DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Tuni na watsar da aiken Inno, na shiga ihu da dukkannin murya ta ko Allah zai sa a jiyo ni, dariya ya shiga yi ba kakkautawa.

“Yarinya da kin hakura babu shegen da zaiji ki, uban me ya fito dake a wannan lokacin shegiya.”

“Aike na akayi wallahi.” Nace ina sharbe hawaye da majina.

“Daidai kenan, idan na ci ubanki zaki gane shayi ruwa ne.”

Ya fada yana kokarin matsowa kusa dani.

Sosai na kara karfin murya ta, cikin tsananin tashin hankali, magiya nake masa ina rokon sa, sai dai hakan ba sa ya fasa aiwatar da abinda ya kudurta a ransa. Tun daga nan bansan me ya kuma faruwa ba????????



Tafiya yayi sosai yana mai jin dadin yanayin garin, kafin zuwa lokacin da iskar ta taso, sauri ya kara don ganin ya isa gida, be yi tunanin ruwan zai zo da iska haka ba. Saukar ruwan ne ya rage karfin iskar sosai, hakan ya bashi damar cigaba da tafiyar sa cikin kwanciyar hankalin ruwan na dan taba fuskar sa kad’an-kad’an. Kamar daga sama yaji ihu, ihun ma na mace me karancin shekaru, sai dai karar saukar ruwan yayi tasiri kwarai wajen kasa tantance daga ina ihun yake, hankali ya tashi ya hau neman ta in da muryar ke fitowa, kamar mahaukaci haka ya shiga kai kawo a cikin ruwan, hankalin sa ne ya kai wajen, da wani irin mugun guda ya nufi dan karamin shagon daya gama tabbatarwa daga nan ɗin ne yake jin kukan, beyi wata wata ba yana zuwa ya daki kofar da dukkan karfin sa. Abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali, da gudu yayi kansa ya shiga dukan shi, duka me cike da tsantsar bacin rai. Yanayin rashin karfi da a tattare da Garbatin ya hana shi katabus, sai daya yi masa duka sosai sannan ne hankalin sa ya dawo kanta, tana kwance kamar mara rai, abinda ya dade yana jin labarin yana faruwa ga yara masu kananan shekaru ne ya faru da yarinyar nan, yarinyar da dududu ba zata wuce sa’ar Amal ɗin su ba, da sauri yayi kanta ya dago ta, tuni ta sume saboda tsabar firgicin data shiga, wani irin kuka ne ya taso masa, wannan wane irin rashin imani ne?. Da dukkan karfin sa ya daga ta ya sata jikin sa, be bi ta kan Garbati ba da yake kokarin tare shi, har ya kai kofa maganar shi ta dakatar dashi

“Ni kayi wa wannan dukan? Akan wannan yar iskar yarinyar?”

A halin da yake ciki ba zai iya magana ba, saboda haka ya juya da sauri dan ganin ya ceto rayuwar yarinyar. Yana juyo hargowar Garbatin me cike da gargadin abinda zai aikata masa.

Gida ya wuce kai tsaye yana jin kamar zuciyar sa zata bar jikin sa. Har lokacin dukkan su suna falo ya shigo da sauri dauke da ita Baba maigadi na bin bayan sa, a tare duk suka mike suna kallon shi cike da mamaki.

“Yah Farouk..!

Amal ta fada tana zaro

“Bude min daki na.”

Da gudu ta yi gaba suka take masa baya, dakin sa ya kaita, ya kwantar da ita saman gadon sa, sai a lokacin ya ga fuskar ta, kallon su yayi duk sunyi cirko cirko kamar sun ga abin tsoro.

“Kira Dada Ja’afar.”

“Wacece ita Yah Farouk?” Ya tambaya ba tare da ya motsa ba.

Kallon sa yayi rai a bace daa karfi yace

“Will you go and call her or…”

Da sauri ya juya ya bar dakin, dafe kansa yayi ya sake dagowa yana hararar kowa.

“Duk ku fice min anan, Amal ki tsaya.”

Yar rige rigen fita suka hau yi, kowa zuciyar sa cike da tambayar abinda yake faruwa.

Gefen sa amal ta zauna tana kura mata ido

“Yah bata da lafiya?” Ta fada cikin tausaya wa.

Daga mata kai yayi zaiyi magana Dada ta budo kofar cikin tashin hankali.

“Babana,me ya faru?” Ta fada tana shigowa dakin, ganin da tayi mata yasa tayi saurin ƙaraso wa wajen

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, me zan gani haka?”

Hannun sa ya saka cikin na Dadan yana kokarin saita yanayin bugun zuciyar sa.

