DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Aminatu, karbe ta ki sake gwada mata ko Allah zai sa a samu ruwan, kece ma dai kinki cin abinci, dole idan kika je gidan su tilasta miki sa wani abu a cikin ki, ruwan nono sai da abinci zaizo.”
Hannu na mika na karbeta, na dora ta saman cinya ta ba tare da sanin takamaimai ta inda zan fara mata.
“Dauke ta ki sata jikin ki mana, shiririta.”
Kamar zanyi kuka na daga hijabi na na sata ciki, juyowa yayi bayan muka hada ido dashi, da sauri na janye ido na ina kallon kasan kujerar,
“Hajiya ya za’a yi ne? Itan za’a fara kaiwa ko yaya?”
Gabana ne ya fadi, nayi kasak’e ina jiran amsar ta, waigo ni tayi tace
“Aminatu,wacce unguwar kuke? Kunga an kusa shiga Kanon mu fara rakaki gida sai mu wuce.”
Rau-rau nayi da ido na da ya cicciko lokaci daya, na daure na cije nace
“Bansan kowa ba sai mutum daya, hasalima wannan ne karo na na farko dana zo Kanon, sai dai bansan inda zan same ta ba, wayar da xan kira ta na manta ta a gida.”
Bude baki sukayi a tare suka ce
“Kina nufin baki san inda zaki ba?”
Daga kai na nayi ina sharar kwalla, ransa naga ya ɓaci, ya kalle me motar
“Idan kaje kwanar dawanau ka sauke mu, sai ta fada maka ita inda zaka kaita, nawa zamu biya gaba daya?”
“Anas…”
“Kiyi hakuri Hajiya, bana so daga taimako mu shiga matsala, kuma kinsan ni a rayuwata na tsani karya, me yasa zata boye mana gaskiyar ta? Sai data ga munzo zata ce bata san inda zata ba?”
“Shikenan.”
Tace tana kallo na, kasa na sake yi da kaina ina kuka, zuwa lokacin jaririyar tayi baccin wahala, dan babu nonon sam yaki zuwa.
Sanda muka iso inda yace, inaji motar ta tsaya, ya fita da sauri aka bude masa booth, ya cire kayan su, bude mata kofar bangaren ta yayi yana sake daure fuskar sa tamau.
“Fito Hajiya.”
Kallon da tayi masa ya dauke kai kamar be gani ba, ya maida kansa bangaren driver yana tambayar sa lissafin kudin tunda mu kadai ya dauko tun daga chan din.
“Kudin dukka kujerar zaku bayar, ita kuma idan na isa tasha sai ta sauka ta nemi wani abin hawar, iyakata tashar ne kawai.”
Lissafa wa yayi ya ciro kudin ya bashi yana yin gaba, a hankali na furta
“Nagode Allah ya saka da Alkhairi.”
Sarai yaji, dan har sai da yayi dan alamun kamar zai tsaya, kafin ya kara daga kafar sa Hajiyar na take masa baya. Kuka na saka sosai ina jin bani da sauran gata a duniyar nan. Rayuwata ta kare, ina ji a raina gab nake da mutuwa, sai dai idan na kalli yar karamar halittar dake hannu na, wadda yanzu dukkan rayuwar ta, na rataye a wuya na, sai naji komai ya sake min, zan rayu ko don sabo da ita, na kula da ita.
Ban yi aune ne na ganmu a tashar, sake rungume ta nayi sosai a jikina, motar na tsayawa na balle murfin na fito,ina sake karewa ko ina kallo, a karo na farko na zo Kano, ba tare da sanin inda zan dosa ba. Jakar nan ya fito min da ita, hade da sauran kayana, dauka nayi na matsa daga wajen ina neman inda zan fake don zuwa lokacin har ta kuma tashi tasa kuka, baccin nata baya nisa saboda yunwar dake damun ta. Chan na hango kasan wata bishiya, nayi saurin isa wajen, na rabe ina jijjigata. Nayi nisa a son ganin tayi shiru, kamar daga sama naji muryar sa a kaina
“Kin tabbata ba wani mugun abun kikayi kika gudo ba?”
Dagowa nayi idonmu suka sarke waje guda, da sauri na daga kaina alamun Eh
“Idan kinyi alkawarin sanar dani gaskiya, zan taimaka miki.”
“Nayi Alk’awari.”
Hannu ya mika ya dauki kayan nawa, na tashi da sauri nabi bayan shi.Daurin Goro*
18
© Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????
18
Adaidaita sahu naga mun dosa, muna zuwa ya mika kayan ciki yace wa Hajiya
“Ku tafi bari na hau wani, zan sameku a gida.”
“Shiga.” Yace yana nuna min ciki, shiga nayi Hajiya ta miko hannu ta karbi yar jaririyar.
“Kiyi hakuri kinji?” Tace min tana kallo na. Murmushi kawai nayi muka dauki hanya ba tare da sanin takamaimai inda muka dosa ba.
Unguwa ce tsaf tsaf babu cinkoso balle hayaniya, a kofar wani dan madaidacin gida naga mun tsaya, ni na fara sauka sannan ta fito,
“Dauko kayan Aminatu.”
