DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

BAYAN WATA SHIDA
Haka rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji Ranar wata talata Inno ta fita sayo kaya,tun safe ta fita sai wajen Magriba ta dawo, yanayin ta kawai na kalla na tabbatar babu lafiya, a gefe kawai ta ajiye kayan ta fada banɗaki, ta jima ciki sannan ta fito, dakin ta ta wuce ta kwanta, ina ganin haka na mike na bita dakin, tayi nisa a tunanin ta na shigo, tana gani na ta tashi tana kokarin fita daga dakin,
“Inna bak’ya jin dadi ne?”
“Gajiya ce kawai, sai dan ciwon kai.”
“Allah ya sauwake, bari na dauko miki paracetamol kisha.”
Nace ina barin dakin, biyo baya na tayi, ni kuma na shiga daki dan dauko mata, a bakin rijiya na ganta tana alwala, tsayawa nayi ta gama sannan na bata maganin, balla tayi tasha ta wuce daki zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallah. Alwalar nima nayi na wuce daki dan yin sallah.
Tsawon sati guda kenan Inno na cikin zulumi, tun ina tambayar ta har na hakura na zura mata ido kawai ina alakanta hakan da yanayin jikin Baban.
Muna zazzaune a tsakar gidan ana yar hira, Baba na daga kofar dakin sa saboda yanayin da ake na zafi akan fito dashi shima yana shan iska. Shigowar bakuwar dauke da sallama ya saka Inno kusan sakin fitilar k’wan dake hannun ta.
“Harira!” Ta furta cikin tsananin mamaki
“Nice nan Innaro, kinga bakuwar daree ko?” Tayi maganar cikin wani irin salo dauke da yar karamar dariya.
“Muje ciki.” Inno tace tana saurin fadawa dakin ta, bin bayanta tayi, a hankali naji an turo kofar dakin alamun an rufo ta, mamaki ne ya kamani, na dan muskuta kadan ina tunanin abinda ya kawo matar, a yanayin Inno kawai ya nuna batayi maraba da zuwan nata ba. Tsawon lokaci suka dauka sai tashin magana k’asa k’asa, chan suka fito tare, Inno sanye da hijabi suka fita tare. Har wajen tara shiru bata dawo ba, ina ta sake-saken abinda yake faruwa sai gata ta shigo. Bata yi wa kowa magana ba ta wuce ciki, har zan bi bayan ta sai kuma na fasa ina kunna Radio cikin wayata. Washegari na tashi bani jin dadin jiki na kwata-kwata. Tun bayan dana shiga wata na takwas nake jin wani iri, haka dai na lallaba na d’anyi abinda zanyi, na koma na kwanta. Shigowar Inno dakin yasa na tashi da kyar ina kallon ta, zama tayi a gefen yar katifar tawa, hankalin ta sam baya jikin ta. Kallon idon ta nayi naga yayi ja, sai duk naji babu dadi.
“Dan Allah menene yake faruwa inna? Kullum baki da nutsuwa kamar ma baki daa lafiya ne.”
Gyara zaman ta tayi, ta dube ni a nutse tace
“Abubuwa ne da yawa suka tarar min Aminatu, sakamakon abinda na aikata ne yake bibiyata, dan Allah dan Annabi ki yafe min, na zalunce ki ban miki adalci ba, saboda son zuciya irin tawa, ki yafe min dan Allah…”
“Inna? Me Kika yi min haka har zaki bani hakuri, ni wallahi bakiyi min komai ba, iyaye ai basa taba laifi a wajen ƴaƴansu, nice ma zan nemi gafararki, watakila na miki wani laifin ne da yasa ki a halin da kike ciki.”
“Kayya, Aminatu. Nidai dan Allah ki yafe min, kuma kiyi min alƙawarin zaki karbi hukuncin dana yanke akanki, shine kadai abinda zan miki na ceceki daga hannun azzalumai.”
“Ban gane ba inna.”
“Karki damu, yau in Sha Allah zakiji komai, banso sanar miki ba, amma ya zama dole idan ina so na samu sauƙin abinda na aikata.”
Daga haka ta tashi ta bar dakin. Kasa binta nayi kawai ina tunanin maganganun ta, ban gane komai ba sai ma toshewa danaji ƙwaƙwalwa ta na neman yi. Mik’ewa nayi da nufin binta naji marata ta rik’e. Komawa nayi na zauna ina yarfe hannu. A hankali naji ta fara saki, na yunkura da kyar na fito, dakin dana gani a rufe yasa na gane ta fita, komawa nayi na haye saman katifa ta na cigaba da juyi ina tunanin maganganun.
