DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Da baya da baya ta koma ta fada saman gadon ta tana sakin kuka, idan har abinda taji Daddy na fad’a gaskia ne, kenan ita da Ya Farouk shikenan? Kai ina bazai yiwu ba, yadda ta kwallafa ran nan dashi, ace kuma shikenan? Sai ta kara sautin kukan ta sosai.
Da ido tabi wayar da kallo kafin ta shiga share hawayen fuskarta da sauri da sauri, dagawa tayi ta shige toilet bayan ta sawa kofar dakin key.
Tsawon lokaci ta dauka suna magana kafin ta ajiye wayar ta fito, lamo ta kwanta tana tunanin mafita.
***Babu wanda yayi mata maganar daga Dadah har Daddy. Taso tayi ma Dadah maganar taji me zatace amma bata so ta tabbatar mata da gaskiyar hakan, duk abin duniya yabi ya dame ta, gashi ana maganar komawar ta makaranta saboda lokaci na kara tafiya, kamar marainiya haka ta zama, duk farin ciki da take dah idan ta tuno da auren dake kanta yanzu ya kau, tunanin ta yadda za’a samu mafita ace akwai aure tsakaninsu kawai take, idan haka ne Mummy ta cuce ta wallahi. Bata da aiki sai kuka, ranar da sukayi waya da Mama ta fada mata abinda ya faru, kwantar mata da hankali tayi, ta dan ji dama dama kuwa, har ta dan saki ranta.
Tun ranar da ta fada mishi abinda ya faru be sake kiran ta ba, ya dai tabbatar mata da yana nan zai san yadda za’a yi.
Sati guda ya dire a kasar, ya wuce kai tsaye Abuja, Daddy na zaune wajen daya saba shan iska ya shigo gidan.
“Saukar yaushe?” Daddy yace yana fadada fara’ar sa, zama yayi kan katon carpet din yana mika masa hannu
“Mun same ku lafiya?”
“Lafiya lou mutanen Turai, Azeema kuwa tasan da zuwan ka?”
“Ina bata sani ba ai, zuwan nawa kenan.”
“Lallai sannu da zuwa, ka shiga ciki toh nima yanzu zan shigo ai.”
“Ok.” Yace kai tsaye ya shiga ciki, tana ganin sa ta rufe baki da hannun ta.
“Ya akayi haka?” Tace tana zaro ido
“Zuwan dole ne, akwai abinda zan duba ne ba jimawa zan koma.”
Ajiyar zuciya ta sauke
“Na zata ai ko lokacin da muke jira ne yazo.”
“Saura kiris.” Yace yana nuna mata hannun sa, dariya ta saka.
Shigowar Daddy yasa su yin shiru, zama yayi suka sake sabuwar gaisuwa,kafin a gabatar masa da abubuwa ci da sha, kadan yaci ya yi musu sallama ya tafi.
Yana fita ya tsura wa gidajen guda biyu ido kafin ya fashe da da dariya, motar sa ya shiga wadda ta kasance a rufe ruf da bakin glass, da karfi yasa hannu ya zare mask din fuskar sa, a razane na saki alkalami na ina sake duban sa da kyau
“Adam!!!” Na furta baki na na rawa.
Murmushin gefen baki ya saki kafin ya maida fuskar ta zama ta wani mutum daban ya ja motar ya bar kofar gidan da mugun gudu.
Ranoa: DG
30
Kai tsaye garin na Kano ya wuce, yana isa ya mata text kafin ya karasa wajen da zasu haɗu. Tana zaune tana jira sakon ya risketa, dama a shirye take saboda haka mayafi kawai tasa ta fita.
Kafin tazo ya cire mask din fuskar sa ya fito a ainihin kamar sa. Tana zuwa tayi saurin fad’awa jikin sa ta saka mishi kuka, shafa bayan ta ya shiga yi a hankali har ta tsagaita da kukan nata, tissue ya ciro ya mika mata
“Menene matsalar ki?”
Ya tambaya yana dago ta,
“Ya Farouk.” Tace cikin muryar kuka. Murmushi yayi mata yana jingina ta jikin kujerar motar
“Karki damu, ki koma karatun ki, zan san yadda zanyi.”
“Yaushe? Daddy fa ya gama sanin komai, kuma ya fada wa Dadah.”
“Akwai lokaci, akwai lokaci.”
Yace yana tada motar.
Shiru tayi tana tuna abubuwan da ya jima yana fada mata, haushin kowa take ji, babu wanda zatayi wa uzuri a cikin su, duk kuwa da sun yi mata sosai a rayuwa amma ba kamar mahaifin daya kawo ta duniya ba. Idan bata tsaya masa ba bayan kowa ya juya masa baya wa zai taimaka masa? Ita kenan daya mallaka a duniya dolen tane ta share masa hawayen sa.
