DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dade baje ba, kuyi hakuri a hankali zamu warware komai, Daurin Goro labari ne me rassa da zaruruka da yawa. A hankali zamu kawo inda muke son zuwa.????

Comments dinku na kara mana kwarin guiwa sosai, mungode.: DG
             23

★★★
Tun daga kan zauren gidan zaka tabbatar da san samu chanji ta kowanne bangare, tana zaune gaban kofar dakin ta, ta yi tagumi tana tunanin rayuwar baki daya, idan aka ce mata komai zai chanja rayuwar ta juya mata baya cikin dan kankanin lokaci zata musa.
Tun bayan fitowar su daga police station bata sake samun nutsuwa ba, magana ta zagaye kowanne lungu da sako na kauyen nasu, bata da damar fita nan da chan, sai kaji ana yar mata da magana. Dalilin haka ta hana kanta fita, gashi komai ya tsaya mata na abinda ya danganci sana’ar ta.
Jikin Baba ya sake matsawa sosai, haka dai suke jinyarsa ita da yalwati duk da karfin jinyar ma ta Yalwatin ce, ita kanta tana bukatar a kula da ita dan kuwa ba isashiyar lafiyar ce da ita ba.
Karime ce ke dan lekowa lokaci zuwa lokaci tana duba su, ta tafi, da haka ake rayuwar cikin kankanin lokaci dan jarin nata ya kare sai yan dabbobin da suka rage mata. Tabbas ko a haka aka barta ta gane kuskurenta, tana ji a ranta bata kyauta wa Aminatu ba, duk da a tunanin ta ta aikata hakan ne don taimaka mata, amma tabbbas tayi kuskure, ta ina ma zata fara neman ta, ta haifi abinda yake cikin ta ko yaya! Wannan tunanin biyu ke sata sake shiga cikin matsanancin tashin hankali.
Cikin dare jikin Baba ya sake rikicewa, babu wanda ya runtsa a gidan, wani irin abu yake fitar wa daga bakin sa, ala tilis da safe suka nufi asibiti bayan ta barwa Nura sallawun daukar guda cikin dabbobin ta ya kai kasuwa wajen mahauta su siya saboda kudin asibitin da za’a bukata.
Ba’a karbe shi ba, har sai da Nuran ya kawo kudin,sannan aka bude masa file aka karbe shi, kafin kuma asan abun da za’a bukata a gaba.


Duk hanyar da take tunanin zata same shi ta bi, tayi dukkan kokarin ta amma babu wani labari. Sosai zuciya da ruhin ta suka kosa da abubuwan, tana bukatar wanda zata fadawa damuwar ta, tun bayan rabuwar su da Daddy ta zama mace me matukar tsauri, bata barin kowa ya rabe ta, bata sabo da kowa balle ta saki jiki , agogo ta mayar da kanta,ko yaushe cikin aiki take ba dare ba rana, duk don son ganin ta manta komai. Sai dai a halin yanzu ta karaya, zuciyar ta tayi laushi ainun, tana son wani a kusa da ita, da zai jibanci al’amuran ta, ya saurari kukan ta, amma waye? Bata da kowa a halin yanzu sai babbar yayarsu data rage dake zaune a cikin garin na Kaduna, wadda itama girma da dawainiyar yaya da jikokinta kadai ya ishe ta, ranar data bar wajen meeting dinsu chan ta nufa, da niyyar ta sanar da ita kukan ta, sai kuma ta tarar da ita ma da tata matsalar, dole ta hakura ta boye natan har ta baro gidan.
Kwanan ta kusan hudu bata sake leka waje ba, jinya take sosai, jiki da ruhi, komai baya mata dadi, tana jin ta kamar a yanzu komai yake faruwa, duk abubuwan data shafe su a babin rayuwar ta a baya, yanzu sun dawo mata suna mata amsa kuwwa a kanta.
Rashin uzurin Daddy da yadda yake rufe idon sa ya kasa gano gaskiya komai,ya sake jefa rayuwar d’an su a wani hali. Ba zata taba bari rayuwar dan nata ta salwanta kamar yadda komai ya chanja mata a rana daya tak!


Bai taba tunanin zai shiga damuwa kamar haka ba, sai gashi komai ya kakare masa, tafiyar Dadah ta kara sashi a wani yanayi, maganganun ta ne ke kai kawo a cikin ransa, babu abu daya data fada masa da bai zama gaskiya ba, sai gashi yana jin son sanin abinda ya faru a bayan, duk da ya rufe babin nan a rayuwar sa, amma kuma wani bangare na zuciyar sa na son sanin komai, watakila hakan zai taimaka wajen samun haske a wannan sabuwar matsalar data same su.
Ita kadai ce zata sanar dashi komai, sai dai yasan ba zata taba sauraran sa ba, duk da kasan zuciyar shi na nan akan bakan sa na abinda ya aikata mata shine daidai da ita, amma kuma yana jin kamar bai mata adalci ba, kamar yayi tsauri wajen yanke mata hukunci, duk da abu ne daya shafi mahaifiyar sa da d’an uwan sa shakikinsa, amma kuma da ya bata dama, yaji wani bangare na labarin ta, sai dai kash, bai yi hakan ba, a lokacin ma sam baijin zai iya bata wannan damar, yadda zuciya da ruhin sa suka azabtu da abinda ta aikata masa. Bata kyauta masa ba, bata kyauta ba!
Mirginawa yayi yana gyara kwanciyar sa, zai dora tunanin sa Mama ta turo kofar dauke da wayoyin sa da ya baro su yashe a saman teburin falon sa. Mika masa tayi ya duba kiran, misscals ɗin MD ne, shaf ya manta sunyi zasu hadu a yau din, tashi yayi ya shirya kansa ya sauya shigar sa daga doguwar jallabiya zuwa farar shadda da hula ya fita. Kai tsaye gidan sa ya nufa, ya shiga ya nufi babban Falon sa da yake ajiye duk wani bako mai muhimmanci a wajen sa.

