DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

∞∞∞
Dadah basu isa Abuja ba sai daf da magriba, lokacin kowa ya watse sai yan tsirarin da suka zama dole, Daddy na zaune a masallacin gidan Aminin sa, tun bayan da aka idar da sallar la’asar suke ciki ba tare da sun fito ba, sosai tafiyar Farouk ta bige shi har yana jin kamar bashi da lafiya, zuciyar shi tayi sanyi,  tabbas yana tsaurara wa a duk abinda ya shafi Farouk din, ya rasa dalilin da yasa baya iya tsayawa ya saurare shi, ko ya bashi damar kare kansa.
    Sai da aka yi magriba da isha’i sannan ya fito, ya nufi cikin gidan nasa yana takawa a hankali, da motar dasu Dadah suka zo ya fara tozali, da dan saurin sa ya nufi shashen nata da zama mallakin ta a dah, Wanda yake a rufe tun bayan tafiyar ta, taron biki yasa aka bude shi saboda mutane, bakin sa dauke da sallama ya shiga, suna zaune dukkan su, Mama na daga kasa wajen kafarta, sai Amal datayi matashin kai da kafarta tana kuka k’asa-k’asa.
   Waje ya nema ya zauna, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa kafin su fara zamewa daya bayan daya suna barin falon, su biyu sukayi saura, daga ita sai shi, kallon sa tayi a tsanake, da hango tsantsar ramar da yayi, wadda ba zata wuce a wunin yau ta same shi ba, Tabbas ba abu bane mai sauki ba tafiyar Farouk din, sai dai a yau zata nuna ma Daddy kuskuren sa, zata sanar dashi abinda ya gaza fuskanta.

“Kabiru…” Ta kira shi da sunan shi kai tsaye, sai yaji zuciyar sa ta kara karyewa, tabbas ko menene zata fada masa yasan me girma ne, cikin girmamawa yace

“Ina neman gafarar ki Dadah, idan na bata miki dan Allah.”

Gyara zaman ta tayi, cikin jan hankali tace

“Idan nace kamin laifi nayi karya, tsakani na dakai, babu abinda zance maka sai Allah yayi maka albarka, ka zama baya goya marayu, ka rike kowa naka, ya’yan yan uwanka ka kula da su da al’amarin su, ba tare da ka duba abinda ya faru a baya ba, sai dai kayi kuskuren wofintar da naka duk da sunan son hukunta mahaifiyar sa, menene laifin sa a ciki abinda bashi da masaniya akai..?”

“Baka taba bashi damar jin ta bakin sa ba, komai yayi laifi ne wajen ka, baka taba damuwa da halin da yake ciki ba, halin da zai shiga, duk da haka yana kokarin yi maka abinda kake so.”

“Ina ji a jikina a duk inda yake ba a dadi yake ba, akwai babban dalilin da yasa shi barin mu.”

“Nayi kuskure, ban taba jin abinda nake aikata masa laifi bane, sai yau, sai dana samu wanda zai fahimtar dani, tun safe maganar da muke kenan da MD, me yasa na kasa gane haka? Sai da lokaci ya kure min, ya zanyi da auren da ke kan Amal? Na rasa ina zan saka raina naji dadi Dadah, komai ya tsaya min.”

“Hakuri zamuyi, mu bar wa Allah komai, mu bashi lokaci muga yadda abubuwan zasu sauya, watakila ya waiwayo mu, idan ransa ya saki.”

“Allah yasa, bana son matsala ta sake faruwa, ina son yadda muka binne komai, kada wannan matsalar ta tono shi, zuciya ta ba zata iya daukar maimaituwar abinda ya shud’e ba.”

“In Sha Allah hakan ba zata faru ba.”

Cigaba sukayi da tattaunawa, a hankali cikin hikima Dadah ke kara nuna wa Daddy laifin sa, sosai jikin sa yayi sanyi, yaji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk a dalilin rufe sirrin gidan nasu, ya bata wa d’an sa komai, da hannun sa ba tare da ya ankara ba. Tsaki yaja yana tuna shi,ba zai taba yafe mishi ba, duk kuwa da k’asa ta riga da ta rufe idanun shi a yanzu, amma tabbas ya bar musa tabo babba a zuciyar sa da ba zai taba iya goguwa ba.
   Kwana Dada uku a daddafe ta tabbatar da komai ya lafa, ta hau shirin juyowa, rokon da suka dinga yi akan ta zauna dasu, ki tayi dan hakan shine abu na karshe da ba zata iya ba. Amal ce ta roki alfarmar zata bita, kai tsaye Daddy ya amince , ta haɗa kayan ta ta bita don samun nutsuwar zuciya.


