaisa da Kawu kanin Baba da Inno. Kamar wanchan karon yanzu ma maigari ne ya sake sabon jawabi, sannan ya bawa Daddy damar jin ta bakin sa. Wayar Dadah ce ta dau burari alamun kira ya shigo, dan dakatawa Daddy yayi ta ciro wayar, da sauri ta furta
“Alhamdulillah.”
Ta daga ta saka ta a handfree
“Assalamu alaikum.”
Muryar sa ta daki dodan kunne na, wani irin zabura nayi daga zaune, kowa ya zuba wa wayar ido kamar shi din ne a wajen. Daddy ne ya mika hannu ya karbi wayar
“Kana jina?”
“Daddy barka da warhaka, ina kwana?”
“Lafiya, kana jina, ba wani dogon bayani muke bukata ba, ina fatan kana hayyacin ka dai ko?”
“Eh daddy, a hayyacina nake.”
“Good, menene hakikanin gaskiyar takardar sakin daka aiko wa matar ka?”
Shiru yayi, kamar baya kan layin, har sai da Daddy yace
“Kaji abinda nace ko?”
“Naji Daddy.”
“Toh ina jinka, me ya faru ka sake ta? Wani laifin tayi maka ne ko menene?”
Kai tsaye yace
“Babu laifin komai, kawai zaman mu ne ya kare.”
Da sauri na dago, Ina son sake tabbatar wa kaina wannan ba Farouk d’ina bane.
“Haka kawai kenan ka sake ta ba tare da laifin komai ba ko me?”
“Eh haka nan ne, babu laifin da tayi mun.”
Share zufa naga Dadah nayi, Inno kuwa kamar bata wajen, kuma baka isa ka gane yanayin da take ciki ba, ni kuwa sai naji kamar yanzu ne komai yake faruwa, jikina har rawa yake, na kasa yarda da abinda kunnuwa na ke jiye min, ina kallo Dadah ta karbi wayar cikin bacin rai tace
“Babana kaine kuwa? Kasan me kake cewa? Kana nufin duk abinda ke jikin takardar kaine ka rubuta shi? Kuma shine gaskiyar abinda yake faruwa?”
Babu ko digon tsoro balle damuwa a cikin muryar sa, kai tsaye yace
“Ni ne da kaina, kuma duk abinda ke rubuce a ciki shine gaskiyar magana, kuyi hakuri idan na bata muku, Allah ya huci zuciyar kowa.”
Kafin ta samu damar sake wata magana kiran ya katse, da sauri tayi kokarin sake kira Daddy ya dakatar da ita.
“Karki kirashi Dadah, barshi kawai, ni ya wulakanta ya nunawa duniya ban isa dashi ba, babu komai amma..”
“Kayi hakuri Alhaji, yaran yanzu ne sai addu’a, idan ka biye tasu sai kayi musu mugun baki.”
Mai gari ya katse shi, sannan ya maida kallon sa wajen da muke zaune
“Toh kun ji dai daga bakin yaron, duk da dukkannin mu babu wanda zancen nasa yayi wa dadi, amma dole haka zamu hakura, aure ya riga ya kare, dama shi raine dashi, idan kwanan sa ya kare ko ana so ko ba’a so dole a hakura.”
“Amma ba wai na katse ka bane, yarinyar nan fa tana dauke da juna biyu, ya kamata a duba lamarin nan.”
Kawu yace yana duban maigari da Daddy,
“Juna biyu !” Suka hada baki a tare cikin tsananin mamaki
“Tabbas tana dauke da juna biyu, ni da kaina naga sakamakon gwajin da akayi mata.”
A cewar Dadah tana duban Daddy.
“Amma shine yaron nan zai maida mu yan iska? Lallai ma wallahi, dani yake magana.”