DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kinsan bata min lokaci zakiyi kika kawo ni, bayan kin tabbatar min an gama magana.”
“Ja muje kawai aikin banza.”
Da sauri Harira tayi wajen motar, kafin ta k’arasa sun ja sun bad’e ta da kura, bin su tayi da gudu tana kwala kiran ta amma basu tsaya ba. Zage zage ta shiga yi cikin bacin rai.
★★★
A gurguje ya hada komai, ya rurrufe ko ina ya fito, baki daya tsawon zaman da yayi a wajen cikin rashin kwanciyar hankali yayi shi, kafatanin tunanin shi na wajen ta, duk da dai yasan ya bar ma mutane biyu amanar komai a hannun su wanda yake tunanin ba zasu taba yi masa ba daidai ba, amma hankalin nasa sam yaki kwanciya, har zuwa yau da suka samu yancin barin wajen, sosai yayi dana sanin shiga aikin soja, aikin da zai raba ka da kowa naka idan ba girma kayi a cikin sa ba, tsawon lokaci ba tare da anji daga gareka ba, babu service balle ka kira wani, idan ma akwai baka da kwanciyar hankalin kiran.
Babbar mota ce sumfurin Hilux suka cika kayan su a ciki, suka dauki hanya. Ife ife ne kawai ke tashi a motar cikin yaren su na sojoji, kowa da abinda ya dame shi wasu ma waka suke bi cikin nishadi da murnar zuwa gida. Kallon su kawai yake ba tare da ya sa musu baki ba, daya gaji da hayaniyar tasu sai ya kwanta kawai ya lumshe idon sa yana jin farin ciki da daukin zuwan nasa gida.
Sanda suka iso Abuja, dare ya soma yi sosai, bashi ya samu isa gida ba sai bayan sha biyu na daren.
Rataye yake da jakar goyo irin babbar nan, sai yar karamar trolly daya riƙe yana jan ta a kasalance, ya ɗan buga gate din, sojan dake tsaye kofar ne ya leko, da sauri ya bude cike da mamaki sa, gaisawa sukayi ya wuce ciki kai tsaye, ganin dare yayi ya sa ya wuce bangaren su, ya tura kofar bakin sa dauke da sallama. Ja’afar na zaune a kan sofa Yana danne dannen waya yaji an turo , dagowa yayi da nufin ganin waye, cikin tsananin tashin hankali wanda yasa saura kadan ya saki wayar hannun sa ya furta
“Ya Farouk!”
Murmushi yayi,
“Kana mamaki ne? Ko ka dauka na mutu ne?”
“Wai yanzu kazo? Yanzu yanzu zuwan kenan?”
“Ga zahiri ka gani, malam karbi kayan ka kaimin daki mana ka tsare ni da tambaya.”
“Auw.” Yayi saurin karbar kayan yayi hanyar dakin dasu, shi kuma ya fada saman kujerar yana sakin ajiyar zuciya.
“Home sweet home.” Ya furzar da iska me dadi kafin ya tashi ya nufi fridge, ruwa ya dauka ya koma ya zauna yasha, sannan ya ɗan mike kafar sa. Jin shiru shiru Ja’afar be fito ba yasa shi kwala masa kira, a zabure ya fito kamar mara gaskiya.
“Kai kuma daga ajiye jaka sai ka zauna, bayan kasan dole zan tambaye ka.”
“Bacci ne ya soma dauka ta, afwan, ya hanya ya komai?”
“Normal.”
Dan zamowa yayi daga kujerar kadan yana fuskantar shi
“Allah yasa dai abinda na saku kaida Amal kunyi min shi babu shirme ciki, nasan ma dai babu abinda zai sa kuyi min hauka, dan zan iya komai akai wallahi.”
“Na’am..?” Ya zaro ido
“Yadda kaji, yanzu dai bari na kwanta, da safe ka shirya da wuri mu wuce, kasan i can’t wait any longer.”
Tashi yayi wuce daki, a hankali Ja’afar ya zame a wajen yana jin wani mugun tashin hankali. Da sauri ya jawo wayar sa ya hau kiran Amal, har ta katse bata daga ba, haka yayi ta jera mata kiran duk kuwa da yasan ba dole ne ta daga ba, duba da dare yayi.
A falon ya kwana, ba tare da ya runtsa ba, duk kuwa da yasan dole zai dawo dama, amma beyi tunanin dawowar shi a wannan lokacin ba. Lallai akwai matsala babba, matsalar da zata iya haifar da komai.
