DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Yaaahh…”
“Waye ya saki!!!” Ya daka mata tsawa da karfn da ta kusa sakin fitsari a wando, babu bata lokaci ta shiga sanar mishi komai tana kuka sosai.
Kansa ne ya hau juyawa, ya soma ganin dishi-dishi, bayan samun evidence din da yayi a jakar ta da yadda abin ya dawo masa kamar Flash back, duk da ya shiga kaduwa, sai dai bai taba tunanin zasu aikata masa hakan ba, mutane uku masu matukar muhimmanci a rayuwar sa, wanda ya aminta dasu, yake ganin su a matsayin wanda suka fi kowa a wajen sa, su suka taimaka wajen tarwatsewar rayuwar sa, da baya da baya ya shiga takawa har ya dangana da daki, ganin haka yasa ta fita da gudu tana kuka sosai kamar ranta zai fita.
Daki ya fada ya saka kuka, kukan da ya jima yana neman sa, sai a yau ya samu damar yin sa, lallai ya chanchanci yayi kuka. Ya jima yana yi, sai da yaji kamar zai fita hayyacin sa, sannan ya tashi ya dauro alwala ya shiga gaya wa Allah kukan sa, yana sallar yana hawaye sosai, hawayen zallar bakin ciki yadda suka ci amanar sa.
Asubar fari ya tattara komai nasa yayi wa gidan kallon karshe, ya dau hanya ba tare da tunanin zai sake waiwayo wa ba har abadah.
Ranar data kasance ranar da za’a daura auren, a rana yayi bankwana da kowa nasa da dukkan memory d’insa da yayi tare dasu.
Karfe sha daya kamar yadda aka tsara, dubunnan mutane suka shaida daurin auren Amal Adam Shagari, Da Farouk Kabir Shagari. A daidai lokacin yana kwance a dakin hotel din daya sauka, ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi,ya san daga lokacin da Daddy zai gane yayi nisa, duk da yasan zai yi fada ssoai, zai kuma yi fushi dashi me tsanani, amma ba zai iya ba, ba zai iya zama ba, zai bi abinda zuciyar sa ta riga ta saka masa, ko da hakan na nufin zare shi daga cikin ahalinsa ne.
Rano????
Manage ????????
: DG
22
★★★
Kuka take sosai ta kudundune kanta cikin katon bargo, tana jin lokacin da aka sanar da daurin auren, amma bata da katabus, tana ji suka shigo baki dayan su, kowa na kokarin tsokanar ta, da sauri duk suka yo kanta ganin yadda jikinta ke faman rawa, suka shiga tambayar abinda yake damunta, kayan jikin ta ne tun na jiya, idanun ta sun kumbura sosai alamun kwana tayi bata runtsa ba, da sauri daya daga cikin su ta fita dan kiran Mama. A tare suka dawo dakin, ta dago ta tana karata jikin ta
“Baki da lafiya ne dama aamal?”
Kasa magana tayi, sai wani iri da take kamar zata shid’e, riko ta sosai Maman tayi suka fita daga dakin, dakin ta ta kaita babu kowa ciki, ta kwantar da ita tana kokarin kiran ko Ja’afar ne tun da tasan Daddy na cikin Jama’a. Be d’aga ba shi din ma, alamun shi ma ya shiga busy. Jawo mata kofar tayi ta dawo falon, daidai lokacin da Uncle Buhari ya shigo yana gyara zaman Babbar rigar sa.
“Ina Amal?” Ya tambaya bayan ya amsa gaisuwar matan dake falon
“Tana daki na, bata jin dadi ne.”
“Ok Ina son ganin ta. “
“Lafiya dai ko?”
“Eh kalou, magana zamuyi.”
Ganin da mutane wajen yasa tace ya biyo ta dakin nata,suna shiga ya matsa jikin gadon, ya duba ta kadan kafin yace
“Kunyi magana da Farouk daga jiya zuwa yau?”
Gaban ta ne ya fadi, tayi saurin girgiza kanta tana fatan ba wani abu yace ba, d’an jim Uncle Buhari yayi kamin yace
“Farouk fa ya tafi, ya ajiye letter a dakin su, yanzu haka Yaya bai san inda zai sa kansa ba, matsalar ma ba’a ga letter tasa ba sai bayan aure ya dauro.
“Innalillah wa inna ilaihi raji’un, mun shiga uku.”
Mama tace tana sallallami, karfin kukan Amal din ne ya karu, ta mike zaune tana sake bude muryar ta sosai, girgiza kai Uncle B yayi yace
“Kinga yi shiru kar ki ankarar da mutane halin da ake ciki.”
