DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL


A gaggauce ya shirya yana yi yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, karo na shida kenan da yake faman kiran sa akan an fara baya wajen, cikin sa’a ya gama shirya wa ya dauki hanyar jami’ar.
  Yana isa yayi saurin dukawa kansa a k’asa yace

“Tuba nake ranka ya dade.”

  Harara ya sakar masa, ya bigi saman kafadar sa cikin jin haushi yace

“Allah ka iya jirga mutane, da ban azalzala ka ba da shikenan sai ayi babu kai.”

“I’m deeply sorry oga.”

Ya sara masa yana kokarin cire hular kansa, da wani irin shock ya tsaya yana kallon su, yan mata ne su biyu cikin shiga iri d’aya sai dai d’aya ta girmi daya duba da yanayin shekarun su

“Kb!”

Ya kira shi da d’an ƙarfi ganin yadda ya bada attention d’insa gaba daya wajen su.

“Man nayi farin zuwa, wallahi naganta, no wonder naji sai na tsaya na tsara kwalliya ta ashe yau zan hadu da future d’ina.”

Dariya Marwan yasa ya kama hannun sa.

“In dai Abidah ce kamar yadda naji ana fada ba sauraran ka zatayi ba, amma wacce kake so cikin su? Karamar ko babbar?”

“Babbar, itace Abidah?”

“Wai, toh ka gwada sa’ar ka, nidai babu ruwana idan ta wulakanta ka.”

Gyara wa ya shiga yi sosai

“Aiko zan gwada, nasan nafi karfin wulakanci wallahi.”

“Owk best of luck, bari na matsa ciki kafin a fara, kuma wallahi ka zama kusa dan zan neme ka.”

“An gama my guy.”

A chan nesa ya hange su, suna tsaye gefe suna kallon yadda ake gabatar da taron convacation ɗin, magana suke kasa kasa da juna, kai tsaye ya isa wajen cikin gwarewa ya shiga introducing kansa, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dan murmushi tayi kawai bata ce komai ba, karamar ce ta amsa masa suka shiga hira kamar sun saba, da haka ya hilace su har ta saki jiki dashi, cikin dan kankanin lokaci suka saba, ta ware sosai tana amsa masa,tun daga lokacin shikenan suka saba, soyayya ta shiga tsakanin su.


Bayan Aure!

Part uku ne sai na Dadah dake gefe, baya zama saboda yanayin aikin sa, hakan yasa ka shakuwa mai karfi shakanin ta da Adam da Aliyu, bata da matsalar komai duk sanda yazo yakan yi two weeks sai kuma wani dogon lokacin. Kasancewar Dadah mace wadda tasan ya kamata yasa suke zaune lafiya kowa yana mutunta kowa.
A lokacin ne Marwan yayi aure ya auri wata yar zaria, basu wani dade ba auren ya mutu tun da ya ji tana waya akan yadda take so dukiyar sa ta dawo hannun ta, ya tattara ya watsar da duk wata maganar aure ya cigaba da zaman sa haka nan.
  Rayuwar ahalin Dadah rayuwa ce mai dadi da kaunar juna.
Shekaru biyar da auren Kabir da  Abidah Allah ya azurta su da samun d’a namiji, wanda take Dadah ta zaba masa sunan mahaifin ta Umar Farouk, dukkan soyayyar da d’a yake nema wajen mahaifin sa Uncle Aliyu kamar yadda Abidah take ce masa ya karbe ta, shine yake masa komai na uba saboda rashin zaman mahaifin sa.
   A lokacin Marwan ya sake auren har mata biyu suma duk abu daya ne ke kawo su data farkon, gashi duk cikin su babu wadda ta haihu sai dai suzo su tafi. 
  Kanwar Abidah mai suna Safiyya ta gama karatun ta, ashe dama soyayya suke da Aliyun babu wanda ya sani, hakan ya kara faranta ma Dadah dan ta gamsu da Abidah saboda haka zata so su kara hada zuri’a.
   Rikon Farouk ya koma kachokam wajen Aliyu da Safiyya bayan auren, su ka cigaba da zaman lafiyar su cikin kauna da kwanciyar hankali.
  


Cikin kankanin lokaci dukiyar Marwan Muhammad Dikko ta bunkasa. Samun aikin sa a PTDF ya sa dole suka tattara suka koma garin na Abuja, kasuwanci ya cigaba yana juya dukiyar su, daga shi sai mahaifiyar sa har lokacin baya maganar aure,  babu yadda aminin sa bai masa ba amma sam yaki maganar auren da uzurin har lokacin bai samu wadda tayi masa ba.
   Gini ya fara a hade da juna guda biyu, komai iri daya sai dan banbancin girma, abun da akwai kudi ba’a wani dau lokaci ba ya kammala. Yanayin aikin Kabir yasa har aka gama ginin be san komai akai ba, mukullin gida kawai ya damka masa a matsayin kyauta ya zauna har karshen rayuwar sa. Ba karamin murna yayi ba, saboda bai taba zato ko tsammani ba, nan suka hau shirin tariya suka tattara komai suka koma garin na Abuja har Dadah, duk da Safiyya da Aliyu basu ji dadin tafiyar tasu ba, amma sun san hakan wani cigaba ne, dole suka bisu da fatan alkhairi suka rabu cike da kewar Farouk da ya zama tamkar d’an su.
 


Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun faru, ciki har da haihuwa da Allah ya azurta Aliyu da Safiyya ta d’a namiji, suka sa masa suna Ja’afar, lokacin Farouk na da shekara biyar a duniya. Har lokacin Alhaji Marwan Dikko bai yi aure ba, kuma bashi da niyyar yi, takanas Hajiya Turai ta aika aka kira mata Kabir (Daddy) ta sasu a gaba da fadan lallai ya matsa masa ya fitar da mata, dan zaman shi haka ya ishe ta babu da balle jika, hakuri suka hada baki suka bata, suna fitowa Kabir ya sake dora masa da nasa fadan, haka dai yayi masa alƙawarin zai yi kwanan nan babu jimawa.


Bakaken Ranaku

Yanayin aikin soja da rashin lokacin su ya kara saka shakuwa mai karfi tsakanin Adam da Abidah, a bangaren ta yake zama har dare ayi kallo ayi hira da wasa da dariya, wani lokacin ma har sai ta tafi ta kwanta ta barshi idan ya gama ya rufe mata kofa.
  
Watarana da daddare bayan ta tafi daki ta kwanta sai taji tana buƙatar dauko ruwa, kanta tsaye ta nufo falon, tun daga nesa take jin alamun magana a cikin fushi, d’an dakatawa tayi tana sauraron shi,

“Kinsan Allah, kije chan ki nemi uban da yayi miki ciki, dan kin rainan wayo shine zaki kwaso cikin ki kizo ki na na min.”

“Eh nasan wannan amma sau daya shikenan sai kice ni, tab ai wallahi uban da yayi miki kije can ki neme shi, dan tsabar iskanci sai da kike gab da haihuwa sannan zaki kirani kina min wani banzan zance, karki kara kirana wallahi kinsan ni kinsan me zan iya.”

Tsaki yaja da karfi ya kashe wayar yana bugata saman kujera, rai a bace Abidah ta ƙaraso falon

“Anty!” Ya fada cikin alamun tsoro tsoron ko taji, bata amsa ba sai ma zama da tayi kujerar dake kallon sa tana tallafe cikin ta dake wata takwas.

“Adam, me naji kana cewa?”

Ta watso masa tambayar tana kallon yanayin sa. Zai yi magana tayi saurin daga masa hannu

“Ciki kayi ma wata Adam?”

Juyar da kansa yayi gefe a ciki ciki yace

“Tun da kin riga kinji, bani da damar boye miki, mistake ne ba wai hali na bane.”

A cikin tsananin mamaki take kallon sa, bata taɓa tunanin Adam da aikata abu makamancin hakan ba, fada ta hau yi masa ta inda take shiga bata nan take fita ba, tayi masa tas kuma tace tabbbas dole yan uwan sa da mahaifiyar sa su sani, da sauri ya zamo kasa ya haɗa hannun sa ya hau yi mata magiya, bata saurare shi ba tayi wucewar ta daki ta rufe da key.

Tsawon kwanaki uku yana mata ziryar ta rufa masa asiri, kin bashi fuska tayi, ta daina sakar masa fuska ko kadan, tunanin yadda zata sanar wa Dadah take, bata son abinda zai daga wa matar hankali, haka tayi ta fama da abin a ranta ta rasa wanda zata faɗa wa.
  Kwatsam sai ga Safiyya da Aliyu sun zo, hakan ba karamin dad’i yayi mata ba, bayan sun huta ne ta samu damar sanar musu abinda yake faruwa, sosai Aliyu ya dau zafi ya kirashi ya ci masa mutunci sannan ya ce dole ne Dadah ta sani sannan dole Kabir ma ya sani, shawarar yadda zasu fara fad’a wa ita Dadah sukayi musamman suka je har dakin ta, tare da Adam ɗin yana sunkuyar da kansa kamar munafiki, tun da taga yadda suke nuku-nuku ta gane akwai matsala, kafin su samu damar fada mata ta jefe su da tambayar,ala dole Aliyu ya daure ya sanar da ita, iya kar rudewa ta rude, bata san sanda ta rufe shi da duka ba, tana yi tana kukan ya cuce ta, da kyar suka lallaba ta, ta yi shiru suka shiga tunanin yadda za’a bullo wa al’amarin tun da dai ya tabbatar musu ba halin yarinyar bane shine ya yaudara ta da dadin bakin zai aure ta ita kuma ta amince masa.
  Tunanin zuwan Daddy kowa ya shiga yi dan yasan ba karamin artabu za’a sha dashi ba, ranar da ya kira kuwa yace yana hanya duk jikin su a sanyaye, haka ya zo ya tarar dasu sukuku kamar wanda akayi ma mutuwa.
  Wanka yayi ya fara hutawa kafin ya nufi bangaren Dadah, bayan sun gaisa ne suna d’an taba hira Alhaji Marwan ya shigo, yana zama aka shiga yin sallama a ɓangaren, Dadah ce ta yunkura ta leko, mata ne guda biyu cikin yanayin tashin hankali da rashin nutsuwa, hannun su tabi da kallo a take tasha jinin jikin ta jiri-jiri ne ya soma daukar ta, tayi saurin dafe bangon tana yi musu iso ciki, a d’arare suka bita, falon suka koma suka samu waje suka zauna. Hakan yasa suka katse hirar da suke suna kokarin mik’ewa Dadah ta dakatar dasu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button