DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

*** AMINATU
Na cigaba da zuwa makaranta da taimakon Allah dana Baba Altine data zama wata babbar bangare na sabuwar rayuwa ta.
Bani da matsalar komai gefe ga Kamal daya zama abokin shawara ta. Ban yi watsi da duk abinda Anas ya ce min ba ina matukar kokari wajen ganin na kare mutunci na.
Lokuta da dama nakan tuna Baba, Inna da Karime, Yalwati da sauran mutanen da suka fi kowa kusanci dani a da amma babu ko daya cikin su yanzu a rayuwa ta, hakan ba karamin sani yake na kara tuna wacece ni ba, mara asali da tushe abar kyama ga kowa.
DG
29
★★★★
Dukkan abubuwan bukatuwa na makaranta ta Kamal ya dauke min shi, tun ina fada har na kyale shi na zuba masa ido, ranar ina tsaka da duba wani handout ya iske ni wajen da muka saba haduwa, a dan gefe ya zauna yana leken cikin handout din
“Kaga yan allazi boko.”
Yace yana dariya, harara na sakar masa ina janye handout din.
“Wai dan Allah yaushe zaki kawo min Iman ne, I’m dying to see her kinsan abinki da hanta da jini, daga zuwa sau daya shikenan nasan ma ta kara wayo.”
“Sai dai ka shirya kaje da kanka, ni bazan iya dauko ta makaranta ba,dame zanji?”
“Toh ai ni hakan ma zaifi min farin ciki, yaushe zaki gama da school?”
“Lecture daya ya rage, nan da 30min zamu shiga.”
“Shikenan ki kirani idan kin gama.”
Yace yana mik’ewa, waya ta dake cikin jakata tayi k’ara, tsayawa yayi ya harde hannu yana jiran yaga mai kiran. Ina ciro ta naga ya kwashe da dariya
“Yanzu zata nutsu kamar wani maka’ika.” Yace yana bata fuska, ban bi ta kan shi ba na kara wayar a kunne na gami da sallama. A nutse na shiga amsa masa har ya ajiye wayar, ajiyar zuciya na sauke ina duban KAMAL da shi ma nidin yake kallo
“Ya Anas ne fa.”
“Na sani, ai naga sunan, ki rage tsoro kamar zai yanka ki idan ya kira.”
“Kai ka sani, aka ce ma tsoron sa nake? Kawai ina respecting d’insa ne.”
“Daga baya kenan, ki cigaba da nuna masa tsoro, idan kika aure shi kisha wuya yarinya.”
Da sauri na ware ido ina murmushi
“Yanzu Kamal har kasan wani aure? Inyeee.”
Dariyar shima yasa yana yin gaba abin sa, sai daya dan d’ara wajen kafin ya ce
“Kinci sa’a ke sirikace zaki bani Iman amma da kinji magana gabza gabza wallahi.”
Murmushi kawai nayi ban kuma ce masa uffan ba na hau tattare kayan karatu na ganin lokacin shiga ajin ma ya kusa.
A gaban Hall d’in na tarar dashi tsaye yana jira na, ni har na manta ma munyi maganar zamu tafi tare, babu yadda na iya haka na bishi muka dau hanya, sai dai kamar yadda ya san gidan a dah yau sai yaga mun chanja akalar tafiyar tamu, kallo na yayi yace
“Kun chanja gida ne?”
“Eh.” Na amsa mishi a takaice, muna zuwa na shiga na sanar wa Baba Altine zai shigo, cikin daki ta koma na rik’e hannun Iman muka fito, da mamaki yake kallon mu, sai kuma ya ƙaraso ya daga ta sama yana dariya sosai
“Baki da kirki Meena, haka matar tawa ta girma amma baki fada min ba?”
“Shigo ciki dai sarkin zance, sai muyi maganar.”
Cikin muka koma, ya zauna a kan dardumar dana shinfida masa, ruwa na dauko masa na ajiye sannan na shiga daki na ajiye jakata na sake fitowa, yana zaune yana wa Iman wasa ita kuma tana ta dariya kamar ta sanshi, Kitchen na wuce na duba, shinkafa da wake Baba tayi, sai salak da tumatir dake yanke an tsaftace shi a cikin mazubi, hadowa nayi na jera komai na kawo masa ina zama.
“Ga abincin gidan talakawa sai kasa albarka.”
“Kinci bashi wallahi.”
Murmushi kawai nayi, a gefen sa ya ajiye Iman ya bude flask din, ya dauki plate ya zuba abincin sosai ya shiga ci muna hira, sosai yaci dan banyi tunanin zai ci haka ba, ganin yadda yake d’an gayu sai na dauka a komai ma hakan ne, shiyasa Bature yace never judge a book by it’s cover, tabbas haka ne, kar kayi saurin yanke wa mutum hukunci ba tare da sanin ainihin waye shi din ba.