Manage pls???? Yau ruwa yayi mun duka jama’a ???????????? Saura naji wata tayi min dariya????????
8a: Daurin Goro*
17
© Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
17
★★★★★★
Cikin yanayin da ke bayyana tsantsar farin cikin sa ya tashi, mika yayi hade da salati, kafin ya fada toilet a gaugauce. Be dau lokaci ba ya fito, ya hau shiryawa cikin kaya mafi tsada da kyau, yana yi yana kallon kansa a mirror, murmushi ya saki da ya tuna inda zashi, shigar manyan kaya ce a jikin sa, wadda suka fito da zahirin kyawunsa na bakattsinen asali. Lekowa yayi falon da nufin kira Ja’afar, wayam babu kowa sai kalacin dake zube a saman centre carpet din dake ajiye a tsakiyar falon, tsaki yaja ya fito, ya nufi main part din gidan yana karewa ko ina kallo. Kicibis sukayi da Amal dake shirin fita a yanayi me wahalar fada, da sauri taja baya, cikin yanayin rashin gaskiya tace
“Yahh…”
Murmushi ya sakar mata kafin yace
“Suprice!”
“Saukar yaushe?”
“Jiya kina ta bacci, nasan lokacin kin kai Australia ma dan nasan ki da shegen bacci.”
“Waye nake gani kamar Farouk?”
Ta katse su tana fitowa daga kitchen rik’e da babban tea flask me dauke da kunun tsamiya.
“Nine wallahi Mama, ina kwana?”
“Ah laillai maraba da manyan sojoji, sannu da zuwa ya hanyar?”
“Alhamdulillah walalhi ,sai kewar gida, sam aikin nan ba dadi wallahi.”
“Toh ya za’a yi, ka gaisa da Daddyn naku dai ko? dan yanzu yake shirin fita.”
“Aiko yanzu nake shirin shiga bangaren nasa, bari nayi sauri dan nima Kano zan tafi.”
“Za’a je a gano Hajiya kenan, toh karbi flask din nan ka tafi masa dashi, bari na dauko sauran kayan.”
“Ko da yake ma…” Ta kalli Amal dake tsaye kamar munafuka tana sauraron su tace
“Daughter zo ki dau sauran kayan ki kai masa na karasa wani aiki anan.”
***Tare suka jera yana tambayar ta bayan tafiyar sa, amsawa take har suka karasa part din Daddy, wayar ta dake cigaba da k’ara ta sake katse wa a karo na ba adadi, dariya Farouk yayi
“Sirikin nawa ake wulakantawa ne?”
Sai ta kalle shi da sauri, girgiza kai tayi suka shiga falon a tare, Daddy na zaune ya shirya cikin shigar sa kamar ko yaushe, da tsananin mamaki yake kallon Farouk din har suka ƙaraso ciki, ajiye kayan sukayi akan food mat din da ake jera masa kayan abincin kafin kowannen su ya zame ya zauna, Amal ce ta fara gaishe shi, kana ta mike kamar wadda ake mintsina ta fice da sauri, tana ji Ya Farouk yana bata sakon ta kira masa Ja’afar tayi gaba kawai ba tare da ta amsa ba.
“Barka da Safiya.”
Ya furta cike da karsashi ba tare da ya gama karantar yanayin Daddyn ba. Be amsa ba, sai ma wurgo masa da tambaya yayi cikin dakewa yace
“Sai yanzu kake nuna fuskar ka anan ko?”
Kai tsaye yace
“Ayi hakuri Daddy, wallahi tafiya ce ta taso a ranar, na sanar da Ja’afar amma ya fada maka, bayan na kirkira wayar ka ban samu ba, tun da muka shiga jejin nan babu service wallahi, sai jiya da Allah yayi muka fito lafiya.”
“Toh… Tafiyar ce ta saka ka yanke d’anyen hukuncin daka yanke kenan? Bayan haka ka nuna min kaine ka haife ni, ka watsa min k’asa a idon duniya ko? Ka kyauta..”
Cikin rashin fahimta yace
“Allah ya baka hakuri Daddy, amma sam ban gane abinda ake magana akai ba, ka gafarce ni dan Allah.”
“Rainin wayon naka har ya kai haka? Lallai wuyan ka ya isa yanka.”
Kasa yayi da kansa, yana ji Daddyn ya mike, ya shige bedroom d’insa, kasak’e yayi yana tunanin inda maganganun suka saka gaba, sai dai ya kasa gano ko daya. Fitowar Daddyn yasa ya dago, a fuskar sa ya jefa masa takardun guda biyu, kana yace