DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kwashe kayan ki shiga dasu kizo muyi magana, dare ya fara yi.”

Kwashe wa nayi na dawo, na karbi Iman data fara bacci na kaita itama na sake dawowa na tsaya.

“Ya karatun?” Ya tambaye ni

“Alhamdulillah, yasu Hajiya? Kwana biyu bamuyi waya da Raudah ba nasan suna shirye shiryen finals.”

“Lafiya lou.”

“Ya maganar mu?”

“Na’am?”

“Kinji ai, ina so mu fara fuskantar juna, idan yaso sai nayi kokarin shawo kan Hajiya.”

Girgiza kai na nayi a nutse nace

“Maganar iyaye magana ce mai matukar girma, kayi hakuri mu yi abinda tace, bana so ka sami matsala da mahaifiyar ka.”

“Zaki jirani zuwa lokacin da zata amince? Zaki jirani?”

“Bani da zabi da rayuwa ta sai abinda Allah ya zaba min, idan kai din Alkhairi ne gare ni, nima kuma alkhairi ce a gareka, Allah ya sa ta amince, idan har ta amince ni bani da zabi.”

“Shikenan, in sha Allah zata amince, ki bani lokaci.”

Daga masa kai nayi, ya sakar min murmushi ya fada motar yana daga min hannu, sai dana ga fitar sa daga layin sannan na shige ciki ina saka key a kofar.

Da daddare nayi ta juyi ina tunanin maganganun, bani da zabi face amince masa, wacece ni ma da har zai tsaya bata lokacin sa akai na, bani da asali bare tushe, bayan haka wannan ce hanya kawai mafi sauki da zan saka masa da dukkan alkhairin sa.
    Sake juyawa nayi zuwa dayan barin ina tuna Farouk, mutum na farko daya so ni duk da karancin shekaru na, ban taba tunanin shi ma zai guje ni ba, haka dama rayuwa take shiyasa na bar wa Allah zabin komai na rayuwa ta, sau tari tunanin sa kan hanani sukuni har naji zuciya ta na zafi, tun ina sa ran haduwa dashi har na hakura na barwa Allah.
  Ban cire rai ba amma, kila watarana ya waiwaye mu, ko ba dan ni ba, ko dan yarinyar sa, duk da yace babu komai tsakanin mu, amma ina fatan ganin da zai mata kadai ya isa ya gamsar dashi yar sa ce,shafa kanta nayi ganin yadda yake bacci cike da kwanciyar hankali, bata da damuwa ko matsala, tsoro na daya ranar da zata tambaye ni mahaifin ta, duk da ina fatan kafin ranar na samo gamsasshiyar amsar da zan bata.


Shirin fita take taji ana mata knocking, ajiye abinda take tayi ta nufi kofar kai tsaye tana tunanin waye, turus tayi ganin shi, tayi saurin ja baya tana kokarin maida kofar

“Karki rufe min kofa.”

Wani kallo tayi masa kafin tayi dariya

“A matsayin ka nawa?”

“A matsayi na na wanda kike jira tsawon shekaru.”

“Jira?”

Tayi dariyar rainin hankali

“Karka manta babu auren tsakanin mu.”

“Kema karki manta nasan kinyi auren kin fito, kin zata bani da labari?”

Juyawa tayi kawai ciki ya bi bayan ta yana murmushi, falon yabi da ido, yadda aka kawata shi da kayan kawa da komai, sanyin Ac hade da kamshin turaren ta tun na fil’azal ne manne a falon, iska ya shaka ya fesar yana zama cikin jerin manya manyan kujerun da suka kara wa falon kawa.
Ciki tayi ta barshi zaune, sai data dau tsawon lokaci sannan ta dawo ta sauya shigar ta zuwa simple gown ta rufe kanta, zama tayi chan nesa dashi tana kallon screen din wayar ta.

“Me kake bukata?” Ta tambaya kai tsaye kuma a gajarce

“Nazo ne nayi miki wasu yan tambayoyi, nasan tabbas kinsan amsar su.”

“Then…” Ta kalle shi cikin ido sosai

“Kin shayar da Amal?” Yayi mata tambayar kai tsayen, kai tsayen itama ta amsa masa

“Eh akwai wani abu ne?”

“Akwai, kinsan auren Farouk dake kanta ko? Kuma kinsan musulunci ya hana auren wanda suka sha nono daya, amma ban manta ba tun a lokacin dana ga take taken ki na hana, saboda irin wannan ranar.”