Kayan na kwaso ta bude yar karamar kofar jikin gate din muka doshi cikin gidan, da wata dattijuwar mata muka fara haduwa tana zaune gaban fanfo kayan wanke-wanke ne a gabanta tana yi, da murnar ta ta taso ta tare mu,
“Sannu da dawowa Hajiya.”
“Yawwa Altine, ana ta aikin ne?”
“Wallahi, jiya mukayi ta zuba ido shiru har dare sannan Ramlah ta hakura ta kwanta.”
“Wallahi kam.”
“Sannu.” Tace tana kallo na, gaishe ta nayi ta amsa sannan muka dunguma zuwa cikin falon, ko ina a share tsaf na samu gefe na rakube ina jin su suna cigaba da hirar tasu inda na fuskanci ita Altinen me aikin Hajiya ce, mika mata kayana tayi tace ta shigar min dasu dakin Ramlah.
“Jeki ki huta Aminatu, nasan kin gaji.”
Tashi nayi nabi bayan ta, a gefe ta ajiye kayan, dakin a hargitse duk an barbaza kaya, tattarewa ta hau yi tana mitar halin wadda aka kira da Ramlah ɗin, tana gamawa ta fita, da sauri na haye gadon na kwanta dan ji nake kamar zan fadi, anya ma ina da isheshen jini a jikina ma kuwa? Na tambaya kaina ina karewa ko ina na jikina kallo, na dashe nayi fari tas ga wani matsanancin ciwon kai da jiri da nake ji. Shiru nayi ina ayyana yadda zamu kwashe da Anas, dan da alama mutum ne mai zafi, zan yi kokarin sanar dasu gaskiyar labari na, dan na samu na makale kafin zuwa gaba naga yadda Allah zaiyi dani.
Kukan da naji yana doso dakin yasa na tashi na zauna sosai, Hajiya ce ta shigo rik’e da yarinyar dake faman tsala kuka, zuciyata ce ta tsinke da tsananin tausayin ta, bata da damuwar komai sai ta cikin ta, yunwar dake damun ta itace ta hanata sakat, waya take da alama da Anas ɗin take yi, kafin ta ajiye yana mika min ita.
“Karbe ta ki sake gwada mata, kafin a kawo mata madarar da tausayi sosai wallahi.”
“Toh.”
Nace na karbeta, fita tayi ta jawo mana kofar, yadda zan fara bata ne ma sam ban iya ba, kici-kici nake tayi na kasa, gashi sai kara karfin kukan nata take, duk na rikice na rude, a haka ta sake shigowa ta tarar dani, hannun ta dauke da bakar leda, da sauri ta ƙaraso tana ajiye kayan kafin ta karɓe ta,
“Baki iya bata ba Aminatu? Na shige su, ai na zata kin iya, shiririta kenan.”
Sauke kaina kasa nayi, ta cigaba da jijjiga ta, shigowar Altine da tea flask yasa ta ajiye ta ta shiga hada mata madarar a sabuwar feeding bottle din da aka siyo tare da Madarar, ina zaune ina kallo har ta gama haɗawa sannan ta shiga bata, da sauri da sauri take sha gwanin tausayi, kwalla na share a ido na ta gefe ina godiya da Allah daya kawo min mutanen nan a lokacin da nake tsananin bukatar wani a kusa dani.
Ana gama bata ta koma bacci, kwantar da ita tayi, tana dariyar yadda take fitar da numfashi a hankali.
Kura mata ido nayi bayan fitar su daga dakin, murmushi na saki a hankali na kai hannu na saman kanta ina jin sabuwar soyayyar ta na bin dukkanin jikina.
Ruwan wanka Altine ta haɗa min, ta kawo dakin, ganyen darbejiya naga ana shigowa dashi dakin, kuka yazo min, kukan farin ciki, bansan da wanne bakin zan gode wa wannan matar ba, da kanta ta shigo ta saka ni a gaba tayi min wankan, wankan jegon da iyaye keyi ma kowacce yarsu, a lokacin da nake tunanin na rasa wannan gatan, a lokacin Allah ya aiko min da ita rayuwa ta. Wankan da nayi ba karamin jin dadin jikina nayi ba, ina gama shiryawa aka aikon da abinci lafiyayye irin wanda ya kamata mutumin da yake irin yanayin da nake ciki yaci, sosai naci abincin dan rabona daci tun kafin komai ya sake canja min, dadin dadawar ta tabbatar min da idan ban ci abincin ba, jaririyar tawa ba zata samu ruwan nono ba, hakan ya kara min kaimi wajen ganin naci abincin sosai.
Ina gamawa nabi lafiyar katifar, sam bana son nayi tunanin maganganun Inno, dan ba karamin hargitsa min lissafi suke ba, na kasa gasgata abinda ta sanar min, duk da na riga nasan ba zata taba min karya ba, amma kuma zuciya ta sam ta kasa aminta da maganganun.
Dawowar shi naji yo muryar sa a falon, gabana ne ya fadi da tunanin yadda zamu kwashe dashi, ina nan kwance aka turo kofar, Hajiya ce a gaba sai shi a bayanta, yar karamar kujerar dake dakin yayi wa kansa mazauni, inda Hajiyar ta zauna a gefen gadon tana kallon jaririyar