***Tsawon makwanni biyu ya dauka a garin kafin ya tattara ya koma inda ya fito, itama Amal sai ta koma can Abuja don karatun ta ta cigaba da rayuwar ta kamar babu komai. Duk da lokaci zuwa lokaci sukan yi waya amma babu wanda ya san da hakan sai Mama kawai, shiyasa ma bata da matsalar komai dan kanta tsaye take abubuwan ta tun da sau tari ma a wayar Maman zai kira bayan sun gama magana sai ta bata.
Alaka ce mai karfi tsakanin su, sai dai ta gaza gane wacce irin alaka ce hakan da har tasan sirrin sa.
Dukkan kokarin Daddy na son ganin ya samu wani bayani ta wajen Mummy sam ta ki bashi fuska, rashin sanin yadda zai ɓullo mata ne da yadda yake mata gadara yasa ta kafe itama, zuciyar ta, ta riga ta k’ek’ashe shiyasa bata wani jin shakku ko wani abu game da hakan.
Tun yana tunanin jan aji ne irin na mata har ya gane da gaske take ba zata saurare shi ba, duk baya jin dadin komai, tun bayan rabuwar su da auren da yayi bayan lokacin da kadan bai taba jin wani abu game da ita ba sai yanzu da girma yazo.
Duk da Mama na kokari sosai wajen kula dashi amma ya kasa yakice ta daga ransa. Mai yasa ya kasa mata uzuri a wancan lokacin? Ya kasa gane dalilin sa na yin hakan, gashi yanzu ya fada kogin nadama da dana sani mara amfani.
Farouk
Aiki yake sosai babu kama hannun yaro, sosai yake jin dadin aiki da Mr Johnson shiyasa bashi da wata matsala da kasar.
Zuwa lokacin da ya fara karatun sa ya riga ya tara kudade masu yawan gaske, duk da haka duk weekend yana zuwa ya zauna a wajen hakan kuwa ba karamin dad’i yake ma Mr John ba dan shi a rayuwa yana son mutum mai kwazon aiki.
Da gangan Farouk ya zamar da kansa agogo baya bada lokacin sa a komai sai neman halal dan yayi wa kansa alkawarin ko zai koma gida ba zai taba bari ya rabi da kowa ba balle har ayi masa wata alfarma.
Batun mutumin nan kuwa, tun ranar bai sake haduwa dashi ba, sai ya tattara shi ya watsar ya rungumi sana’ar sa da karatun sa.
***A gurguje ya sauko kasan shagon tun bayan daya samu sakon supervisor din sa akan yana son ganin sa, dole ya tattare aikin da yake waje daya ya nufi makarantar.
A daidai gate din shiga ya hange shi, da motar sa ya fara gane shi, sai dai yau ba shi kadai bane hadda mace da yara, da sauri ya tsallaka bangaren su yana tsaida su, kamar ba zai tsaya ba sai kuma yaga yaja ya tsaya dage gefe, karasawa yayi cikin sassarfa yana kokarin ganin fuskar sa.
“Assalamu alaikum.”
Yayi sallama kai tsaye, a tare suka amsa dukkan su, kafin namijin ya juyo da dukkan fuskar sa yana duban shi, duba na tsanaki.
A wani irin yanayi suka hada baki a tare kamar wanda maganar tazo wa a lokaci daya cikin yanayin dake kama da an fuzgota suka ce
“Farouk!”
Ware idanun sa yayi, duk da karancin shekarun sa ba zai taba mantawa dasu ba, mutane biyu masu kusanci dashi, daya kani ne ga mahaifin sa, daya kuwa kanwa ce ga mahaifiyar sa. Mai suke anan? Me yasa babu wanda yake tunawa dasu? Babu wanda yake maganar su. Bayan har da d’an da suka tafi suka bari. Ja’afar! Mai yasa suka manta da kowa suka zo nan suka kafa sabuwar rayuwa. Bashi da amsar ko daya daga cikin wadannan tambayoyin, shaf ya manta da abinda ya kawo shi makarantar, da sauri ya fada motar yana kallon yaran guda uku dake zaune a bayan motar suma suna kallon sa.
Sautin kukan Anty Safiyya ne ya sake dagula masa lissafi, kuka take sosai sai dai babu wanda yace uffan har suka isa gida. Daga kai yayi yana karewa gidan kallo, tsawon wannan shekarun suna rayuwar su su kadai ba tare da dangi ba. Mai yasa?