DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Saboda tsananin kukan da nake muryata ko fita batayi, bansan a wanne mazauni zan dauki zancen na ajiye shi ba, ji nake kamar zan haukace saboda tsabar firgice, sama sama numfashi na yake fita. Duk addu’ar data zo baki na na shiga karanto wa, ina kokarin ganin na saita kaina

“Kiyi hakuri, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba. Bamu da lokaci Aminatu, ga jakar ki nan, da duk kudin dana karba wajen iyayenki, kiyi amfani dasu, domin sanar wa kanki rayuwa me kyau, Harira ta kulla wani babban abu, da bazan iya barin ta aiwatar wa ba, kuma bani da hujjar da zan ƙaryata ta, ko na nuna wa duniya ainihin wacece ita, rayuwar ki na cikin hatsari idan kika zauna anan, zan sauka na koma daga nan, ki kula da kanki, ki kula da kanki. Allah yayi miki albarka.”

Kukan ne yaci karfin ta, ta shiga yin shi babu kakkautawa. So nake nayi magana, so nake nace wani abu, amma na kasa, na kasa samun harafi kwaya daya da zai samu zama akan harshe ne har na iya furta shi. Ina jin ta ta bude kofar ta fita, cikin dakiya tace

“Sai watarana Aminatu.”

Sai a sannan naji karfi yazo min, na yunkura da sauri na balle murfin motar na fito.

“Inna…” Na kwala kiran da dukkan karfin muryar ta, chak ta tsaya, da tafiyar da take batare da ta juyo ba, k’asa daga kafa ta nayi, hankali naji wani abu kamar ruwa yana bina. Cigaba tayi da tafiyar ta, ina kallo ta bacewa gani na. A wajen na durkushe ina jin numfashi na yana barazanar barin gangar jikina.
Sama sama naji wani mutum yana min magana, ban iya amsawa ba, sai nuna masa motar nake da hannu na. Barin gurin yayi da sauri, chan ya dawo tare da wata mata.

“Taimaka Hajiya mu sata a motar chan bga kamar.” Ina ji suka kamani, suka saka ni a motar, daidai lokacin me motar ya dawo.

“Kaine me motar nan?”

“Eh nina, tafiya zakuyi?”

“Eh, amma ga passenger ka nan babu lafiya ai, ka taimaka a mika ta asibiti kusa.”

Lekowa yayi cikin motar, ganin yadda nake murkususu yasa shi firgicewa

“Kuyi hakuri gaskiya ba zan iya ba, sai dai idan kunyi niyyar taimaka mata ne toh.”

Cikin bacin rai namijin yace

“Ashe baka da tausayi, baka ga halin data ke ciki bane?”

Da sauri ta dakatar dashi

“Anas karka dau zafi, ina ganin haihuwa ce, ya kamata muyi sauri taimaka sai a biya ka malam.” Tace tana kokarin shiga motar.

“Muje toh tunda biya zakuyi.”

Kwafa Anas yayi a bude motar a fusace ya shiga.

Ignore any error

Rayuwar Aminatu. ????????????

Nagode sosai da addu’oin ku gareni, kunsan matsalar ido sai a hankali, yau tun safe nake typing ɗin nan ina yi ina ajiye a hankali saboda idon. Please bear with me Dan Allah ????

Ranoa: ©Hafsat Rano

                    (16)

★★★★★

Tsaki kawai yake har suka isa asibitin, zuwa lokacin na bana gane komai, tsananin azabar da nake ji tafi gaban a bayyana ta. Tun kafin motar ta gama tsayawa yayi saurin balle murfin motar ya fito yana kwala kira nurses din, da sauri daya ta ƙaraso wajen motar, suka taimaka aka fito dani, kujerar da ake dora mara lafiya aka saka ni akai, aka nufi labor room dani. Fitowa nurse din tayi ta bashi list ɗin abinda ake bukata, da sauri yaje ya siyo a cikin asibitin ya kawo.
     Tsawon lokaci aka dauka ina fama, nasha matukar wuya kafin na haihu, ina haihuwa na suma cikin tsananin wahala. A wannan lokacin suka gyara min jikina ba tare da nasan me ya faru ba.
   Sama sama naji suna kiran sunana, a hankali na fara dawowa, ido na ya sauka akan jaririyar dake kwance bisa kirjina, babu ko kaya a jikin ta, kura mata ido nayi, kuka take sosai da dukkan karfin ta.

“Ga tana tabarakallah, lafiyayya kuwa.”

