DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Atoh, yafi dai.”
Jikin motar muka tsaya, tsawon lokaci sannan ya zo ya bude mana muka shiga, rannan nasa a jagule, kamar wanda akayi rigima dashi, banki muka wuce direct ya karbar min Form, na cike komai, wajen sa marital status ne har na zabi wajen Married, naga yayi min wani kallo, da sauri na gyara ina yak’e, na mika masa ya karba yana sake sakarmin harara. Dariya ma ya bani, na dan murmusa kawai, shi sam abin bacin rai baya masa kadan, komai abin ayi fushi ne, sai dai duk inda mutum me nutsuwa da kamala yake ya cika, bashi da hayaniya balle baragada, komai yana yinsa ne gently cikin tsantseni da takatsantsan.
Yana ajiye mu a gida be ko shiga ba ya ja motar ya tafi, Hajiya bata nan taje Barka, Baba Altine ce kawai a gidan ta gama aiki tana kishingid’e tana jin radio, sai a lokacin muka samu muka ci abinci sannan muka zauna muna d’an tayata hira.
★★★
Daya bayan daya mutanen dake cunkushe a harabar makaranta suka dinga yayewa, har ya zama na babu kowa sai yan tsirarin mutane, ran Farouk babu dadi ganin da gaske har ana neman gama wa babu alamar ta, hakan na nufin ta hakura da duk wasu muhimman abubuwan da suka dace da rayuwar ta kenan ko me? Baya so zuciyar sa tana raya masa wani abu mummuna ya faru da da ita, yana ji a ransa tana nan da ranta, kuma koman daren dadewa zata dawo gareshi. Amma yaushe? Yau? Gobe ko jibi? Babu rana balle wata, a duk sanda ya kira Shagari jikin sa kara mutuwa yake, a tunanin sa zata dawo baya, duk da yasan ba lallai bane tunanin ta ya kawo mata hakan, duba da yadda komai ya zo mata a lokaci daya.
Da kyar ya bar makaranta zuciyar sa babu dadi, yana zuwa ya rufe kansa a daki ya kwanta kawai, ba zai taba yafe wa Inno ba, da kuma duk wanda yake da hannu a ciki.
Sakon text message ɗin Ja’afar ne ya iso masa, ya bude yana karantawa
“Daddy na neman ka, idan da hali ka baro komai ka dawo Please.”
Ajiye wayar yayi ya koma ya kwanta yana yanke hukuncin amsar tayin na Daddy. Saboda haka yana tashi da safe ya sanar wa da Dadah kudurin sa, addu’a kawai tayi masa tare da sake karfafa masa gwuiwar yayi wa mahaifin sa biyayya.
Haka ya tattaro koman sa ya dawo, ya kuma jewa da Daddyn da albishir ɗin karbar tayin nasa, tsabar farin ciki a take ya kira waya ya nemi alfarmar barin sa ya tafi karatu na tsawon wasu shekaru ba tare da ya bar aikin nasa ba, babu bata lokaci aka gama komai aka hau shirye-shiryen biki na alfarma.
Shi dai sai ya koma gefe ya zuba musu ido kawai dan bashi da katabus akan komai zasu aiwatar.
Da yake abun na gida ne sati biyu aka saka, tun daga lokacin Mama ta soma aikin gyaran amarya, aka shiga hidima sosai tun da wannan su shine karon farko da za’a yi aure a cikin gidan, auren kuma na mutum biyu.
Wednesday suka fara events, dama sam babu wanda yasa ran Farouk din zai halarci abu ko daya a ciki, a harabar gidan dake manne da nasu da ya zama gidan shikiki kuma aminin Daddyn suke yin komai saboda girman sa.
★★★
Sanye take da takalmi me kamar slipers rigar jikin ta doguwa ce me budewa sosai, sai d’an karami mayafi data dora saman kanta, a hankali cike da farin ciki take taka harabar gidan har ta dangana da part din Mama, yan uwa ne cike kowa na zaune ana hada-hada, cike da karsashi ta karasa garesu, suka hau yi mata kirarin ga amarya ga amarya, bakin ta ya kasa rufuwa saboda tsabar farin cikin da take ciki, kan wata Anty ɗin su ta faɗa tana kunshe fuskar ta.
Tsokanar ta suka cigaba da yi, ta zame da kyar ta fada bedroom din su, sauran yan uwan su sa’annin ta ne da manyan ma da suka girme mata a zazzaune ana shafta, cikin su ta shige aka cigaba da yi dakin ya kaure da hayaniyar su.