“Bani ruwa da sauri ke Amina.”

Da sauri amal ta tashi ta dauko ruwan, karba ta shafa mata a fuska, sai data yi wajen sau uku sannan ta bude ido tare da sakin wani irin ihu wanda ya karade kusan kowanne lungu da sako na gidan.

Bude ido na nayi wanda yayi min matukar nauyi ina kallon kowa na dakin, a lokaci daya zuciya ta ta shiga tariyo min abinda ya faru, kuka sosai na saka ina jin tsananin zafi kamar an watsa min barkono, riko ni dattijiwar tsohuwar dake kusa dani tayi tana kokarin sani a jikin ta.

“Kwantar da hankalin ki, yi shiru, babu abinda zai faru kinji? Yi shiru karki karawa kanki ciwo.”

Abinda kawai naji tana ta maimaitawa kenan yana shiga kunne na cikin wani irin yanayi dana kasa tantancewa.

“Dada asibiti zamu kaita, She’s bleeding so Badly.”

Muryar sa ta daki kunne na, kallon sa Dada tayi kafin tayi magana cikin harshen turanci.

“Who is she?”

“It’s a long story, babu time zan sanar dake komai, for now let’s help her please.”

Ya karashe a marairaice.

“Owk, Amma Ina son sanin amsar, kasan dai mahaifinku, kasan kuma labari zai kai masa zuwa gobe, i just hope ba kaine ba.”

Ta zura masa ido tana son ganin gaskiyar sa. Be yi magana ba, sai ma mikewa da yayi ya fice daga dakin, jim kadan ya dawo yana kallon Amal data makale a gefe tana mun kallon tausayi.

“Zaki rakamu ko?”

Da sauri ta daga kanta.

“Dada ga driver ya dauko motar, muje ko?”

” Shikenan.”

A hankali ta daga ni zata mikar dani, wata irin kara na saki me cike da azaba, da sauri ya waiwayo ya fasa kokarin fita daga dakin, da baya da baya ya dawo ya daga ni chak ya fita dani suna take masa baya.


Tun Inno na zuba idon dawowa ta har hankalin ta ya fara tashi, ganin tasowar hadarin yasa ta sake shiga tashin hankali sosai, turawa tayi aka kira mata Nura a zaure ya bi bayana, lokacin iskar nan ta taso sosai. Safa da marwa Inno kawai take yi, duk wajen kowa yayi tsit ana jiran dawowar Nura, tsawon mintuna talatin ya dawo hankalin sa a tashe, babu ni babu dalili na, hakan kuma yayi daidai ta tsugewar ruwan, iya kar tashin hankali Inno ta shiga, bata fatan abinda zuciyar ta ke raya mata ya zama ya faru,bata da wata hujjar kare kanta a duk lokacin data shirya karbar muradin zuciyar ta, ko ma ba haka ba, baya cikin yarjejeniyar da sukayi tsakanin su, ko ba komai zata ci darajar nata dan.

Tuni su karime da sauran yaran suka fara kuka, babu me rarrashin wani, ana haka ruwan ya fara tsayawa, gaba daya suka fito dan zuwa nema na, lungu da sako babu alamun za’a same ni, tashin hankalin da ba’a sa maka rana kenan, gida suka dawo kowa yayi jigum jigum ana tunanin ta in da zan ɓullo, duk da zuwa lokacin kowa ya gama saddak’arwa wani mugun abin ya same ni.

Duk suna zaune sunyi cirko cirko, makotan da suka shigo duk sun tafi, yara sunyi bacci sai yan kadan, aka yi sallama a kofar gidan, da sauri su Nura suka fito tare da su Baba.

“Garbati?” Nura ya fada yana kallon su.

“Mune nan.” Ilu ya amsa yana jingina a jikin garu

“Lafiya dai ko?” Baba yayi tambayar ganin basu ce komai ba.

Ilu ne ya kalli Garbati kafin ya shiga magana

“Dama akan Aminatu ne.”

Da sauri a zabure suka hada baki.

“Kun ganta ne?”

Ilu ne ya dora

“Bamu ganta ba, sai dai mun san inda take, dan munyi iya kar kokarin mu wajen ganin mun taymaka mata, garin haka ne ma Garbati yasha wannan dukan da zaku ga jikin sa haka.” Ya fada yana haske Garbatin

“Tana ina?”

“Ina bakin gidan Bature? Daya daga cikin su ne muka kama shi, dan a lokacin da muka je ko numfashin kirki batayi, garin kokarin mu ne ma yasa masu gadin su sukayi wa Garbati mugun dukan nan, sannan ya dauke ta ya tafi da ita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button