La’asar likis ta shigo gidan a matukar gajiye, dakin da nake ta nufo, sallama kawai tayi ta shiga hade min yan abubuwa na waje daya, duk da dama ba wasu kaya bane masu yawa, cikin kankanin lokaci ta gama ta ajiye su a gefe sannan ta fita, cigaba nayi da kwanciyar kawai na zuba wa sarautar Allahu ido, chan ta shigo ta dauki kayan ta sake fita, bansan me hakan ke nufi ba. Da kyar na tashi na gabatar da sallah, idarwa ta kenan ko hijabin ban cire ba Inno ta sake shigowa, hannu na naga ta kama.
“Tashi Aminatu, lokaci na kurewa.”
Mik’ewa nayi da d’an karfi na ta shiga jan hannun nawa, hanyar waje naga tayi dani, na cigaba da binta, motar dana gani ce yasa gabana faduwa, bude min tayi Na shiga sannan itama ta shigo, tana rufewa me motar yaja muka bar kofar gidan.
Tafiya mukayi sosai babu wanda yayi magana a cikin su har sai da muka fita daga kauyen namu muka isa babbar tasha, gefe ya samu ya faka ya kashe motar ya fita daga ciki ya bar mu. Yana fita Inno ta juyo tana kallo na
“Inna dan Allah me yake faruwa?”
Kasan kafarta ta zura hannu, sai ga jakar da ta jima tana ajiyar ta, akan cinyata ta ajiye min tana kokarin maida kwallar fuskar ta
“Gashi nan Aminatu, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba, na raba ki da dukkan farin cikin ki, ta hanyar rabaki da ainihin iyayenki….”
Ras gabana ya fadi jin abin tace, wani irin juyi naji cikana yayi, nayi saurin dafe wajen ina zaro ido
Bayan hannun ta tasa ta share fuskar ta
“Labari me tsawo Aminatu, sai dai wallahi tallahi yaudara ta sukayi, ba tare da sanin komai ba, na amince musu, nayi dana sani Aminatu, nayi dana sani tun ba yau ba, Allah ne shaida ta. Kiyi hakuri da abinda zan sanar dake, bani na haife ki ba, hasalima bansan iyayenki ba. Rana daya muka haihu da mahaifiyar ki. Sai dai ni haihuwa nayi da kaina ita kuma aiki akayi mata. “
“Watarana naje asibitin ganin likita, a lokacin cikina wata tara har da doriyar yan kwanaki, tare da kawata Harira data rakani, muka hadu da wata Hajiya, kana ganin ta kasan hamshakiyar mata ce, wadda ta jiku da kudi da jin dadi, yadda take ta kallon mu, yasa na dan zargu amma na share. Sanda muka zo tafiya ne ta tsaida mu, ta kira Harira gefe, sun jima suna magana har na gaji na zauna, sannan tazo muka tafi. Kwana biyu tsakani Harira ta bijiro min da maganar data firgita ni, da farko sam ban amince ba, amma yadda ya dinga kwadaita min abubuwan Alkhairin da zamu samu, naji na amince da bukatar su ta indai namiji na haifa zan basu, su kuma su bani tasu indai mace ce. Sai dai na kafa sharadin ba za’a dau lokaci ba zasu dawo min da d’ana, da farko matar bata amince ba, amma da Harira tayi mata bayani sai ta yarda. Bansan me ya faru ba ranar ina kwance sai ga Harira dauke da magani, ta kawo min wai nasha, ban kawo komai ba nasha, kafin wani lokaci na fara nakuda, da kanta ta dauke ni muka nufi asibiti, muna zuwa aka ce haihuwa ce aka shiga dani. Ban dau tsawon lokaci ba na haifo dana namiji, kukan sa kawai nake iya tunawa da yake min amsa kuwwa Harira ta dauke shi ta fita dashi, jim kadan ta dawo dauke da ke, da wannan jakar wadda ke dauke da manyan kudade masu yawa da tsoratarwa, haka ina ji ina gani aka tafi da d’ana, aka bar min ke. Bansani ba ashe Harira yaudara ta tayi, bata san su ba, bata taba ganin su ba sai ranar da muka hadun nan asibiti. Kiyi hakuri tabbas an zalunce ki, duk da bansan alakar ki da matar data tsara wannan abin ba, amma tabbas mahaifiyar ki bata da masaniyar abinda muka aikata.”