Hakimce take saman kujerar ta ta gado, me samfurin karagar mulki, farar tsohuwa wadda a ƙalla ta doshi shekaru tamanin da yan kai, bata da Abu mafi soyuwa a rayuwar ta fiye da jikin nata wanda ya kasance d’a kwaya d’aya tak.
   Hajiya Turai kamar yadda sunan ta yake, wadda tsabar farin ta yasa aka saka mata sunan, gashi har tsufan ta tana nan da farin nata da ya sake haduwa da hutu da jin dadi.
   Sanye yake da rigar sa marar nauyi da gajeren wando da be wuce masa guiwa ba, hannun sa rike da football yana dokata a hankali ya isa falon.
   Fara’ar fuskarta ce ta dadu, ganin abinda yafi komai soyuwa a gareta, dukkan soyayyar da take wa mahaifin sa ce ta dawo kansa, da ya zama da d’aya tilo da ta haifa a duniya, bayan ta cire dai ta fitar da tsammanin samun sa.
   Zama yayi yana cigaba da doka ball ɗin yana kamawa, ransa a bace babu walwala, tasan kwanan zancen,saboda haka ta shiga yi masa kirarin data saba masa a kodayaushe, biris yayi da ita kamar bai san tana yi ba,

“Wanane ya taba min kai wai?”

“Haba Old Woman kinsan fa dalilin fushi na, nace ku fada masa bana son karatun a Nigeriar ma baki daya kunki, ace a rasa ina zanyi University kamar ni sai a Kano, a Kanon ma ba Private Uni ba, chan ta kowa da kowa har da ya’yan talakawa, Allah ya gani an cuceni walalhi.”

“Ka kwantar da hankalin ka, ka fara chan ɗin tunda ya kafe, idan yaso a hankali sai na sashi dole ya fitar da kai wajen, amma sai ka fara rage rawar kan naka ya tabbatar ka nutsu sosai.”

“Ni wai wacce rawar kai nake, haka kullum Ammi sai faɗa take min, ke kadai ke sona sai Anty, ni na gaji da gidan nan ma baki daya duk babu dadi ayi ta yimin iyaka da abinda ya zama mallaki na.”

“Yo dama uwar ka ai ba sonka take ba, ka rabu dasu duk zanyi maganin su dan uban su, kaji shalele na, ka daure ka fara chan din tunda ya kafe.”

“Old Woman…” Ya kafe ta da ido

“Wai bake kika haifi Dad bane?”

“Nice mana, me ka gani.”

“Kawai ki tilasta masa kice kin gama magana ya kaini waje nayi karatu.”

“Ba za’a kai ka ba, dan gidan ku.”

Da sauri ya mike yana sosa kai, yayi wuri wuri da ido yana neman hanyar fecewa daga falon, matsowa yayi har gaban sa kafin ya sakar mishi rankwashi a tsakiyar kai, da karfi yasa ka ihu kamar karamin yaro, hakan yasa Hajiya Turai yin salati tana tafa hannu

“Karka kashe min shi, rankwashin nan sai ya juya masa kwakwalwa ai.”

Kunkuni ya saka ya bar falon da sauri.

“Hajiya duk ke kike biye masa wallahi, yanzu Kamal shekara nawa yake? Amma bai san abinda ya dace da wanda be dace ba, gashi kinga ni shekaru na kara hawa suke, yaushe zai yi hankalin da zai kular min da dukiya? Ya kula da mahaifiyar sa dani? Lokaci fa tafiya yake.”

“Ka kaishi wajen daya ke kulafuci mana, chan anfi saurin karatun nan danan sai yayi ya gama ya dawo.”

Girgiza kansa yayi

“Hajiya dan Allah, mu bar wannan maganar, Kamal zan dauka na kai waje? A gaban mu ma ya yakare? No bazan taba wannan gangancin ba.”

Juya masa baya tayi, tana magana kasa-kasa, sallama yayi mata ya fita dan yasan idan ya biye mata rigimar da zata sashi a gaba tayi ba kadan bace. Bayan motar sa ya fada yana addu’ar shiriya ga tilon dan nasa, duk kuwa da yasan laifin na mahaifiyar sa ne, taki barin su sam suyi masa nagartacciyar tarbiyyar data dace dashi.

Niko Nace hmm, Allah sarki su malam Kamalu an zake da yawa????????


Gaisuwa ta musamman gareki Oum Iman me comment da readmore???????? Allah ya bar kauna. Muna gani kuma muna godia.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button