DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sai wata ranah!”

★★★★★
Kullum idan na dawo daga makaranta sai nabi hanyar ko zan sake ganin ta, sai dai ko mai kama da ita ban sake haduwa da ba, tun ina saka rai har na hakura na cire na barwa Allah komai na rungumi karatu na, duk bayan sati biyu ake kawo mana balance, da su nake amfani wajen hidimar makaranta ta da abinda ba za’a rasa ba, tun Anas na fada har ya daina ya zuba min ido, daidai gwargwado yana kokarin sa a kaina duk da hakan, tun da mafiya yawancin lokuta shine yake ajiye ni a makaranta,bana cin komai har naje na dawo shiyasa ba wani kudi nake kashewa ba, nidai burina nayi karatun na taimaki kaina da yata.
  Tun bayan fara zuwa na makaranta haduwar mu wajen bakwai da Kamal d’an gayu, duk sanda ya ganni sai yayi kokarin min magana a haka har na saki jiki dashi muke gaisawa, anan na gane course din da yake business adminstration. Na lura kwarai ba karamin dan masu kudi bane duba da yadda mutane keyi masa a duk lokacin da suka ganshi, bashi da girman kai ko kadan sai dai dan gayu ne na ajin farko, kullum cikin sabuwar shiga yake komai masa abin kallo ne tun daga kayan sawar sa har zuwa takalman da yake sawa.
A hankali sabo ya shiga tsakanin mu, har mu kan zauna muyi hira duk da bata fita tsawo ba, kullum maganar sa guda daya ce Kakar sa, ko da zaman mintuna biyu kayi dashi zaka tabbatar da irin shakuwar da ke tsakanin su, tabara da tsantsar gata take nuna masa fiye da tunanin mai tunani.
A off-campus yake zaune, gida guda ne yake zaune a cikin sa, duk da ba karamin takura yayi ba a yadda ya saba, amma hakan yake zaune ala dole bisa tursasawa mahaifan sa, duk weekend a gida yake yi, sai Monday da safe yake dawowa wani lokacin ma sai Tuesday, bashi da matsalar komai duk abinda yake so shi yake yi.

Ina ta sauri zan fita daga makarantar ganin yau har la’asar ta taho ban isa gida ba, mota ce ta tsaya a gabana,na daga ido na dubeshi, daman nasan sai shi, fitowa yayi ya tako har wajen da nake, ina sanye da dogon Hijabi maroon har k’asa, sai jakata dake makale jikin sangalalin hannu na.

“Gida kikayi ne irin wannan sauri Meena?”

“Wallahi yau na dade, shiyasa nake ta sauri.”

“Lemme drop you mana idan ba damuwa.”

“A ah Ina, bashi na samu bus ta fita dani, see you.”

Nayi gaba ina nufar wajen da cincirindon mutane suka kowa na jiran abin hawa, dage kafadar sa yayi ya jingina jikin motar sa yana kallon mu, mota daya ce tazo, aka hau rububin hawa, kasa shiga nayi ina kallo aka cika ta, na sake matsawa gaba. Tsawon lokaci muka dauka shiru babu alamar zuwan wata motar, gashi ranar kudi na kenan, idan nace zan fita titi na hau normal abin hawa ba zai ishe ni ba, waigawa nayi gefe na hange shi still yana inda na barshi, muna hada ido ya saka dariya yana turo bakin sa alamar gwalo, da sauri na dauke kaina na yi gaba ina sauri ganin wata motar ta tawo, ita dinma hakan ce ta kasance, ina kallo aka gama shigewa aka barni, dafe kaina nayi dake ciwo na sake kallon sa, gani nayi ya fada motar sa ya bata wuta, yazo ya wuce ni, duk sai naji babu dadi, na hau takawa a kafa, ga yunwa gashi rashin nawa Iman abincin ta da banyi ba yasa duk sun cika sosai har na fara jin zazzaɓi na neman rufeni.
Tafiya nayi mai nisa kafin na isa gate ina yi ina haki, a wajen gate din na hangi motar sa a fake a gafen titi, an bud’e kofar mai zaman banza daidai inda zan wuce, har zan dauke kaina muryar sa ta iso min tun kafin na karasa

“Miss… da kin cire komai kinzo na ajiye ki, after all ba cinye ki zan ba, idan ma na cinye ki, za’a iya kamani ai tunda nasan za’a ce an ganni tare dake last.”

