DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Tsaki naja na tashi ina daukar mayafi na, baki daya sun kasa gane yanayin da zuciya ta take ciki, kokarin su na son ganin lallai sai na sake dasu, bani da yadda zanyi, haka na fito falon ina wara ido, a hakimce yake a saman kujera ya ajiye laptop a gaban sa yana aiki, be dago ba duk da yaji sallamar danayi masa, a ciki ya amsa yana cigaba da danne dannen sa hankali kwance, rasa ta ina zan fara masa magana, sai dana juya iya kalmomin da zan iya fada masa sannan na soma magana a hankali, har na kai aya be fasa abinda yake ba, be kuma kalle ni ba, sai kawai ya ture laptop din yana daukar slip ɗin nawa, dubawa yayi ya ajiye, ya sake jawo laptop din sa ya cigaba da aikin gaban sa. Mik’ewa nayi tsam nayi hanyar dakin zan koma naji yace

“Allah ya kaimu, best of luck.”

Cigaba da tafiya ta kawai nayi ba tare da na tsaya ba, nayi shigewa ta ina turo kofar, Ramlah na riƙe da Iman tana jijjigen ta, ba laifi akwai rigima idan ta fara kuka har sai kan mutum yayi ciwo, karbar ta nayi na yi mata abinda nasan zai sata shiru, da haka na dora sabon tunanin mutum daya tamkar da dubu wanda ya zama min kamar wata al’adah ta yau da kullum.


Daddy be sake neman sa ba, kamar ma ya bar maganar gaba daya, har aka soma kiran sa na gaggawa a wajen aiki, ranar yana hanyar Kano kiran ya riskeshi, ba tare da sanin madafa ba ya isa gidan na Dadah. Sai daya ci abinci ya huta sannan ya sanar da ita halin da ake ciki, ta jinjina lamarin duk da ta fara cire rai akan ganin Aminatu nan kusa, sai dai ba zata taba hanashi auren Amal ba, da shi da ita dukkannin su nata ne, babu wanda zata zaba sama da wani, dadin dadawar maraicin yarinyar, duk da babu laifi Maman na kokarin kula dasu, sai dai rashin uwa tun kana d’an karami ba abu bane me sauki.
Abu daya ta dogara dashi a halin yanzu shine Exams d’in da Aminatun zatayi wanda tabbas tasan idan har tana da rai da lafiya ba zata kasa zuwa ba, idan kuwa haka ne zatayi amfani da wannan damar wajen ganin ko za’a dace.
Sanda ta sanar masa da kudurin ta, murna ya hau yi, kamar ance an ga Aminatun ne an gama, duk da babu sanin takamaimai ranar da zata je ɗin, sai dai a hakan zasu duba ko Allah zai sa a dace d’in.
Bincikowa yayi ya samu date ɗin da za’a yi dukka Exams din da venue, ya had’a komai intact yana jiran ranar.

★★★
Ranar labari shine ranar da zatayi ta ta Exams din, tun ranar Monday suka fara jelar zuwa makarantar, daga nan suyi nan har la’asar babu alamun ta, haka suka koma gida washegari ya komo shi kadai ba tare da Dadan ba, nan ma haka ya gama zagayen sa daga nan zuwa nan har aka gama baki daya, ya sha wuya matuka sosai haka ya hakura babu komai a cikin sa ya koma gida yana fatan samun dacewa.

Karfe 9 zamu shiga hall saboda haka da wuri na shirya, Ramlah ma ta shirya don dama sunyi hutun makaranta, shirya Iman akayi saboda zamu biya ta banki daga makarantar, tare muka fito suna zaune da Hajiya yana shan tea, kallo daya yayi mana ya maida hankalin sa kan abinda yake yi, zama mukayi ya karasa Hajiya na dan jana da hira, tashi yayi yana mika min kofin kafin yayi hanyar fita

“Sai mun dawo Hajiya.”

“Allah ya bada sa’a, sai kun dawo.”

Kitchen na nufa na ajiye kofin na dawo mukayi mata sallama Ramlah na rungume da Iman muka fita.
Yana zaune cikin mota ya kunna ta,muka shiga ya ja muka bar gidan. Karo na farko dana fito kenan tun bayan zuwa na, kallon unguwar nake babu hayaniya, layi ne Babba me dauke da shinfidaddiyar kwalta, daidai kofar wani madadaicin gida me kyau da tsari gate din gidan ya bude a hankali, wata bakar mota me bakin glass ta fito, da wani irin gudu ya hau kan dan karamin titin ba tare da ya kula da motar mu ba. Tsaki naji Anas yaja cikin kuluwa yace

“Sojan nan yazo kenan!”

