DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ka shiga taitayin ka, na wuce yadda kake tunani wallahi, zan iya yin komai.”

Dukan kirjin sa yayi ya tura shi baya,

“Babu abinda ka isa kayi sai abinda Allah ya ƙaddara akaina.”

Yana kaiwa nan ya juya ya bar masa dakin.

Bangaren Dadah yayi yana riƙe da hannun yaran, tana zaune ta rasa ina zata saka kanta, da sauri ta dago tana ganin shine ta mike

“Aliyu, dan Allah karka ce zakayi bincike akan abinda ya faru yanzu akan yayar matar ka, karka ce zaka tsaurara bincike na roke ka.”

Durkusawa yayi a k’asa ya kaskantar da kansa yace

“Ke mahaifiya tace, idan har kike bani umarni dole nabi ko da hakan zai zamar min matsala, wajibi ne nayi idan har bai sabawa Allah ba, sai dai a wannan karon zan nemi afuwar ki tun kafin àbinda zai kasance ya kasance, zan tsaya wa Anty Abidah na bi mata hakkin ta, ba zan hakura ba har sai sanda gaskiya tayi halin ta. Ki yafe min.”

Kuka ta saka ta shiga yi mishi magiya ya bar komai kar ya tsaiwata bincike, babu alamun zai saurare ta, tashi yayi da nufin barin dakin tayi saurin rike shi tana kuka sosai.

Yana tsaye kyam a bakin kofar dakin ya harde hannun sa a saman kirjin sa, cikin isa da gadara yacw

“Barshi, wanda bai ji bari ba, shine zaiji hoho.”

Juyowa Aliyu yayi a fusace ya bar dakin da sauri, kukan yaran dana Dadah ya hautsina dakin, be bi ta kansu ba ya wuce uwar dakin ta, yar jaririyar sa na kwance tana jujjuya kafarta da alamun ta jima da tashi har tayi kuka ta gaji, yau ne karo na farko daya mata kallon tsaf tun ranar da aka kawo ta gidan, babu maraba tsakanin ta dashi sai ta banbancin jinsi. Shafa kanta yayi makogaron sa na kaiwa da komowa yace

“I ll come back for you one day!”


Tsawon sati kenan Daddy na rufe a bangaren sa, baya zuwa ko ina ko sallah ma a daki yake yin ta, sosai abin ya taba shi, yana ganin kiran Alhaji Marwan amma sam yaki dagawa, duk sanda ya runtse idon sa su yake gani, sun cutar da zuciyar sa, sun dasa masa wani babban al’amari da zai ta bibiyar tunanin sa.
  Tsawon satin nan babu wanda ya leko tsakanin Aliyu da Adam, yaran uku dake gaban ta su kadai take kalla taji hankalin ta ya tashi, bata taɓa fatan ko tunanin abinda zai zo ya wargatsa musu kwanciyar hankali ba cikin d’an kankanin lokaci, gaba daya gidan ya fita daga kanta bata fatan cigaba da zama cikin sa, zaman da zai cigaba da yi mata famin abinda ya faru.

Sai da Alhaji Marwan yayi da gasken gaske sannan ya samu Daddy ya fito, yayi muguwar rama da baki, fada yayi ta masa amma bai sanar dashi abinda ya faru ba, labarin yafi gaban a bada shi ba, duk kuwa da yadda suke da karfin abota amma ba zai iya ba.
   Tubure musu Dadah tayi akan lallai sai ta bar gidan, ba kuma Katsina zata koma ba, bata son duk wani abu da zai tuna mata komai, ganin ba zata amince da kokarin kwantar mata da hankalin da suke kokarin yi ba yasa suka yanke shawarar sama mata gida a Kano, wannan shine asalin komawar Dadah Kano tare da Farouk, Amal da Ja’afar.


Daddy na rurrufe ko ina na gidan dan komawa aiki Adam ya shigo, har lokacin kansa rufe yake da bandage, dauke kai Daddy yayi kamar bai ganshi ba, ya wurga masa keys din bangaren sa

“Ka duba komai naka ka kwashe ka bar min gida.”

Dage kafadar sa yayi ya tsuguna ya dau keys din, bud’e dakin yayi ya dauke abinda zai dauka ya fito,kamar yadda ya wurga masa keys din shima hakan yayi, ya gefe shi dashi cikin keta yace

“Sai watarana!”