Naji nurse din na fad’a wa abokiyar aikin ta. Rasa a wannan  matsuguni zan ajiye wannan ranar, ranar da nake gudun zuwan ta, duk kuwa da na hakura na barwa Allah ikon sa, sai gashi tazo min a bai bai, cikin yanayin da ni kaina ba zan iya tantance shi ba, bani da kowa yanzu kenan? Sai wannan jaririyar da bata san komai ba, yanzu ne ma zata fara sanin abinda ke kunshe cikin duniyar nan. Hawayen da bazan iya banbance na farin ciki ne ko na bakin ciki ba suka shiga bin fuskata, ina ji suka cire ta daga jikina, suka shiga gyara ta. Dakin hutu aka maida mu, suka shigo a tare, kallon su nake har suka ƙaraso inda nake, Hajiya ta dauki yarinyar cikin farin ciki, ta shiga jera min sannu.

“Masha Allah, Allah ya raya ta.”

“Matso ciki mana ka ga jaririyar.” Tace tana kallon sa, yana tsaye jikin kofar yana kallon ciki, a hankali ya tako, ya ƙaraso gaban ta ya leka cikin shawul ɗin da aka rufe ta, murmushi naga yayi, a hankali ya furta

“Tabarakallah Hajiya, kinga baby me kyau kamar a bani.”

Dariya ta saka

“Kai fa Anas na manta son yara ne dakai.”

“Wallahi Hajiya. Ina son yara.”

“Allah ya baka masu albarka.”

Da sauri ya amsa

“Amin Hajiya ta.”

“Ja’iri.” Tace tana dariya. Kallo na tayi

“Baiwar Allah ya kamata ki kira yan uwanki, kinga mu akan hanya muke, idan yaso ko zuwa gobe ne sai mu wuce, nasan ma dai goben zasu sallame ki tun da kalou kike ai.”

Ido na ne ya cicciko jin abinda tace, wa zan kira? Bayan bani da kowa a yanzu, wayar ma ko dauko ta banyi ba, ganin yadda duk suka kafa min ido yasa na wayance nace

“Ba anan suke ba, a Kano suke.”

“Kano? Toh ai muna yan chan ɗin ne, idan kin yarda damu sai mu tafi tare gobe da safen, idan yaso sai dai su ganki da babyn ki.”

“Allah ya kaimu goben.” Nace ina kokarin boye damuwa ta. Ido na ne ya sauka akan jakar nan, wani yawu me kauri na hadiye ina tunanin abin yi. Babu inda ta bar ya Farouk, komai nasa ne, hatta yatsun kafarta dana hannun ta nasa ne, hawaye na share a hankali ba tare da na bari sun ganni ba.
Fita Anas yayi ya nufi masallaci, ya bar mu a dakin muka karasa kwana, da safe wajen tara aka sallame mu, mota yaje har tasha ya samo mana, aka zuba kayana muka dauki hanyar Kano a karo na farko a rayuwa ta.

***Isar Inno gida tana kokarin shiga yayi daidai da tsayawar motar, Harira ce ta fito kafin daga bisani matar da suke tare ta fito ita ma. Juyowa tayi tana kallon su, fuskar ta a yanayi me wuyar fassara wa. Karasowa sukayi suka tsaya mata a gaba, Harira tayi dariya sannan tace

“Yau dai ga uwar yarinya nan, sai ki bata ita ta tafi da ita, ki gode wa Allah ma da bata ce zatayi karar ki ba wallahi, dan haka salun alum ba sai kowa yaji ba, shiga ki fito da ita.”

Kallon banza tayi masu a tare kafin tace

“Ashe ma ni mahaukaciya ce kamar ke, kina tunanin bayan kinzo kin same ni da maganar banzar ki zan sake amince miki har na sake wani gangancin? Kije duk inda zaki ki tona min asiri, na riga na shirya wannan ranar tun kafin zuwan ta.”

“Kina nufin me kenan?”

“Abinda kike tunani.”

“Baki yarda da abinda nace ba kenan?”

“Ai yadda dake tun ranar da na gano cuta ta kikayi, a ranar na cire ki daga sahun mutane masu hankali, kuma a ranar na daina yarda da duk wani mutum a doran kasar nan.”

“Ina wai yarinyar take?” Matar ta tambayi Harira tana yatsine.

“Kina ji ai ko? Ki shiga ki fito da ita, kinga shiyasa ma muka zo da daddare muyi komai cikin sirri, in Kuma so kike kowa yaji ne toh?”

“Idan kinga dama, ki dauki abin magana ki zagaye duk garin nan ki sanar musu, a nan ne zan gane cewa baki da mutunci.”

Daga haka tayi shigewar ta gida, tsaye Harira tayi tana kallon matar, cikin bacin rai ta juya ta nufi mota tana mita

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button