DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ku tsaya ayi komai a gaban ku, dan kuma ta shafe ku.”
Komawa sukayi suka zauna da tunanin abinda yasa tace hakan,
“Sannun ku da zuwa.”
Tace tana mika hannu dan karbar jaririyar hannun su.
“Gata nan, tabbas bamuyi tunanin ganin ku haka nan ba, ranmu a bace muka tawo sai dai a yadda kika yi mana yasa muka ji nauyi da kunya, gata nan, yar ku ce dan dukkan bincike ya nuna yaron gidan nan ne yayi mata cikin, sai dai ita Allah yayi mata rasuwa wajen haihuwar shiyasa ma muka jinkirta kawo ta har zuwa sanda akayi sadakar bakwai.”
“Allahu Akbar, Allah ya jikan ta, Allah ya raya mana, kuyi hakuri dan Allah, d’a ne ka haife shi, amma baka haifi halin shi ba, kuyi hakuri kuyi hakuri.”
“Me ya faru Dadah.?”
“Kira min Adamu a waya, yazo nan bangaren sai kuji komai.”
Daga waya yayi ya kirashi, ya ajiye yana jin zuciyar sa kamar zata faso kirjin sa. Kan sa tsaye ya shigo falon, da kallo duk suka raka shi har ya samu waje ya zauna yana kallon matan. Tashi Dadah tayi ta mika masa jaririyar tana buɗe rufin da akayi mata da abin daukar yara
“Ko da ace zaka ƙaryata, ka dube ta, babu abu daya data bari naka sanda kana karami, babu abu ɗaya, kaga ikon Allah ko? Toh haka rayuwa take, duk wanda yayi da kyau zai gani.”
Sai ta juya wajen su Daddy
“Gashi nan ya ce aka kawo muku, sai yayi muku bayanin yadda akayi aka haihu a ragaya, sai dai wannan tsantsar kamar ta isa ta tabbatar da komai.”
“Ku kuma dan Allah kuyi hakuri akan abinda ya faru, bani da bakin da zan iya baku hakurin rashin kyautawar da akayi wa yarku, sanadiyar da har ta rasa ranta, Allah ya baku hakurin rashin ta.”
Mik’ewa sukayi a tare, sukayi sallama suka tafi. Suna fita Dadah ta karbi jaririyar tayi dakin ta tana jin kamar ta yi kuka, yau itace zata goya yar da ba ta hanyar sunna aka same ta ba, sai dai dole laifin iyayen ba zai shafe ta ba, zatayi kokarin ganin hakan bai shafi rayuwar ta nan gaba ba.
***Wata irin shaka Daddy ya kai masa, ya shiga bugun sa da dukkan karfin sa, da kyar Alhaji Marwan ya kwace shi dan tuni ya sauya masa halitta, da rarrafe ya fita daga falon saboda tsabar yadda ya daku.
Saman kujera ya fada yana dafe kansa, idan akwai abinda ya tsana take kyama a rayuwar sa ya kasance zina, abu ne da duk wanda zai iya aikatata to tabbas bashi da sauran mutunci a idon sa.
Idan ya tuno yar jaririyar sai yaji kansa ya sake sarawa, komai daren dadewa dole ne gaskia ta fito. Ya zatayi da abinda bata da masaniyar komai akai? Shigowar matar dake dan taimakawa Abidah da aiki a guje ya maida hankalin su gareta
“Alhaji ina tunanin haihuwar tazo.”
A kid’ime suka bi bayan ta, aka nufi asibiti da ita, lokacin ta riga ta gama galabaita sosai, har bata gane wanda ke kanta sosai. Sai data dau tsawon lokaci dan har an soma shirye-shirye shiga da ita theatre ta haihu sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Kwanan ta biyu a asibitin aka sallame ta.
Bangaren Abidah Dadah ta nufa dauke da jaririyar a hannun ta, Abidah na zaune tana shan tea a kofi duk jikin ta babu dadi aka shigo, ajiye kofin tayi tana kokarin mik’ewa ta dakatar da ita
“Zauna dan Allah. Ke da ba lafiya ba.”
“Ai da sauki Dadah, ashe sun zo ranar.” Tace tana mai kallon hannun nata
“Hmmm sun kawo ta gata nan, gashi sam taki karbar madara wallahi, kwana biyun nan kuka kawai take sai dai idan taji uwar bari ta karba tasha kadan, na rasa yadda zan.”
“Allah sarki.”
Tace tana kallon yarinyar, da sauri Farouk ya taso yana leka fuskar ta, daidai lokacin ta saka kuka sosai, da sauri ya kalli Abidah
“Mummy kuka take, sabuwar bbyn da kika haifa mana ce?”
