DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN????????
2260792279
MARYAM SANI
ZENITHBANK
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin????????
07067124863
GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA????????
09032345899
Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali????????????????????????????????????????????????????????
Mucigaba da shakatawa da wannan
©️Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
Ko kuma
09032345899
(3)
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Suka hada baki suka fada a tare.
“Yanzu ina ya kaita?” Baba ya tambaya cikin jimami.
“Wallahi muma bamu sani ba, mun dai zo mu sanar ne dan a sani, amma abunda yafi shine mu dunguma muje gidan su, idan yaso sai a sa ya fito da ita. “
“Abinda za’a yi kenan, kai Nura shiga kira min Yahya da Lawan duk mu dunguma, ba dan dare yayi ba ma wajen maigari zamu fara zuwa.”
A tare suka fito, Inno na tambayar su yadda ake ciki babu wanda ya tanka mata, suna fita ta sulale kanta na juya mata, tsananin tsoro ya hana ta motsi, idan ta tuna abinda zai faru.
Babu kowa a hanya har suka isa gidan, haske fitilu ne tarwai kamar rana, buga kofar Ilu ya hau yi da dukkan karfin sa Garxali na taya shi, Baba maigadi ya taso a zabure yana tunanin ko sune suka dawo. Yana budewa yayi turus ganin mutanen da be wani waye dasu ba a wannan daren, kallon kallo sukayi wa juna kafin yayi karfin halin tambayar su
“Lafiya dai?”
Lawan da duk yafi zafi cikin su ya bata rai yana leken gidan
“Yarinyar mu da kuka sace muka zo ku fito da ita.”
Da sauri Baba maigadi ya kalle su yana tuno abinda ya faru kafin isowar su, kar dai ace? Da sauri ya kauda tunanin yana mai tabbatarwa kansa hakan ba mai yiwu wa bane, yasan waye Farouk, yasan me zai aikata, duk da ance ba’a yabon yaran yanzu, sai dai yana kyautata masa zato ko ba komai yaro ne nutsattse.
“Kayi magana mana, wallahi ko a fito da ita ko mu nuna muku mune muke da garin nan dan uwar mutum.”
Garbati ya katse masa tunanin da ya tafi na wucin gadi, kallon su yayi daya bayan daya yana yanke hukuncin abinda ya kamata ya sanar musu.
“Bansan me kuke magana akai ga gaskiya, babu kuma wata yarinya da tazo gidan nan, amma ku bari na shiga ciki na yi magana da masu gidan.”
“Karya ne wallahi, karku yarda Malam Ayubah, yaran gidan ne a gaban idon mu ya sungume ta ya tafi da ita, bayan ya gama da ita, Allah ma yasa ba yan yankan kai bane wallahi.”
“Subhanallah!”
Sai a sannan Baba yayi magana yana jan murya
“Kayi wa Allah idan diyata na hannun ku ku fito min da ita, hankalin mu gaba daya a tashe yake, dan Allah na roke ka.”
“Wallahi Baba bansan komai akan maganar da kuka zo da ita ba, amma me zai hana mu bar maganar zuwa garin Allah ya waye, a lokacin masu gidan ma sun tashi, kunga sai ayi magana sosai.”
“Kana nufin mu bar maganar yar mu har sai gobe, bamu san halin da take ciki ba, idan ma cinye ta za’a yi ko kashe ta zuwa goben kaga shikenan ko?saboda ba yarka bace ta bata ba. Toh wallahi ba’a isa ba.”
“Ni dai kuyi hakuri dan Allah.”
Zasu sake magana Baba ya dakatar dasu
“Mu bar wa goben idan Allah ya kaimu, ita kuma Allah ya bayyana mana ita, ku muje dare na sake yi.”
Haushi ne ya taso wa Garbati, ba haka yaso a tashi wasan ba, so yayi su kutsa kai gidan ya samu damar cin uwar yaron nan, kwafa yayi a ransa yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai masa idan Allah ya haɗa su. Zai gane ya tana Gaza Boy.