Wayar tace tayi k’ara, ta daga da sauri, ganin sunan Yah Farouk yasa ta mike tayi saurin fadawa toilet tana saka key, shikiyanci suka hau yi mata tana jinsu ta daga wayar tana karawa a kunnenta
“Kizo side dinmu yanzu ina jiran ki.”
Fitowa tayi ta fice tana ji su sake tsokanar ta, har ta isa bangaren nasu babu kowa,tura kofar tayi ta jita a bude, ta tura kanta kai tsaye, yana kwance akan cusion ya daga kansa sama sanye da farar singlet da dogon wando fari, wajen sa ta nufa yasa hannu ya dakatar da ita
“Zauna a saman kujerar nan magana zamuyi.”
Jikin ta ne yayi sanyi ta zauna tana mamakin yadda yayi mata, tashi yayi zaune , idon sa sun kada sunyi ja sosai, gaban ta ya fadi da suka hada ido.
Takawa ya shiga yi yana kai komo tsakanin farkon falon da karshen shi ya gaza furta kalma daya, duk in da yayi sai ta bishi da kallo, har ya isa gaban system ɗin dake ajiye tana fitar da sautin suratul munafikun cikin kira’ar Ghamid’i. Kashe karatun yayi ya dauko d’an karamin Flash ya jona a jiki, hoton bidiyon da aka turo masa ne ya bayyana a saman screen din, dan zabura tayi, har ya iso gaban ta ya tsaya kusa da ita daf, ya kura wa videon ido yana masa kallon ssoai, hadiye yawu tayi cikin wani irin yanayi ta kalli fuskar sa, hankalin sa kachokam ya tafi kan kallon video, pause ya saka ya juyo yana hade hannayen sa suka bada sauti me dan karfi. Cikin shakakkiyar murya yace
“Ina kika samu Flash ɗin nan?”
“Ni… Ni? Na’am!”
“Kinji me nace, bazan sake maimaitawa ba.”
“Ni ba nawa bane, bansan nawa ye ba.”
Wani irin kallo yayi mata shakeke, kafin ya tashi yana matsawa baya
“Tun ranar da abin ya faru, ban taba hutawa daga binciken wanda zai min haka ba, I tried very hard na gano ranar da ni da kaina na zauna na rubuta takardar, sai dai na kasa.”
Dan sunkuyowa yayi daidai fuskar ta
“Kin tuna ranar da kika zo kika kawo min juice Ina aiki, ranar dana fada miki zanyi tafiya ina so kuje wajen ta, kin tuna?”
Daga kai tayi da sauri don har ta fara digar hawaye,
“Bude baki kiyi min magana!” Ya daka mata tsawa
“Na tuna.”
“Good, what did you do? I trust you the most, na kula dake na baki dukkan gata, kinsan komai nawa, what did you do?”
Ya fad’a cikin daga murya
“Ya Farouk, dan Allah.”
“Shissshhhhhhh…” Yasa hannu a saman leban sa
“Don’t say a word, bayan na amince miki, you betrayed me, kika bani juice da akayi mixing da abun da zai dauke min hankali, and you gave me this na rubuta same abinda ke jiki.”
Ya dago takardar yana nuna mata a fuskar ta da ita da kanta ta rubuta, karfin kukan ta ya karu sosai, wani irin harbawa jijiyoyin kansa suke, ba zai taba yarda idan aka ce masa Amal zata cuceshi haka ba, me yayi mata da yayi deserving wannan sakamakon? Tabbas abinda ya faru kenan ranar, amma yayi imani ba zata taba aikatawa ita kadai ba, dole sai dai idan da hannu wani babba,amma wa?
Kokarin saita kansa yayi dan yana son jin komai.
“Ki daina kuka, ina son sanin dalilin da yasa kika yi min wannan hukuncin, me nayi miki? Soyayyar dana nuna miki tun kina tsumma? Shine sakamako na?”
“Ya Farouk dan Allah kayi hakuri.”
“Amal hakuri, is that all? Kinsan halin da kika samu dukka? Dalilin haka yanzu ba’a san inda take ba, and kice nayi hakuri?”
Girgiza kai kawai take tana kuka sosai, tsugunawa yayi a gaban ta yana jin dama shima ya samu damar yin kuka, hannun sa ya dora a saman bakin sa, da sauri ta hadiye kukan da take tana ajiyar zuciya.
“Waye ya saki?” Ya zare mata ido sosai yana sake hada ransa