DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Yayi maganar a fusace
“Mubi komai a sannu Alhaji, idan yaso sai a sake tuntubar shi yaron kan maganar cikin.”
A cewar maigari.
“Babu bukatar hakan dan yaro ya riga ya nuna baro-baro babu wani abu da ya hada shi da ita, dan haka magana ta kare.”
Duk muka juyo da sauri, Mummy ce tana tsaye tayi kyau ainun cikin shigar alfarma, kallon juna sukayi ita da Dadah, kafin cikin bacin rai Daddy yace
“Me kike yi anan Abidah?”
A gadarance tace
“Abinda ya kawo ka, shi ya kawo ni,kasan dai ina da hakki akan Farouk ko? Wanchan lokacin na kyale ka da kayi kokarin bata min rayuwar yaro, akayi masa sharrin da kai kanka kasan ba shine ya aikata ba. Shine yanzu za’a sake ruguza min rayuwar sa bayan Allah ya taimake ni ya gane gaskiya, naji komai a wajen Ja’afar tun ranar da abin ya faru, har zuwa zaman da zakuyi anan ɗin, dalilin zuwa na kenan saboda na karba wa d’ana yanci.”
“Danki? Ashe dama kina da d’a?”
“Kafi kowa sani ai, bani da lokacin amsa maka wannan tambayar, maganar d’ana nazo, babu kuma uban da ya isa ya tilasta masa aikata abinda beyi niyya ba.”
Kasa magana Daddy yayi saboda tsananin kunyar data rufe shi, kasa yayi da kansa kawai yana jin kamar kasa ta tsage ya shige, jawabi ta shiga korawa maigari, a karshe tace Farouk ba zai karbi cikin jikina ba dan ba nashi bane. Tun da ake maganganun nan jikina yake rawa kamar mazari, tuni zuciya ta ta kekashe, hawayen dake faman kai kawo a saman fuskata ya bushe, cikin dakiya na tashi, na isa tsakiyar wajen, hannu na biyu na hada waje daya cikin wani irin yanayi nace
“Ina rokon duk wanda yake wajen nan, da yayi hakuri, da abinda yake faruwa, ni kaina bansan menene matsalar ba, sannan ina neman wa Ya Farouk afwa wajen ku iyayensa, tabbas bashi da laifi ko daya a cikin duk wani abu da ake tuhumar sa, hasalima shi taimako na yayi. Daga rana irin ta yau na bar maganar nan, zan cigaba da rayuwa ta a matsayin wadda bata taba sanin shi ba, zan manta dashi, zan cigaba da rainon abinda ke cikina, har zuwa ranar da zai zo duniya, ina fatan hakan ya faranta wa kowa.”
Ina kaiwa nan na juya da sauri, zuciya ta na tafasa na bar dakin, ina ji suna kwala min kira, ban saurara ba, dan bana jin zan iya sauraron duk wani abu da zasu ce min, maganar da akayi da ya Farouk a waya kadai ta isheni, bana bukatar jin sauran wani bayani, a yau na tabbatar da na rasa shi, rashi na har abadah, zan sake sabuwar rayuwa, duk da bazan ce zan manta dashi a rayuwa ta ba, amma tabbas zan ajiye dukkan shafukan rayuwar mu tare a baya, zan bude sabon shafin rayuwar da bani da masaniyar in da zata kaini.
“Aminatu ina so kiyi karatu, ina so ki zama abar alfahari sanda zaki sadu da sanyin idaniyar ki.”
Wadannan sune maganganun sa a kullum gareni, wanda bani da masaniyar hakikanin abinda suke nufi, sai dai yau nayi wa kaina alkawarin, zan dauke su a matsayin wani tsani na matakin rayuwar da zan shiga anan gaba.
Hanya kawai nake haɗawa da taimakon Allah na isa gida, da sauri Karime ta tare ni, tana kokarin rikeni na raba ta gefen ta, na shiga daki na hada kaina da guiwa ta cikin rashin sanin makomata. A kaina tazo ta tsaya tana min magiyar na sanar da ita abinda yake faruwa, ban iya ce mata kala ba, har ta gaji ta samu gefe na ta zauna tana rafka tagumi.
A tare suka shigo gidan, kai tsaye dakin Inno suka shigo, Dadah ta ƙaraso gareni tana daga ni.
“Aminatu tashi zakiyi mu tafi, mun gama magana da Maman ki, ba zan iya kyale ki ki raini cikin nan ke kadai ba, maza tashi kinji.”