Bani da zabi, ila na shigan, a hankali na ja kafafuwana na zauna ina cin magani, dariya ya sa ya ja muka tafi yana yan kananan wake-waken sa da harshen turanci.
Hanya na dinga nuna masa har muka isa, sosa kansa yayi yana kallon unguwar,

“Kinga fa akwai gidan da Daddy yaso na zauna anan unguwar naki, babu nisa daga gidan ku.”

“Kafi so ka zauna Off-k kaci karanka ba babbaka ko?”

“No ban saba squatting bane a rayuwa ta, kinga ba zan fara yanzu da girma na ba.”

“Yayi, nagode sosai, sai Monday idan Allah ya kaimu.”

Nace ina balle murfin motar. Daga min hannu yayi ya bar unguwar, na juya da nufin shiga gida, gabana ya fadi ganin shi a tsaye yau ma kamar ranar, ya harde hannayen sa a kirjin sa, fuskar nan tasa kamar wuta. Dakewa nayi naje zan wuce ta kusa dashi, hannun sa ya sauka a cikin hannu na, da wani irin karfi yasa ya fizgoni, ya tura ni cikin gidan, kamar zan fadi nayi saurin tsayawa a kafata fuska ta dauke da madaukakin mamaki.

Da hannu ya nuna ni, cikin tsananin bacin rai ya soma magana

“Baki isa ba wallahi,kinyi kadan kina kawo mana samari kofar gidan, samarin ma na jami’a, kanana yara wanda basu mallaki hankalin kansu ba, uban me wannan dan yaron zai baki, shiyasa kika yi zaman ki a makarantar bayan yau da wuri kuke gama lecture ko?”

“Ban gane ba.” Nace ina matsawa baya ganin yadda yake matso ni

“Dama ba zaki gane ba,haka zaki ce kullum akayi miki magana, U act as if baki san me mutum yake ciki ba…”

Dukan kirjin sa yayi da hannun sa biyu

“Can’t you see how much I love you? Nace baki gane ba? Ke makauniya ce? Baki da ido? Ko baki da wayo? Ba zan dauka ba, ke tawa ce, mine and mine alone! Kin gane? Get it straight to your filthy head, ni zan aureki saboda haka bazan dauki ganin ki da kowanne kazami ba.”

Daya bayan daya na hau kokarin fahimtar maganganun sa, kamar ya zare haka ya cigaba da magana yana sake nufo ni, yaki bari na sam na gama digesting kalaman nasa, wasu yake kara min akan wasu, a bayan mu muka ji salati, muka juya da sauri gaba daya

“Na shiga uku,Anas mai zan gani? Tsintasshiyar magen zaka aura? Innalillah wa inna ilaihi raji’un, abinda nake gudu ya faru.”

Rano                  DG

                   26

BARKA DA SALLAH!

       
★★★
Asalin su shine jihar ta Katsina, tun yarinta shakuwar su babba ce tunda daya baya iya komai ba tare da daya ba, sun shaku matuka har zuwa girman su babu abinda ya chanja na daga yadda suke.
   Asalin amintar su ta fara ne daga kusancin iyayen su maza, kar kawo yanzu.
   Kabir Aliyu Shagari kenan da aminin sa Marwan Muhammad Dikko. Duk inda kake neman shakuwa da yarda da juna toh sun hada, tare suke komai tun daga matakin farko na rayuwa har zuwa shigar su jami’a.
  Tafiyar su jami’a bisa mabanbantan ra’ayi be sa sun chanja ba, Kabir ya zabi bangaren aiki soji inda ya tafi makarantar horar wa dake garin na Kaduna, inda Marwan ya zabi tafiya jami’ar ta Ahmadu Bello dake garin na Zaria. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin nasara.
   Kasancewar shi Marwan d’a daya tilo wajen iyayen sa yasa shi kara shakuwa sosai da aminin nasa, saboda babu wani wa ko k’ani da zasuyi shawara sosai. Masu arziki ne na gaske, abun kwatance a kaf fadin yankin su .
    Kabir su uku ne wajen iyayen su duk maza, shi ne na farko sai kannen sa Adamu da Ahmadu. Mahaifiyar su da suke kira da Dadah mace ce mai kirki da sanin ya kamata. Tana da abokiyar zama guda daya sai dai Allah bai sa ta haihu a gidan ba har zuwa lokacin da maigidan ya rasu ta tattara ta kama gaban ta, duk da hakan har yanzu suna gaisawa da juna.
  Bayan rasuwar mahaifin su komai ya dawo hannun Kabir, shine ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kula da abinda mahaifin su ya bar musu, ya kuma cigaba da kula da yan uwan sa.
  Cikin hukuncin Allah komai ya dinga tafiya musu cikin nasara da daukaka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button