Daga masa kai tayi, ta mika hannu ta karɓe ta daga hannun Dadah ta soma jijjigen ta.
“Bari na dauko madarar a sake gwada mata, kukan ya soma yawa wallahi.”
“Mummy ya sunan ta? Itama kanwata ce kamar Ja’afar?”
“Kanwar ka ce Farouk.”
“Yess!” Yace yana murna, yana kama dan karamin hannun ta, Dadah ce ta dawo dauke da madarar ta bata ta koma wajen bakin da tayi, karbar ta tayi suka shiga daki, ta sake hada mata madarar ta bata, kadan tasha ta yi bacci, shiru tayi tana tunanin taimakon yar jaririyar da bata san abinda duniyar ke ciki ba. Ba tare da shawara da kowa ba ta yanke abinda take ganin zai taimaka mata ya kuma farantawa Dadah.
***: *DG*
27
Adam duk ya fita hayyacin sa, babu wanda ke bashi fuska a gidan, zaman daki ne ya zama abin yin sa tunda idan ma ya fito babu wanda ke kulashi, gefe daya yarinyar da yake mutuwar so da kauna, kwana wajen nawa kenan yana sintirin kiran ta a waya amma bata daga wa, daga karshe ma sai tayi blocking kiran sa baki daya, abin yayi masa zafi ssoai, dole ya shirya ya tafi gidan su, tun da ya hango motar yaji jikin sa ya soma rawa, ganin an bude gate din gidan yasa shi labewa a baya, itace tayi kyau ainun, cikin shigar ta kamar ko yaushe, ta nufi motar. Motar Alhaji Marwan ce, ji yayi numfashin sa ya soma ja da kyar, be kara shiga tashin hankali ba sai daya ga ya zuro kafafun sa ya fito, shi din ne kowa, fuskarsa dauke da madaukakin farin ciki, yadda tayi masa jagora zuwa cikin gidan yasa gama tabbatar da komai ya kare masa. Wayar sa ya sake kira yana son sake tabbatar wa, sai dai kamar ko yaushe ne, ba zai taba iya kiran nata.
Da kyar ya kai kansa gida, zuciyar sa na zafi, zafi irin na rabuwa da masoyin daka kwallafa rai akan sa, ka dora dukkan buri akan sa, shin me hakan ke nufi? Ta san abinda ya faru dashi ne yasa ta juya masa baya? Ko kuwa dai Alhaji Marwn…
Tuni zuciyar sa ta hau tururi, yaji kamar ana zare masa sauran tausayin da ya rage masa a zuciyar sa, sai da ya zama babu digo ko sauran tausayin kowa a ransa, a take ya yanke wa kansa shawarar abinda yake ganin shine daidai.
Zagayen dakin yake yana dan shafa saman kansa, tunanin sa ya tsaya tsak daga lokacin da ya tuna tabbas Abidah ta shayar da Amal nono, eh duk da ba wai ta shayar da ita bane har zuwa sanda ta isa yaye, amma tabbbas ta zama mahaifiyar ta ta shayarwa kamar yadda musulunci yace,ya akayi dukka suka manta da wannan? Duk da a lokacin ya hane ta ya gargade ta akan kadda ta shayar da ita bayan ya gano take taken ta, sai dai a yanzu yana hasaso hakan a matsayin wani ɓangare da yake bukatar dubawa. Da sauri ya jawo wayar sa, number ta da har lokacin ke ajiye a wayar sa, har ya danna kiran sai kuma yayi saurin katsewa, akwai sauran abubuwan da yake son ganowa, dan haka dole ya gama bitar komai daki-daki kafin ya kira ta.
***Babu bata lokaci aka shiga hidimar bikin Alhaji Marwan Dikko, zuwa lokacin Adam ya zama kamar wani tsohon mahaukaci, komai ya tsaya masa, babu kuma wanda ke bin takansa, kowa sabgar gaban sa yake akan abinda yake ganin wani kuskure ne da ya aikata da ya kamata su sassauta masa, idan yaje dakin Dadah bata wani sauraron sa, balle kuma Abidah da taso tafi kowa daukar zafi ita da mijin ta Uncle Aliyu da Safiyya na tayasu, sai yaji duk ya sake tsangwamar kansa.
Haka akayi biki aka watse aka kawo amarya, ranar bai iya baccin kirki ba, atleast yaso yaji ta bakin ta akan dalilin daya sa tayi masa hakan, sai dai duk cikin su babu wanda yake da niyyar sauraron sa. Hakan kuwa ya taimaka wajen dasa mummunar kiyayyar su a zuciyar sa. Zuciya bata da kashi, tuni ta shiga ingiza shi, da sunan daukar fansa wanda yake ganin haka ne kawai mafita.