A kusan tare suka bar gidan, sai da Daddy ya fara biya wa ta Kano ya duba Dadah, kafin ya wuce wajen aikin daya dauki lokaci mai matukar tsawo kafin ya sake waiwayar gida.
   Samun babban matsayin da yayi shi ya rage masa nauyin abubuwan da yake, ya tattara hankalin sa waje daya yayo gida, Dadah na ganin shi tasa masa kuka, kukan dake nuna tsantsar halin da take ciki, sai a sannan take sanar mishi ta mutuwar Adam din, hatsarin mota ne ya rutsa dashi daga Lagos zuwa Kano ko gawar sa ba’a kawo ba.
  Babban tashin hankalin ta bai wuce daina ji daga Aliyu da Safiyya ba, tun bayan rasuwar, taje gidan yafi a kirga amma magana daya take samu daga makotansu shine sun yi tafiya.

Takanas Daddy yaje da kansa har wajen aikin Aliyun, sai a sannan ne ma yake jin labarin ai ya bar aiki tun da jimawa, abun ya matukar daure masa kai, haka ya dawo a sanyaye gida ya sanar wa Dadah, wadda hakan ba karamin sake gigitata yayi ba,tun daga nan basu sake k’ara ji daga gare su ba, a hankali suka manta, kamar an cire musu su da abinda ya shafe su daga ƙwaƙwalwar su, babu wani daga cikin su daya sake yin maganar sa har kawo yanzu!


Sake shiri yayi, ya fito a cikakken mutum mai cikar zati da haiba, sai dai yanayin fuskar sa kadai zata tabbatar maka da ba daidai yake jin jikin sa ba, bayan mota ya fada ya d’an kishingida kadan yana lumshe idon shi, tabbas yana bukatar ji daga gareta, yana so yaji komai daga bakin ta ko da kuwa ba zata saurare shi ba zai gwada sa’ar sa.
Su biyu ne kaɗai daga shi sai driver sa, yau baya jin zai iya yin wannan tafiyar da masu kula dashi, bayan haka ma baya bukatar hayaniya yana so yaje mata a Kabir ɗin sa, Kabir ɗin data sani shekarun baya ba na yanzu ba..

“Ina zamu je ranka ya dade?”

“Kaduna.” Ya amsa mishi a gajarce yana sake mikewa sosai.


Duk nauyin dake cunkushe a zuciyar sa yau yayi sauki har yana jin bukatar fara aiwatar da abinda ya kawo shi. Shigar manyan kaya yayi kamar ba a k’asar masu jajayen kunne ba, ya dora hula ya fito a cikakken bahaushe bakar fata, kai tsaye inda sukayi zasu hadu ya nufa da taimakon address din daya bashi.

Daga d’an nesa ya hango shi, tabbas shine mutumin nan na ranar nan, ya akayi suka sake haduwa? Daga kafar shi yayi cikin sauri ya nufe shi, daf da zai isa gareshi yaga ya bude wata mota dake ajiye wajen ya shiga, bai iya ganin fuskar sa sosai ba sai rabi kamar wanchan lokacin, kamar an dasa shi a wajen haka ya tsaya yana kallon motar har ta bar wajen, jan ƙafarsa yayi zuwa shagon yana kokarin ganin ya yakice shi daga zuciyar sa, ya rasa dalilin ma da yasa yake jin wani abu game da mutumin. Ganin zai bata wa kansa lokaci yasa yayi saurin shigewa ciki yana duba agogon hannun sa, yasan baturen mutam da ka’ida, baya so ka saba masa alkawari.
Tambaya yayi aka nuna masa inda zai same shi. Cikin aiki ya tarar dashi kacha-kacha, yana ganin shi yayi dariya, yana tura masa takardun gaban sa, da mamaki Farouk ya kalle shi amma kafin yayi magana ya riga shi

“No time to waste.”

Gid’a kansa yayi a hankali ya furta

“Nima bani da lokacin batawar ai, I’m here for it”

Aikin ya shiga nuna masa,da yadda yake so komai ya kasance, babu wani bata lokaci ya fuskanci abubuwa da yawa sai dan abin da baza’a rasa ba wanda sai a hankali dama.
Ranar a gajiye likis ya koma gida cike da farin cikin fara aikin da yayi da shugaban shagon wanda dalilin social media suka hadu tun da dadewa, sai gashi yayi masa rana a lokacin da bai taba tunani ba.
Wanka kawai ya iya yi yasha tea ya kwanta dan sosai yake jin bacci, yana kwanciya kuwa baccin ya dauke shi wanda rabon da yayi irin sa ba zai iya tunawa ba. Gashi dama duk sanda yayi yunkurin baccin sai tunanin ta ya shigo masa, daga nan sai yaji sam baccin ya fita daga kansa, daga nan sai ya dasa sabon tunani har zuwa sanda baccin zai dauke shi ta karfin gaske ba tare da ya shirya ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button