DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kin batar dani Ramlah, kina nufin Amal nada hannu a komai?”
“Eh haka tunani na ya bani, ko da ba komai ba, amma a wannan lokacin akwai ayar tambaya akan, akwai babban dalilin da yasa tayi miki hakan.”
“Taki bani damar da zan san inda take, ballantana na rok’i alfarmar ta hadani dashi ko da na dan sakanni ne, akwai tambayoyin da nake son yi masa ne, sannan na nuna masa abinda ya tafi ya barni dashi, shine kawai buri na.”
“Shiyasa nace miki abinda tayi nada alaka da hakan, tabbas bata son haduwar ku dashi ne, idan har ya cire ki a ransa, ba zai ji shakkar haduwa dake ba, ita kuma kai tsaye zata hada ku dan tasan bashi da alaka dake, amma me? Sai taki ta hauki da cin mutunci, Allah ma yaso ta ba tare dani bane, wallahi da sai na saki shegiya na yar a wajen.”
Murmushi nayi ganin yadda ta hakikance, sai na zame na kwanta a wajen ina jin kamar wata dama na samu mai muhimmanci a rayuwa ta ta kuma kubce min. Yin ranar haka nayi shi sukuku, abincin kirki ma ban iya ci ba, daren wuri na lallaba Iman tayi barci ni kuma na hau kogin tunani.
Dan buga gadon tayi tana harara ta, sai a lokacin na lura da tsaiwar ta akai na
“Allah ki rage tunanin nan, is not good for ur health,ki taso Ya Anas na kira.”
“Bacci fa na fara, Please kice masa nayi bacci kaina ke ciwo kinga kuma ina bukatar hutu.”
“Kinsan shi sarai, sai ya zo har dakin, babu ruwana wallahi ki taso ni nayi gaba.”
Ganin da gaske tayi ficewar ta yasa na mike da kyar na dauraye fuskata na zura dogon Hijabi na fito, idon sa kur akan kofar dakin namu, ina kallon yadda ya sauke ajiyar zuciya a boye ba tare da sun ankara ba, dauke kaina nayi na karasa na zauna a gefen Amal,.
“Bak’ya gajiya da zaman daki?”
Yace yana kallo na, da sauri Hajiya tace
“Bata fa dade da tafiya dakin ba, kaine dai zuwan ka kenan shiyasa.”
“Duk da haka Hajiya, ta fiya takura kanta a daki, ya kamata ki dinga fitowa ana hira dan an riga an zama daya kin gane?”
Daga kaina nayi bance komai ba, maida hankalin sa kan Hajiya yayi
“Ina ganin shawarar siyan adaidaita sahun (babur mai kafa uku) ita kawai zamu dauka kawai, ko hudu ne a samu a siya sai a dinga kawo balance duk sati.”
“Hakan yayi, Allah ya taimaka.”
“Nace ba, idan tana da ra’ayin hakan sai a hada da ita, idan yaso ita ma sai a dinga kawo mata wani abu duk sati…”
Ya karashe yana kallo na,
“Kina da ra’ayin siyan abin hawa ana miki haya? Kudin ki zai isa ki sai guda daya ko ba sabuwa bace, idan Allah yasa miki albarka sai kiga kin maida kudin kin sayi wata.”
Dadi ne ya kamani, dama ina ta tunanin abin yi, tunda zaman ba zai yiwu haka ba, ko ba dan Iman ba ko dan makaranta ta, da sauri na amince, dan shine kawai abinda nasan za’a yi min ɗin ba tare da ya shiga lokacin makaranta ta ba.
Murmushi yayi, daga ganin yadda na amince din yayi masa dad’i, dan shi mutum ne mai son a yarda shi, kuma kai tsaye yake nuna maka yadda yaji game da kai.
“Shikenan, Nagode da damar da kika bani, sai a hada a siya dukka Hajiya, hakan ina ganin yayi ko?”
“Yayi.” Tace Muryar ta a dan ciki
“Yauwa Anas, wai ya maganar da mukayi ne tun ranar? Shiru fa nake ji ya kamata kasan abinda kake ciki, shekarun ka kara ja suke.”
“Hajiya kenan, ai ina ganin lokaci kawai nake jira na bayyana miki komai, ki tayani da addu’a kawai ta karbi tayi na, dan nasan zaki yi farin ciki sosai da zabi na.”
“Ah masha Allah, shine tuni baka sanar dani ba? Ka barni ina ta tunanin wa zan binciko maka a dangi.”
“Na hutassheki Hajiya, ke zaki fara sani bayan ita, kuma nasan zaki yi farin ciki sosai dan yarki ce ma.”
“Toh madallah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi.”
“Amin ya ALLAH.”
