DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yah Farouk, dama kana tsaye?”
“Umm. Ina tsaye ina jinki kina waya da siriki na.”
“Ni?” Ta zaro ido tana dafe kirjin ta
“Da fa Ilham muke magana.”
“Ahaap, idan ma dai boye min shi kike shikenan, anyway zo muje ina son magana dake.”
Gaba yayi ta bi bayan shi cikin tarardadin abinda zai ce mata ɗin, part dinsu ya shiga, ya zauna saman kujera cikin sanyin jiki ta zauna gefen sa tana kallon sa.
“Kina da wanda kike so?”
Tayi saurin dagowa,
“Yes… Idan har akwai wanda kuke magana dashi, let me know, ni kuma zan yiwa Daddy maganar.”
Marairaice wa tayi kamar zatayi kuka tace
“Ni dai babu kowa Allah.”
‘Dan jim yayi kafin yace
“Kin tabbata?”
Daga mishi kai tayi tana sake kwabe fuskar ta, girgiza kansa yayi ya furta
“Shikenan ba damuwa, kije kawai.”
“Ya Farouk!” Ta kira sunan sa ba tare da ta tashin ba, maida kallon sa yayi kanta yana jiran yaji me zata ce, wasa ta soma da hannun ta kafin ta daure tace
“Mamaa tace min zaka aure ni, shiyasa bana kula kowa.”
A mamakan ce ya bita da ido har ta bar dakin da sauri, janye hannun rigar sa yayi cikin rashin sanin madafa ya jingina kansa da jikin kujerar yana lumshe idon sa.
Kwana uku a tsakani yana ta tunanin mafita, ya rasa yadda zai ɓullo wa al’amarin, idan har yace ba zai aure ta ba, toh tabbas kamar ya dasa wani babban abu ne tsakanin sa da mahaifinsa, wanda bashi da wani buri sai na ganin ya faranta masan.
Muskutawa yayi yana sake kiran Number a karo na ba adadi,magana d’aya ce babu wani sabon bayani game da neman nata, tsaki yaja yana ajiye wayar, chan ya sake dauka ya danna wa Dadah kira, bata daga ba har ta gama ringing, zamewa yayi a wajen ya mike kafar sa yana fatan komai ya zama masa da sauki.
Yayi nisa cikin tunanin da yake na kokarin ganin ya samu mafita, ganin yana kara bata lokaci yasa shi mik’ewa ya sauya shigar sa zuwa kayan motsa jiki, mota ya fada ya nufi wajen motsa jiki. A chan ya dade ba tare da ya dawo gida ba, sai daya ji ya gaji sosai sannan ya juyo gidan.
Part dinsu ya wuce kai tsaye, Ja’afar ne zaune da sauran yaran gidan suna buga game d’in wot, idanun sa ne suka sauka akan Amal dake zaune cikin su ana yi tare da ita, ransa ne ya ɓaci, ya daka mata tsawar data saka dukkan su firgita, hannu ya nuna mata kofa yana jin kamar ya kikkifa mata mari, gaba daya wannan wani sabon hali ne da be san ta dashi ba, duk da sukan yi hakan a lokacin yarinta, amma yabzu fa? Sam ba zai yarda da wannan shashancin ba, dole ya taka wa Ja’afar birki dan shine babban banza, idan ba haka ba ace duk cikin su basu san abinda ya dace ba,yadda zamanin nan ya sauya, yan uwan da suke uwa daya uba daya ma shaidan na iya tasiri akan su, ballantana ita da take ba muharramar su ba, ya lura kanta na rawa sosai da yadda suke shige wa juna tsakanin su. Dole yayi wa tufkar hanci ba zai yarda su kara masa wani ciwon kan aakan wanda yake fama dashi ba.
A kufule yayi hanyar daki wanda tun kafin ya kai ga yi musu magana duk kowa ya dare ya kama gaban sa.
★★★
Idan nace ina da matsala ta zamantakewa ta da wadannan bayin Allah nayi karya, duk wani abu da zamu bukata nida Iman sai dai mu ganshi.
Sai dai har yanzu zuciya ta ta gaza daukar nauyin abubuwan da ke cunkushe a cikin ta, duk da ina kokarin dauke damuwa ta ko dan yawan fadan Hajiya a gareni, Amma Tabbas ba karamin abu bane a gareni, mutanen da ka sani a matsayin dangin ka, rana daya a tabbatar maka da babu wata alaƙa tsakanin ku, mesa tun da ta kasa daukar haske a kan hakan duba da yadda Inno take mata, sai a yanzu wata maganar da Babarsu Harira ta taɓa fada mata ke dawo mata, Inno bata taɓa shayar da ita ba, a lokacin ta dauki hakan a matsayin wata lalura kila data hana hakan, sai gashi yanzu ta gane babban dalilin ta nayin haka, ba zata ce ta cuce ta ba, amma tabbas bata kyauta mata ba, bata yi mata adalci da d’an data haifa ba.
