DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kinga ashe baiwar Allah yunwa ce, gashi yanzu sai baccin ta take.”

“Uhum.” Nace ina kokarin daidaita zama na saboda yadda naji duk na kasa sakewa.

“Ya jikin?” Ya jeho min tambayar,

“Da sauki.”

“Good.”

“Kamar yadda kika ganmu, wannan mahaifiya ta ce, sai kanwata Ramlah, sai Altine dake taimakawa Hajiya da yan aike aiken gida, wadda ta zama kamar ma yar uwa ta jini. Babu bukatar dogon bayani mu, mu kadai ta haifa, mahaifin mu ya rasu, sai dangin sa dake Katsina inda muka hadu dake munje wata gaisuwar rashin da akayi, dangin Hajiya duk yan Kano ne, yan karamar hukumar Kibiya, kuma yawancin su suna chan. Ina aiki da federal mortgage bank, in da kanwata take matakin farko a jami’ar northwest.”

“Haduwar mu wani iko ne na Ubangiji, duk da haka, ina so ki sanar damu gaskiyar abinda ya dangance ki daya dace muji, ki sani bana bukatar komai sai gaskiya.”

Share hawayen dake faman bin fuskata nayi tun lokacin daya fara magana, a nutse na shiga sanar dasu rayuwa ta. Duk da ba komai na sanar musu ba, amma nayi kokarin sanar dasu abinda ya dace su sani kamar yadda ya nema.
Ina kallon yadda yake girgiza kansa, Hajiya kuwa kuka ta saka cike da tausayi na, ina kaiwa karshe ta taso da sauri ta rungume ni.

“Baa kyauta miki ba Aminatu, ba’a kyauta miki ba.”

Shine kawai abinda take ta nanatawa, mik’ewa yayi tsam ya iso gaban gadon, idanun sa cikin nawa, yasa hannu ya dauke ta, murmushi yayi min tare da girgiza min kai alamun nayi shiru.

“Wanne suna za’a sa mata?”

Ya fada yana tsura min ido, bance komai ba, na maida kaina kasa ina share hawayen fuskata hade da yiwa Allah godiya, sake maimaita wa yayi a karo na biyu, a hankali na furta

“Duk sunan da ka sa mata yayi.”

Murmushi naga ya sake yi, sannan ya kara bakin sa a kunnen ta yayi mata huduba, dagowa yayi yana sauke ta a saman gadon kafin ya kalle Hajiya

“Na sa mata Fatima.”


Har suka isa kauyen na Shagari babu wata magana data hada su, Allah Allah Farouk yake su isa gidan. Suna isa yayi saurin fitowa ba tare da ya jira Ja’afar ya gama daidaita tsayuwar motar ba, cikin zauren gidan ya shiga yayi sallama da d’an karfi dan babu yaron da zai aika.
Inno na zaune taji sallamar sa, gabanta ne ya fadi ta mike da sauri, idan har ba gizo kunnenta yake mata ba, toh tabbas muryar sa ce, idan kuwa haka ne akwai gagarumar matsala. Sake sallamar yayi hakan ya sa ta kara tabbatar da shi din ne, da sauri ta ciri mayafin ta a saman igiya tayo zauren a rikice.
Zagaye yake a cikin zauren ya kasa tsayawa waje daya, da sauri ya kalli hanyar shiga gidan jin takun tafiya, gaba daya tunanin sa ya tafi akan itace, bayyanar Inno a gaban sa yasa ya dan ji faduwar gaba, yanayin fuskar ta ya nuna akwai matsala, a gajarce ya gaishe ta, ta amsa kai tsaye tana gyara tsaiwar ta.

“Dan Aallah ko zan iya ganinta? Duk da nasan ba lallai ta saurare ni ba, amma ina bukatar ganinta dan Allah.”

“Me yasa sai yanzu kake dawowa? Me yasa sai da lokaci ya kure, bayan kayi min alƙawarin zama da ita komai rintse, tabbas dawowar ka a wannan lokaci Farouk bata da amfani.”

“Nasan ni mai laifi ne, amma ina da uzuri, ina fatan idan mukayi magana da ita zata fuskance ni.”

“Ka makara Farouk, Aminatu ta tafi, bansan inda take ba, bansan ina za’a ganta ba, ya zanyi? Na jira ka, tsawon lokaci baka dawo ba.”