Da sauri ta rage kukan nata, sai dai bata daina ba, dan ita kadai tasan dalilin faruwar komai, a yau da tana da iko da kanta, data sanar wa kowa komai, sai dai bata da wannan damar, kenan a haka zata kare rayuwar ta? Ko akwai sauyin da zai zo bayan nan? Kiyayyar Aminatu ce ta shiga ninkuwa a zuciyar ta, duk itace dalilin komai, ta raba ta da Ya Farouk dinta, mai sonta da kaunar ta tun bata san kanta ba.
Cigaba da bayani Uncle B yayi, bata dauki komai a maganar tasa ba, sai data dawo daga tunanin da ta tafi taji yana yiwa Maman bayani
“Abinda nake tunani ko menene akayi wa yaron nan me girma ne, da zai sa shi yanke wannan danyen hukuncin, idan akwai abinda ya haɗa ku ki sanar mana, idan yaso sai asan yadda za’a bullo wa al’amarin.”
Ya kalle ta yana sake tambayar ta a karo na biyu, sake girgiza masa kai tayi tana goge hawayen fuskarta
“Bansan komai ba Uncle B, ni jiya ma tun bayan la’asar rabo na dashi.”
“Shikenan, ku kwantar da hankalin ku, kar a bari mutane su sani, idan kowa ya watse sai musan ta ina zamu ɓullo wa al’amarin.”
Fita yayi ya koma Falon da su Daddyn suke, waya ce a hannun sa yana ta making calls, babu wani information akai, yanke hukuncin kiran Dadah yayi duk da baya son d’aga mata hankali, amma yana tunanin xata iya sanin wani abu.
Yana gama mata bayani ta saki salati, sai kawai tasa kuka sosai, ta gaji da wannan abubuwan dake ta tasowa, ace daga wannan sai wannan? Idan fa wani ciwon ya kamashi? Ba taga ta zama ba.
Sosai maganar ta firgitata, iya sanin ta Farouk ba zai taba aikata abinda zai wargaza ahalin nasu ba, shiri ta soma yi, a yau bayan shekaru masu yawan gaske, zata sake taka garin na Abuja, garin da tayi wa kanta iyaka dashi saboda babban dalilin ta, tana shiryawa tana addu’ar komai yazo musu cikin sauki, dan ba zata juri wani abu ya sake bullowa a ahalin nata ba.
Driver ne ya iso, ya dauke ta da dukkan abubuwan bukatar ta, suka dauki hanyar birnin na abuja.
Tasbah ne ya hannun ta tana ja, bata jin dadin jikin ta kwana biyu, haka dai take daurewa tana yin komai, sai dai a yanzu yadda take jin jikin nata na neman rinjayar ta, addu’a take tayi tana rokon Allah ya daidaita al’amarin ya kare su daga sharrin masu sharri.
Mummy na zaune suna meeting da clients dinta kiran Ja’afar ya risketa, message ta tura masa tana meeting ta kashe wayar baki daya.
A gajiye ta fito bayan sun gama, takardu ne masu yawa a hannun messenger ta, hannun ta rike da yar karamar jakar hannun ta suka nufi motarta, sai data zauna a ciki gami da cilla jakar tata gefe sannan ta daga wayar ta kira shi tana kishingida a bayan motar.
“Mummy, akwai matsala wallahi, Ya Farouk ya tafi, babu wanda yasan ina yake, bayan an gama daura auren shi da Amal na shiga daki duboshi na tarar da letter daya ajiye, dan Allah Mummy ko ya fada miki ina zaije? Hankalin kowa ya tashi.”
Tuni taji gajiyar da take ciki ta warware, tashi tayi zaune sosai tace ma driver ta ya rage gudn motar,
“Kana jina Ja’afar? Ina yace ya tafi?”
“Be fada ba, yace dai yayi nisa kada a neme shi.”
“Dama aure Daddyn naku zai masa? Bani da masaniya akai?”
“Na zata kin sani naga yazo wajen ki before yayi accepting maganar ,shiyasa ma ban sanar miki ba.”
“Shikenan, ka kwantar da hankalin ka, bansan ina yake ba amma i ll try my very best naga na same shi, ka kwantar da hankalin ka.”
“Ok shikenan, sai anjjima.”
Ranta ne ya ɓaci, mamakin girman kiyayyar da Daddy yake mata har ta kai hakan, a karo na biyu ya sake aurar da dan nata ba tare da sanin ta ba, kwafa tayi tana lumshe idon ta, ta gaji da komai, dauriya ce kawai da karfin zuciya, amma wannan karon ya kamata ta nuna masa da gaske ita ta haifi Farouk ba wai shi kadai ɗin bane kamar yadda yake mata iko da gadara akan dukkan abin da ya shafe shi.
Maimakon ta wuce gida kamar yadda ta saba, sai ta sauya akalar motar zuwa gidan su, dan tabbas ba zata bar komai ba, zata nemo danta ta dawo dashi gaban ta, ta bashi dukkan kulawar da ta kamata. Dauriyar ta ta kare!