Janye jikina nayi a hankali na matsa gefe ina kallon ta
“Kiyi hakuri Dadah, ba zan biki ba, na gode da hallacin da kuka nuna min, sai dai na yanke shawarar nesantar duk wani abu daya danganci Ya Farouk, ina ganin hakan da zanyi shine kawai mafita a garemu, kiyi hakuri.”
“Ya zaki ce haka, kina nufin kin karaya, kin hakura kenan? Ni sam ban yarda da Farouk zai aikata ba, akwai dai matsala, ki bini muje in Sha Allah zamu gani bakin zaren.”
“Kiyi hakuri dan Allah, ba zan iya binki ba, hakan na iya haifar da matsala gagaruma a cikin ahlinki, sannan Mummy, ba zata taba karba ta ba, zan yi rayuwa ta, zan zauna anan, tare da yan uwa na dan Allah.”
“Aminatu…”
K’asa na tsuguna ina kama kafarta
“Kiyi hakuri Dadah, kiyi hakuri.”
Kuka ta saka, ba tare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar dakin.
“Ya Allah!” Na furta da karfi ina zama a kasa, kaina kamar zai rabe biyu saboda tsananin ciwo. Matsowa Inno tayi tana kallo na
“Kin tabbata ba zaki bita ba, zaman nan ba zai miki dadi ba, kinga yanzu da dah ba daya bace.”
Girgiza kai na nayi,
“Kiyi hakuri, amma bazan bita ba.”
“Shikenan, ki daina kuka kar kanki yayi ciwo, tashi ki kwanta a saman gadon, zanje na yi mata bayani yadda zata gane.”
Tashi nayi jikina na rawa na hau gadon na kwanta ina lunshe ido na.
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
8/a: ©️ Hafsat Rano
15
Duk hidimar da ake a gidan ban mik’e daga kwanciyar da nayi ba, sake juyawa nayi na maida kaina dayan barin, daga daren jiya zuwa yau na riga na gama yanke wa kaina hukuncin da nake ganin shine zaiyi daidai da rayuwata. Tsawon lokaci na dauka Ina kwancen har lokacin da Inno ta shigo dauke da kwano, a kusa da kafata ta ajiye ta.
“Tashi maza, kici abinci sai kuje chan gidan ki dauko abinda zaki dauka.”
“Toh.” Nace ina tashi, ajiyar zuciya na sauke na jawo kwanon, fara fita nayi na wanke hannu na da bakina na dawo na zauna na shiga cin abincin a hankali, ina gamawa na chanja kayan jikina, na zura hijabi da takalmi na fito. Dakin Baba na shiga na gaida shi na duba jikin shi sannan muka tafi nida Yalwati. Da yake safiya ce bamu hadu da wasu mutane masu yawa ba muka isa gidan, sojoji ne tsaye a gate din, sai Ja’afar dake magana da daya daga cikin su,yana hango mu ya taho yana fad’ad’a fara’ar fuskar sa.
“Sannun ku da zuwa.”
Yace yana tsayawa a gabana, sai dana dan ji wani iri dan sosai suke yanayi da Ya Farouk, dakewa nayi muga gaisa, yanayin yadda yake kallo na yasa na dan ji babu dadi, nayi kasa da kaina har muka shiga gidan ban dago ba. Daddy na zaune suna magana da Dadah muka shigo, da sauri ta mike tana riko ni fuskar ta kamar zatayi ne saboda tsananin farin cikin ganin mu
“Aminatu, kin chanja shawara ko?” .
Yadda tayi maganar cikin farin ciki yasa naji kunya, a hankali na zame jikina na tsuguna a kasa na furta
“Ina kwana Dadah?”
“Lafiya lou Aminatu, nasan dama zaki chanja shawara, Nagode sosai da kika yarda zaki bini.” Sai ta maida hankalin ta kan Yalwati cikin fara’a tace
“Sannun ku da zuwa.”
“Yawwa ina kwana Hajiya.”
“Lafiya lou, ku zauna mana.”
Zama tayi a kujerar dake hanya ni kuma na sake gyara zamana a kasan da nake.Sabuwar gaisuwa suka sake sannan suka gaisa da Daddy da ya gama waya. A hankali na dago kaina na cikin girmamawa na gaishe shi, a sake ya amsa yana nazarina. Komawa Dadah tayi ta zauna sannan tace