Bata da wata hanya ta neman mutanen dake da muhimmanci a rayuwar ta, Farouk, Dadah, da mahaifanta. Yaushe zata gansu? Ta riga tayi ma manta alƙawarin ba zata sake komawa garin na Shagari ba har sai sanda ta tabbatar wa kanta shine daidai lokacin daya kamata ta koma din.
Turo kofar akayi aka shigo hade da sallama, dan gyarawa tayi tana kallon sa, a saman kujerar dakin yayi wa kansa masauki cikin kamala yace
“Ya jikin naki?”
“Alhamdulillah.” Na maida nasa
“Allah ya saka da Alkhairi.” Na dora, nasan abinda yazo gani, tsam na mike na dauki Iman na isa gareshi, hannu ya mika da nufin daukar ta hannayen mu suka hadu waje daya, da sauri na janye nawa ina sauke kaina kasa, kallo na yayi na yan dakiku kafin yayi murmushi yana maida hankalin sa wajen ta, hanyar fita nayi daga dakin bakin daya saboda ba zan iya zama ni dashi kadai ba, yau ne ma rana ta farko daya taddani a dakin ni kadai, ban kai ga fitar ba ya dakatar dani da maganar sa
“Dawo magana zamuyi.”
Da baya na dawo na koma inda na tashi na zauna, shiru ne ya biyo baya, ya cigaba da rikon Iman ba tare da yace komai ba, duk sai naji na takura, dagowa nayi da niyyar ganin abinda ya hana shi maganar, idanun sa a kaina suna yawo, da sauri nayi kasa da kan ina ji na a matukar takure.
“Akwai abinda kike bukata ne?”
Kai tsaye nace
“A’ah…” Sai kuma na tuno da maganar kudin nan, tashi nayi na bude inda na ajiye su, na dauko na dire a gaban sa.
“Dama… Dama idan ba damuwa ina so ko zaka ajiye min kudin nan, idan yaso duk abinda za’a bukata sai ayi a ciki.”
Da wani irin kallo ya bini
“Kamar me za’a yi dashi?” Ya tambaya yana kallo na, kin yarda nayi mu hada ido nace
“Amm.. ko za’a siya ragon da za’a yi mata hakika wai dama.”
“Aka ce miki ban siya ba? Bana bukatar kudin ki, nayi niyya ne ba wai dan wani dalili ba, nayi ne saboda Allah da ya halicce mu, kuma ya umarce mu da mu taimaka wa wanda yake bukatar taimakon.”
Daga kaina sama nayi, sai naga kamar ransa ya ɓaci, ajiye Iman din yayi a saman gadon ya juya zai bar dakin, sai kuma yaja ya tsaya yana juyowa
“Idan kina bukatar inda zaki ajiye ne, zaki iya bude account sai kisa a ciki duk abinda kike bukata sai kiyi a ciki.”
Daga haka yasa kai ya fice, shiru nayi ina tunani, ni banga abin fushi a magana ta ba, sai dai dukkan alamun sa sun nuna haushi yaji, ya zanyi toh ni? Me laifin abinda nace?
Ko da Hajiya ta shigo, sai ta hau min fada, kar na sake maganar duk abinda za’a yi wa Iman din, dan shi mutum ne mai saurin harzuk’a, na bata hakuri tace ya wuce. Tun daga lokacin bana taba cewa komai har idan bashi ne ya yanke ba, sati ya zagayo aka yanka mata abin yanka kamar yadda addini yace.
Sosai muke zaman mu lafiya da Ramlah, kasancewar ta mutum me faran faran da son mutane, Iman kuwa dukkan dawainiyar ta a wajen su take, idan tana makaranta Hajiya amma da zarar ta dawo shikenan ita zata dora.
Slip dina na ciro na post Utme d’ina na duba, date da komai, Ramlah na bawa ta gani kafin tace zata je ta kaiwa Ya Anas, har ta tafi kai masan ina tunanin amincewar sa, ina zaune ta dawo da fara’ar ta,
“Ya kukayi?”
“Yace kije da kanki wallahi, dama nasan haka zai ce wallahi.”
“Na shiga uku, wallahi kunyar sa nake ji Allah.”
“Toh kuwa sai ki hakura wallahi.”