Kiran wayar sa akayi, da murna ya daga yana sawa a handfree
“Old Woman kinyi missing d’ina ne hala shisa kika biyo baya.”
“Sosai kuwa, sati nawa rabon dana saka ido na? Kana cewa baka son Kano sai gashi kayi luf har kana mancewa dani, ko kayi sabuwar mata ne?”
Dariya ya tuntsire da yace
“Aikuwa dai kin iya saurin gano abu, yanzu ma kin ganni wajen ta, nazo mamanta ta cika min ciki da Rice and beans me shegen dadi.”
“Da gaske kake yaron kirki?”
“In bata ku gaisa ne?”
“Eh bata naji.”
A kunne ya kara wa Iman wayar yana kunshe dariyar sa
“Oya say hi to my boring Grandma kinji baby.”
Gwaranci ta soma yi, kamar yadda ta saba duk sanda Anas ya kira a bata wayar, dariya muka hau yi gaba dayan mu har granny din dake kan waya,
“Ja’iri zaka zo har inda nake ka same ni.” Tace tana katse wayar, tallafe fuskata nayi da hannu biyu ina kallon sa
“Baka da dama kamal, Allah shirye ka.”
“Amin, naji, itama da gulmar tsiya ai maganin ta.”
Mik’ewa yayi ya mana sallama ya tafi, bayan tafiyar sa ina kokarin tattare komai na abincin ya shigo, bakin sa dauke da sallama, ido na cikin nasa nayi saurin yin kasa ina jin faduwar gaba, bai sanar dani zuwan sa ba dazu da mukayi waya, da gudu Iman ta rungume shi tana masa oyoyo, daga ta yayi ya manna ta a jikinshi har lokacin idanun sa na kaina yana yawo dasu.
“Sannu da zuwa.” Nace ina cigaba da tattare kayan, da hannu ya amsa min yana nazarin wajen zaman da kayan da nake kwashewa, sallayar na gyara masa ya zauna yana tankwashe kafar sa.
“Bako kikayi ne?”
Yace yana karanta ta, ban amsa na gaishe shi, a gajarce ya amsa daidai lokacin Baba Altine ta fito tana masa sannu da zuwa, da fara’a ya amsa mata ba kamar yadda yayi min ba, ta zauna tana tambayar su Hajiya, tashi nayi na kawo masa ruwa da ragowar abincin na wuce daki, ina jin sa ya jeho ma Baba Altine tambayar da yayi min ɗin, maimakon tace masa eh sai naji tace
“Wata kawarta ce tazo bata jima da tafiya ba ma, ko kun hadu a hanya?”
“No shikenan.”
Girgiza kai na nayi ina mamakin halin shi, kayan na sauya na fito na koma kitchen din na dora indomie dan ba karamar yunwa nake ji ba, zama na nayi a Kitchen din ba tare da na koma Falon ba, ina jiyo hirar su ya ware sosai yana wasa da Iman, wannan na daya daga cikin dalilan daya saka nake sake bashi girma, da gasken gaske yake kula damu kamar wanda muka zama masa dolen sa.
Zama na nayi bayan na gama dafa indomie na ci a Kitchen din na zuba ma Iman da Baba Altine tasu a dan flask na fitar da kwanukan na daureye sannan na koma ciki.
“Mu baza’a bamu indomie ɗin ba ne?”
“Za’a baku.” Nace ina kokarin komawa kitchen din
“Barshi sai da muka roka, dauko hijabin ki rakani unguwa.”
“Baba dauko nake kema kar mu barki ke kadai a gida.”
“A ah wallahi, shikenan kuma sai na biku godai godai dani, Aallah kiyaye sai kun dawo.”
Murmushi yayi kawai ya rike hannun Iman sukayi waje, ciki na koma na zura hijabin na fito.
A jingine jikin motar na tarar dashi, yana gani na ya bud’e min bangaren mai zaman banza, shiga nayi sannan ya miko min Iman ya rufe mana kofar, zagaya wa yayi yaja muka tafi.
Zagaye ya dinga yi damu daga wannan titin zuwa wannan har zuwa lokacin magriba, tsayawa yayi a wani masallaci yayi Sallah sannan ya kaimu wani wajen cin abinci, nidai duk a takure nake haka yayi mana takeaway muka fito, shopping mall din dake manne da wajen abincin ya shiga, ya ɗan dade a ciki sannan ya dawo hannun sa dauke da manyan ledoji ya zuba a baya muka dau hanya.
Muna zuwa gida ya tsaya jikin motar yana nuna min kayan ciki