***Karamin asibitin dake garin suka kaita, babu alamun ma ana aiki a asibitin, maigadi ne kawai yayi saura da yar karamar torchlight din sa babu isasshen haske, Farouk kamar zaiyi kuka haka yaji sanda maigadin ke musu bayanin babu kowa a ciki sai majinyata. Juyawa sukayi suka dau hanyar fita daga kauyen baki daya.
A lokacin jiki na ya kara tsami sosai, ko ina ciwo yake min zufa nake kamar wadda ta hadiyi kunama, babu abinda nake sai kuka Amal na tayani, Dada kam duk hankalin ta ya kara tashi, musamman ganin yanayin da na sake shiga daga fitowar mu zuwa yanzu.
Juyowa yayi a hankali yana kallon bayan motar be ce komai ba sai kura musu ido da yayi yana jin kamar ya bude motar ya fita, yasan Amal da raguwar zuciya da saurin kuka, kasancewar ta marainiya wadda bata san mahaifiyar ta ba yasa yake tausaya mata, baya son ko kadan yaji kukan ta, sai dai kukan yarinyar da yake ji yana neman danne kukan Amal din, har ya zama baya jin na Amal din sai nata kawai dake masa yawo a cikin kunnen sa, zuciya da ruhin sa.
Suna zuwa asibitin aka karbe su, suka zauna a reception aka shiga da ita ciki, Farouk kasa zama yayi ya shiga kai kawo a wajen yana ayyana rashin imanin wasu mazan, basu da maraba da dabbobi. Fitowar Dr Iman yasa duk suka mike, kallon su tayi sosai taga babu alamun kauyanci a tattare dasu, dan bata fuska tayi kafin tace
“Kuzo office Ina son magana daku ku biyu.” Ta fada tana nuna Farouk da Dada, rufa mata baya sukayi suna shiga ta tura kofar tana jingina a jikin kujerar ta
“Menene alakar ku da patient din nan?”
Kallon Farouk Dada tayi zatayi magana yayi saurin katse ta
“We are Family Dr.”
“Good.” Tace tana zama
“Kenan my guess was right, kunyi wa yarinya karama at her age aure, sannan saboda rashin imani ka kasa hakuri da kankantar ta, kayi forcing kanka akanta ko?”
“A ah likita…” Dada tayi saurin katse ta, kafin ta k’arasa yayi maza ya sauke kansa kasa a hankali ya furta.
“Haka ne Dr, I’m very sorry, kuskure ne.”
Biron hannun ta ta saka a bakinta tana kallon sa, shi a karan kansa ba wani babba bane, bata jin zai dora shekaru 20 idan ya dara to ba zai fi da biyu zuwa da hudu ba, yanayin jikin sa na girma da cika yasa zaka kasa tantance shekarun sa, sai dai duk da hakan ba za’a hada shi da yarinya yar shekara goma da doriya ba. Cire glasses din idon ta tayi ta fara magana a hankali cike da nasiha, dan a yadda tayi niyyar shigar dashi kara duba da yadda ta ga halin da ya saka yarinyar a ciki, sai dai yadda ya amsa laifin sa kai tsaye yasa ya sauko ta shiga nasiha da dukkan kokarin ta.
Hannayen Dada a makale da ita ta zuba su akan Farouk din, mamaki ne karara kwance a fuskar ta, bata gane nufin sa ba, bata gane inda ya dosa ba, tasan shi da tsananin tausayi amma bata taɓa tunanin zai iya aikata daukar laifi a ajiye akansa ba, tuni zuciyarta ta sake tsinkewa, idan har hakan ne kuwa ya tabbata Farouk din ne ya bata musu yarinya, in kuwa hakan ta kasance bata san ya zatayi ba.
Bayan sun fito daga dakin Dr yaki yadda su hada ido sam Dada, yasani sarai tana bukatar gamsasshen bayani, amma baya so ya sanar mata da komai sai ya samu nutsuwar zuciya.
Dakin da aka kwantar da ita suka tura suka shiga, Amal na zaune kan kujera tana bacci, drip ne a daure hannun ta, bacci take sai dai yanayin fitar numfashin ta ya nuna tsantsar wahalar da take ciki, karasa wa yayi gaban gadon yana sake kallon ta.