“Naji kamar kuka ko? Jeki duba ko tashi tayi.”
Mikewa nayi na musu sallama, kallon k’asan ido naga yayi min, nayi gaba da sauri ina jin faduwar gaba.
Kamar wadda aka koro haka ta shiga gidan tana waiwaye, ajiyar zuciya ta sauke da karfi ganin bata biyo ta ba, lock ta saka wa kofar ta shige ciki. Kallon tuhuma Dadah ta bita dashi kafin tace
“Ina kika je ne nake ta neman ki, baki fada min zaki fita ba kuma.”
“Kati naje na siyo, ina so nayi waya na kasa siya ta bank shiyasa.”
“Shine kike abu kamar baki da gaskiya?”
“Ni ba abinda nake kece kika ga hakan.”
Tayi cikin dakin ta, tana shiga ta murda dan key din jiki ta cire mayafin ta ta haye gadon tana kiran number. Kasancewar akwai rata da tazara me yawa tsakanin su, sannan akwai banbancin lokaci yasa suka tsara sanda zasu dinga magana a waya, tun da tazo gidan sau biyu kawai sukayi waya. Kamar ba za’a daga ba, dan har ta fara cire rai, sai kuma taji an daga ɗin, cikin magana k’asa-k’asa ta shiga bayanin komai, bata wani dau tsawon lokaci ba ta ajiye wayar tana murmushi.
Duk ranar da Farouk ya gama boye-boyen sa zai fito, daga lokacin zai karbe ta a matsayin matar sa, dolen sa ne, tilas ɗin sane hakan,da shi kadai zata iya rayuwa.
Sam tafiyar sa bata dame ta ba tun bayan da aka tabbatar mata da ita din matar sa ce, aure ya dauro, zata jira shi komai daren dadewa, sai dai ba zata taba gangancin barin sa ya hadu da Aminatu ba, wannan Alk’awari ne tayi wa kanta, tunanin yadda akayi ma har Aminatu tazo nan ɗin, ayi sanin ta bata da wasu data sani a garin na Kano, sai gashi ta hadu da ita a lokacin da haduwar tasu tamkar yankewar farin cikin tane, kuma a unguwa daya da wadda take rayuwa a yanzu, shin dama tasan inda Dadahn take zaune ne ko kuwa co-incidense ne? Amma ta yaya? Idan har ta sani ba zata nemi ta kawo ta ba ai, toh amma? Kanta ya cunkushe ta rasa kalar tunanin da zata saka.
Koma dai menene, ba zata taba barin ta ba, ko da kuwa hakan na nufin tonuwar asirin dake rufe shekaru masu yawa ne!
★★★
Riga ce karama da dogon wando a jikinsa ya dora doguwar Jacket a sama, kansa ruf da woody cap sai bakin glass me matukar duhu daya rufe ilahirin kwayar idon sa, tun sanda abin ya faru yake cikin garin na Lagos, bai taka ko nan da chan ba sai a yau da zai bar k’asar, bolt ya kira suka zo har gaban hotel din daya sauka ya fito suka dauki hanyar filin jirgi.
Sai da ya daidai ta a cikin jirgin sannan ya ciro wayar sa ya kunna, sakonni suka fara shigowa, sai daya tabbatar sun gama shigowa tsaf,sannan ya saka wayar a airplane mode ya shiga duba sakonnin.
Daga na Daddy, Mummy, Ja’afar, Amal sai Dadah ne kowanne da abinda yake cewa, kai tsaye ya goge dukka baya son jin komai daga gare su, idan ba so suke su k’arasa shi ba, dan a yadda yake jin zuciyar sa yasan tabbas ba daidai take ba.
Gyara kujerar sa yayi sosai ya kwanta, sakonnin su kadai sun sashi ya tuna da komai. Zuciyar sa ba zata taba daukar cin amana daga mutane uku ba, Ja’afar, Amal da Dadah! Sune mutanen da ya yarda dasu fiye da kowa a duniya, fiye da iyayen da suka kawo shi duniya. Amma ta yaya hakan ta kasance? A lokacin daya gane akwai sa hannun Amal bai shiga tashin hankali ba kamar sanda take sanar masa da komai, Dadah! Why? Ya kasa gasgata hakan, gashi ya gaza samun hujjar da zata kare daya daga cikin su, shiyasa ya gaza hakuri, ya kasa juriya, ya bar su, bari na har abadah, duk kuwa da yana sa ran haduwa da Aminatu komai daren dadewa, sai dai akwai lokaci, kafin sannan, yana fatan Allah ya bashi aron rai da lafiyar da zai iya fuskantar ta, ya kuma nuna masa gaskiyar komai.
A hankali sanda jirgin su ya lula sama sosai ya furta!