A wani irin yanayi ya kalle ta, kansa ya shiga juyawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi, yayi taga taga zai fadi, Ja’afar yayi saurin tare shi, da karfin sa ya mike, ya kwace daga rikon da Ja’afar din yayi masa, kallon tsana da kiyayya yake bin ta dashi kafin ya nuna ta da hannu yace

“Me tayi miki da kika watsa rayuwar ta haka? Wanne irin rashin imani ne wannan? Baki san inda take ba, me hakan ke nufi?”

“Bani da zabi ne, zaman ta anan na nufin fadawarta mugun hannu.”

“Yanzu kika san a hannun da take? Eh?”

“Ban sani ba.”

“Toh wallahi babu wanda zan kyale, bayan sanin alakar dake tsakanin ku, babu abinda zan tsaya jira ko kunya, idan har zaki iya rufe ido, ki koreta a halin da take ciki, wallahi ba zan yi kasa a guiwa ba wajen ganin na bi mata hakkin ta.”

“Ka saurare ni, banyi hakan don na cuce ta ba, bani da kowa da zai iya tsayamin, Harira ta wuce inda kake tunani, ya zanyi da raina? Kuskure daya tak, ya zama silar rugujewar dukkan farin ciki na.”

Sosai ya koma mata kamar bashi ba, maganganu ya shiga fada mata duk wadda tazo bakin sa, cikin tsananin fushi da bacin rai, da sauri ya juya ya fita, ya fada mota ya bar wajen ba tare da yabi takan Ja’afar da ya biyo shi yana kwala masa kira ba, zauren ya dawo ya tsaya kawai yana tunanin inda Farouk din zashi,

“Dama nasan za’a yi haka, amma ya zanyi da rayuwa ta?”

“Yaushe ta tafi?” Ja’afar ya tambaye ta

“Shekaran jiya.”

Girgiza kai kawai yayi, yace Allah ya kyauta.
A kafa ya shiga takawa, ya nufin gidan Bature, a hanya yaci karo da motar yan sanda, sai Farouk dake gaban su, da sauri yasa hannu ya tsaida shi, tsayawa yayi ya bude masa motar ya shiga suka cigaba da tafiya

“Ya Farouk, kana ganin hakan shine daidai? Karka manta wacece a wajen ta fa.”

“Na fika sani, ai na fada mata, idan wani abu ya sameta, wallahi bazan kyale ba, wanchan karon taci darajar Aminatun bata sani ba, ba kuma naso na data mata hankali, amma yanzu sai inda karfi na ya tsaya.”

Duk da ja’afar be gane inda maganganun suka dosa ba, amma sai yayi shiru ba tare da ya sake cewa komai ba, suna isa gidan yan sandan suka fito, babu wani bata lokaci suka shiga suka fito da Inno, cikin kankanin lokaci kofar gidan ya dinke da mutane, yan kallo, Garbati na zaune a majalisar su labarin ya isar musu, da sauri sauri suka ƙaraso wajen, gaban sa ne ya fadi ganin Farouk ne, boya ya hau kokarin yi a bayan mutane be san tun zuwan sa wajen ya ganshi ba, yana kokarin guduwa yaji an chapke shi, turje turje ya fara yi, yana ihu ganin haka yasa kowa ya hau darewa, suka ingiza keyar shi suka sashi a bayan mota, Inno kasa dagowa tayi saboda tsananin kunya, kuka take har Karime ta ƙaraso wajen dauke da goyon Saddiku tana kuka, ganin Farouk yasa tayi wajen sa da sauri tana rokon sa, hakuri kawai ya bata ya basu umarnin su wuce zuwa kauyen da Harira take. Motar ya fada suka bi bayan su yana jin yau yayi abu na farko daya kamata ace yayi shi tun tsawon shekarun da suka wuce.

Hajiya Inno za’a yi kwanan cell????????

Manage ????????????????????????????:      Hansatu R

                19

ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*

07067124863

Ko kuma

09032345899

ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING????????

★★★★

“Sunana Anas?” Hajiya ta tambaya cikin farin ciki, daga mata kai yayi

“Sunan ki nasa mata Hajiya, ina fatan tayi gadon kyawun halin kirki da nagartarki.”

“Wai kin amince Aminatu?” Hajiyan ta juyo tana kallo na, da sauri na daga kaina sama, cikin wani yanayi na furta

“Bani da ja akai, kin chanchanci fiye da haka.”

“Allah yayi muku albarka.” Tace cikin farin ciki mara misaltuwa.

Gefe ya koma rike da Fatima, ya zauna yana jujjuyata a hannun sa, daidai lokacin ta bude idon ta, hade da sakin kuka, da sauri ya mike

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button