★★★

Rayuwa ta a gidan bayin Allah nan rayuwa ce me cike da kyautatawa da mutuntawa. Na gama gane halin kowa a gidan naci kuma alwashin zama da su da halin su, zuwa ranar da zamu rabu, tunda nasan ba zamu taba dawwama a haka ba, dole watarana xan tafi.
Iman bata da matsalar komai, girma da wayo kawai take karawa abin ta, duk wani abinda za’a bukata nata Anas na samar mata shi tun kafin a nema. Kunsan ance me d’a wawa, hakan ya kara mishi matsayi babba a zuciya ta, ina jin sa kamar wani uba ko babban wa a garemu, ina jin sa kamar wanda aka aiko shi dan ya taimaka wa maraicin mu nida ita a lokacin da muka rasa madafa.
Ina zaune ina ninke kayan ta da na wanke da rana Ramlah ta shigo a gajiya ta fada saman gado tana sakin nishin gajiya

“Makaranta akwai wahala wallahi.”

“Bayan wuya?” Nace mata ina dariya

“Kafin dadin fa? Aiko kinga naji labarin ance Post Utme ta fito fa.”

“Innalillah, kinji yadda naji, Allah sa muna da rabo, karatun nan shine kadai hope d’ina.”

Na faɗa a sanyaye,

“In Sha Allah zaki samu, akwai abokin Baban mu wani professor kuma nasan Ya Anas yayi masa magana, nima dan cut-off mark d’ina na jamb be kai na buk ba shiyasa na chanja northwest.”

“Toh Allah yasa,kinga har naji kamar bani da lafiya wallahi.”

“Allah sa muji Alkhairi.”

Amin nace ina cigaba da aikin da nake, sauya kayan jikin ta tayi ta nufi Kitchen dan samo abinda zata ci.
Da daddare kamar yadda muka tsara Ramlah na koya min karatun daya shafi addini, ba laifi ina karuwa sosai da ita, duk abinda kake da interest akai kana tsayawa ka koya sosai, hakan ce ta faru dani, zama na dasu na gane bansan komai daya danganci addinin ba, daga karatun sallah sai dan abinda ba za’a rasa ba, bana mantawa a makaranta na koyi yadda zan kula da kaina yayin lokacin al’adah. Shiyasa na dage nake takura ta a kullum tana karamin sani a abinda ya shige min duhu.
Da hannun sa rataye a bayansa abinda ya zama masa dabi’a ya shigo dakin namu da sallama, kusan sati guda kenan baya zama sosai a gidan aiki ya masa yawa kamar yadda naji Ramlah na fada, daina karatun mukayi muka maida hankalin mu wajen sa, be ƙaraso ciki ba ya tsaya yana kallon mu, a tare muka hada baki muka gaishe shi, ya amsa a sake kafin yace

“Congratulations, sai jiran admission kinci postutme.”

“Alhamdulillah.” Na shiga jerantawa, cikin tsananin farin ciki na hau yi masa godiya, rana ta farko dana ga babu wannan cunkushewar a fuskar sa, a sake yake amsa min yana yi yana min wani kallo.
Yana fita muka rufe karatun muka yi dakin Hajiya, dan sanar mata, tayi murna sosai ta saka albarka. Daren ranar ban iya runtsawa ba, tunanin Farouk da yadda zaiji idan yana tare dani kawai nake, tun bayan tsawon lokaci yau naji alamun ina da rabo a rayuwar nan.
Haka na tashi da safe cike da farin ciki da walwala, tsokana ta su Hajiya da Altine sukayi tayi ina dariya. Da wuri muka gama aikin mu da zamuyi ranar na bi Altine kitchen ina kara koyon abubuwan da ban taba sanin ma suna existing ba sai yanzun.
Cikin hukuncin Allah Admission ya fito, sunana na jerin sunayen farko da suka samu, nayi farin ciki ranar nayi kuka sosai na kuma godewa Allah, saboda nasan ba wayo na bane ko dabara ta. Tun daga lokacin na tattara dukkAn damuwa ta na watsa ta a bayana na shiga shirye shiryen sabuwar rayuwar makaranta.
Yadda Ya Anas ya soma chanja min ne ya shiga daure min kai, duk lokacin da yake gida ya kan tabbata da ina falon a zaune, duk hirar da za’a yi sai ya sako ni a ciki, ta karfi da yaji yake kokarin ganin sai na sake dashi, ina lura da yanayin Hajiya kamar bata son hakan, duk sanda zai min wata magana sai ta kawo abinda zai sauya akalar maganar zuwa wata daban da bata shafe ni ba. A haka aka fara registration da screening, shine dai wannan karon ma ya shige min gaba akan komai, sannan duk kudin da aka bukata shi ne ya bada su, duk da naso yin wani abun da kaina sai dai sanin halin sa yasa na hakura na zuba masa ido.
Kwana wajen uku sannan na samu nayi screening din, na gama ina zaune karkashin wata bishiya me dauke da zagayayyun kujeru naji an zauna a gefe na, dagowa nayi da nufin ganin waye, hannu yasa ya nuna ni cike da mamaki yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button