“Na shayar da ita tun kafin kayi min magana, haka zalika na bari daga lokacin da ka hana.”

“Mesa baki fada min ba?”

“Me yasa baka fada min da zaka hada auren ba? What is my fault anan? Wait saboda nice karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko? Shine bayan komai ya kwabe muku zaka zo wajena.”

“Why are you like this? Kin chanja sosai.”

Dariya ta shiga yi sosai kafin tace

“Mutane na chanjawa ne daga lokacin da wanda suke tare dasu suka chanja, baka ga komai ba indai nice.”

Mik’ewa tayi tana duban agogo

“Ina da abin yi, can you please excuse me?”

“I’m not done yet, ina son sanin ina d’ana?”

“Shine tambayar da ya kamata nayi maka tun zuwan ka, ka sani ba wai nayi shiru bane, ina baka time ne kayi gaggawar fito min dashi duk inda kasa shi ya tafi.”

Ransa ne ya ɓaci, ya tashi tsayen shima zai maida mata martani wayar ta dake gefen sa tayi kara, kura wa wayar ido yayi da kuma sunan dake rubuce akan screen din kamar mai nazari, da sauri ta sa hannu ta dauke wayar tana sakata a silent. Shiru ne ya biyo baya ya kasa tantance abinda yake ji game da sunan da ya gani. Ganin ya kasa tunawa yasa ya share yana kokarin tausar zuciyar sa, sai daya dan ja lokaci yana tunanin yadda zai yi maganar kafin ya daure kamar an fuzgo maganar yace

“Abinda ya faru shekarun baya, menene gaskiya? Menene tsakanin ki dashi? Me ya faru a ranar?”

Dagowa tayi a dan zabure, sai kuma tayi saurin saita kanta tana sakin murmushi

“Duk abinda zuciyar ka ta tsara maka, shine abinda ya faru,kuma ya riga ya wuce babu amfanin dawo dashi baya, bani da lokacin wannan maganar.”

Tana kaiwa nan tayi shigewar ta daki tana rufo kofar da sauri, kamar wanda aka dasa haka ya kame a wajen yana ayyana abun a ransa, yanayin ta da yadda ya hangi tsantsar tsoro a idanun ta bayan ya kawo mata maganar ta sashi shakku, ko dai ya aikata abu cikin fushi? Ya biye wa dokin zuciya? Yayi mata adalci kuwa a lokacin? Me yasa yanzu yake jin son jin gaskiya duk da tsawon lokacin da aka dauka? Bashi da amsar tambayoyin. Da kyar ya kai kansa mota yana shiga yace

“Kano zamu je.”


Basu suka isa Kanon ba sai dare, Dadah na zaune saman abin sallah tana karatun Alkur’ani, ya shigo, da kallon mamaki ta bishi har ya dire a gabanta yana jin kamar ana sassara masa kasusuwan jikin sa. Da kyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da take masa, shiru ne ya biyo baya sai kuma ya tuna yana bukatar suyi magana

“Dadah kinsan Abidah ta shayar da Amal kuwa?”

Kai tsaye tace

“Na sani, amma ina ga ai ta daina tun lokacin daka hanata.”

Dafe kansa yayi da dukkan hannayen sa

“Ya akayi duk ban san da haka ba? Kinsan musulunci ya hana aure tsakanin wanda aka shayar dasu nono daya, duk da malamai sunyi sabani, wasu sunce idan har an shayar da nonon sau uku, toh ta haramta ga duk wasu da suke muharraman wadda ta shayar da ita din, wasu suka ce ko sau daya ne idan har an bata tasha ta koshi, toh an haramta auren tsakanin ya’yan matar data shayar da ita, ko kannenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya, ko yayyenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya,ko mahaifinta. Duk dai wasu muharraman da babu aure tsakanin su da ya’yan matar data shayar da ita, toh sun haramta ga wannan wadda aka shayar ɗin.
Wasu malaman suna ganin sai idan har ta shayar da ita na tsawon lokaci ne hakan zai kasance, toh amma dai ko yaya ne, nasan tabbas ta shayar da ita, na tsawon wata guda koma fiye, kinga kenan ta haramta ga Farouk.”

“Allahu Akbar, ilimi fadi ne dashi, ban taba sani ko ji ba wallahi, shiyasa ban kawo komai a kaina ba, bayan haka ko da ace na sani,bana ma tunawa da ta shayar da ita din.”

Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kansa da saman kujerar, komai ya chanja masa daga yan da yaso ya kuma tsara.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button