Ramlah ce tayi tsagal tace

“Jiya ma da Hajiya ta aike ni naga motar tasa, ba yau yazo ba.”

“Na tambaye ki?” Yace yana zare mata ido

“Bana son gulma da sa ido kinji, ni da nake da grudges dashi daban, mind ur bussiness.”

K’us tayi tana turo baki, ya sake jan tsakin yana kallon mirror din dake saman motar, hada ido mukayi ya harare ni nayi saurin sauke kaina k’asa. Zuciya ta na tsananta bugu jin ambatar sojan da yayi, tunanin Farouk d’ina ne ya dawo min, shi kadai na sani da hakan. Tun daga lokacin na daina sauraron komai, na fada kundin tunanin sa.

Rano????????????:     DAURIN GORO       
21

Gudu yake sosai muna biye dashi har makarantar, a wajen shiga suka tsaida shi ba’a barin me tinted glass shiga, kamar zai yi musu dasu sai kuma ya dawo da baya yayi wajen da aka tanadarwa masu irin glass din, shiga mukayi still Anas na ta mita, mitar yasan dokar kawai dan shi force ne zai taka, mu dai babu wanda ya tanka masa har muka isa gaban Hall d’in, fita mukayi ya nemi wajen parking mu kuma mukayi wajen gungun mutanen dake jiran zuwan examinars ɗin, zaman mu da kadan suka iso, nan dana aka soma screening ana shiga hall din, ba’a dau wani dogon lokaci ba aka fara, addu’a kawai nake duk wadda tazo baki na, saboda ba kowacce na sani ba, ba kowacce na iya ba, dama Farouk ne yamin alƙawarin sani a islamiyya da zarar ya dawo, ashe hakan ba mai yiwu wa bane.
   Na gefe na ne muka hada ido dashi, ya bini da wani irin kallo kamar ya ga kashi, mamaki ne ya kamani ganin ba wai sanin sa nayi ba, shigar jikin sa kadai ta nuna waye shi, da inda ya fito. Ban sake kallon sa ba, dan na lura dan zafin kai ne, na shiga abinda ya kawo ni. Har muka gama ban sake kallon ko in da yake ba, hanyar fita nayi ina sauri sauri, ya cimmini yana tsaida ni, kamar bazan tsaya ba sai kuma na tsaya, cikin isa da kasaita ya tsaya a gabana yana min kallon up and down

“Na sanki?” Ya tambaye ni looking as if ya taba gani na

“Kamar ya?”

Wani iri yayi da bakin sa, yana sake ware idanun sa a kaina, sai kuma yce

“May be, may be.”

“Ban fa gane ba .”

“Shit!, Kin tab’a attending birthday party haka or kinsan wani a abuja”

Juyawa nayi da nufin barin wajen dan na lura bashi da abun fada sam, sai ya sake biyo ni da sauri,

“I’m Kamal Marwan Dikko by name.”

“Baku gama bane?” Muryar Ya Anas ta kawo mana ziyara har inda muke, juyawa nayi na bar wajen da sauri ina tunanin yanayin da fuskar tasa ta nuna, inda na bar Ramlah na sameta, tana rik’e da Iman dake ta faman kuka, tana zagaye a wajen, tausayi ta bani ganin yadda tayi wujiga wujiga.

“Kar dai kuka take tayi miki tun da muka shiga.”

Nace ina karbar ta,

“Kuma kinsan batayi kuka ba sai yanzu, wannan da muka gani sojan nan dazu, har nan yazo, da yaji kukan ta har da karbar ta, yana da kirki na rasa me yasa basa shiri da Ya Anas wallahi, kinsan yana zuwa ya ganmu tsaye tare, ya haɗa rai ya karbe ta a hannun shi, dalilin barin wajen nan kenan da yayi, kuma dan mugunta irin ta Ya Anas yana tafiya ya dawo min da ita lokacin ta soma kuka,shine fa take tayi har yanzu, taki shiru.”

Dariya kawai na saka muna nufar motar

“Kika san me ya hada su, kinsan ance wasu masu khakhi akwai iya shege, duk da ba dukka ba, Ya Farouk ba haka yake ba sam.”

“Toh wannan din ma bashi da damuwa wallahi, zafin rai ne irin na ya Anas.”

“Maza ya jiki wallahi, ba ruwana.”

Dariya ta saka

“Nima wallahi ba ruwana nayi shiru.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button