DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

★★★★
Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji, idan baku manta kuduri na ba, ba zai wuce na cikar buri na ba, karatu na nasa a gaba babu wani abu daya sauya na daga yadda rayuwar tawa take
Yadda komai yake wanzuwa cikin hukuncin Allah, zaka tabbatar da babu mai tsara bawa ƙaddarar sa face Allah SWA.
Hakan ce ta kasance dani, a yau na rubuta jarabawar karshe ta makarantar horar da lauyoyi dake garin bagauda (law school). Idan na tuna matsayin karatun da nayi a daya daga cikin manyan jami’oin Nijeriya (BUK), na kan ji wani nishadi mara misaltuwa, ban taba hasashen hakan ba, sai gashi Allah ya hukunta min cikin manyan kaddarorin rayuwa ta.
Anas ya zama wani babban jigo a karatu da rayuwa ta, sannan Kamal daya zama mafi kusanci dani da yarinyata
Tun ina tunani ko hasashen zan hadu da wani daga cikin ahalin su Farouk har na daina sai dai har lokacin yana makale a kahon zuciya ta. Duk sanda na kalli Iman na kan tuna dashi da komai nashi.
**Sanda sakamakon jarabawar ya fito sai dana yi kuka, kukan farin ciki saboda yadda result din yayi kyau ainun, wai yau nice rike da shaidar zama cikakkiyar lawyer, Anas yaso yafi ni farin ciki saboda a daidai lokacin ne Hajiya ta amince masa da aure na, duk da abin yazo min a wani irin yanayi amma nayi kokarin boyewa na biye masa wajen nuna farin ciki na, y’an kwarya kwaryar walima ya shirya min daga ni sai shi sai Iman, Baba Altine da Ramlah sai kawayen ta biyu, ban gayyaci kowa ba a yan makarantar mu, duk dama babu wata shakuwa tsakanin mu sai abinda ya shafi karatu.
Kamal tun daya koma ban sake saka shi ido na ba sai dai muna waya sosai dashi.
Komai ya sake chanjawa bayan gama karatu na, kai tsaye Anas yake zuwa a matsayin zance. Mutum ne shi da yake bin komai a tsare, dan haka bai taba ketare iyakar sa ba, komai yanayin sa ne a addinance babu jahilci. Hakan na kara birgeni dashi, yadda yake tafiyar da rayuwar sa cikin tsari abin so ne.
Waye Shi!
Hannu na sakale dana Iman muke zagaye supermarket din, Alk’awari nayi mata idan har ta iya wasu surori zan kai ta, ta zabi abinda take so, da kanta ta fada wa Anas aikuwa sai ga kudi ya aiko mana dashi.
Doguwar riga ce bud’addiya a jikina, na yane kaina da madaidaicin mayafi, takalmin kafata irin flat shoe ne, babu yadda za’a yi daga kallo daya ka gane wacece ni ko daga ina na fito, jikina ya murje sosai na zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni. Bamu da matsalar komai saboda Anas ya tsaya mana.
Mun bata lokaci sosai kafin mu gama saboda yadda Iman ta tsaya ruwan ido,sai dana gaji nace tafiya zanyi sannan ta hakura, napep muka tara muka nufi gida lokacin duhu ya fara sauka.
Muna cikin tafiya wayata tayi kara, ciro ta nayi ganin Kamal ne yasa na daga.
Magana muke wanda ta dauke hankali na har muka kusa wuce inda zamu sauka, da sauri na tsaida me napep din muka sauko na mika masa kudin har lokacin wayar na makale da kunne na.
Kasancewar har anyi magriba tasa layin babu kowa, da hannu daya na rike wayar da kayan dayan hannu na rike Iman dake min mitar na bata wayar su gaisa, tafiya muke a kafa ina cigaba da amsa wayata ban bi ta kanta ba.
Kamar walkiya haka naji an fizge hannu na dake hade da nata, kafin nayi wani yunkuri an watsa min wani abu mai matukar yaji da radadi a idanuwa na, bansan lokacin dana saki kara mai karfi ba cikin tsananin azaba na durkushe a wajen.
Ina jin sahun digadigan su, ina jin ihun Iman mai haɗe da kiran sunana, a birkice na tashi ina laluben ta, tsananin duhun daya mamaye ido naa yasa na kasa aiwatar da komai.
Ƙarar tashin motar su kawai naji, na sake yunkura wa da dukkan karfi na, sai dai ban yi ko da taku daya ba naji an shaka min wani abu da yasa na daina gane komai.
Rano
Manage ????????????????????????????????
Dukkan masu kwamplain an daure su, kuyi hakuri za’a kunce ku a hankali, zaku gane kan komai. DG
31
★★★★★
Kukan da nake ya dawo hankalin mutane wajen, da sauri wani makocin mu daya shaida ni ya karasa gida ya kira Baba Altine, a kideme ta fito babu ko mayafi, tana gani na ta hau salati tana kuka. Zuwa lokacin radadin da nake ji ba kadan bane a idanuwa na, kama ni aka yi da taimakon wani Alhaji ya bada aron motar sa aka dauke ni zuwa asibitin.
Kamal a rude ya fito daga dakin sa, part din Iyayen sa ya nufa riga a hannu yana kokarin sakawa, Ammi na zaune ta tallafe fuskarta da hannun ta ya shigo a kid’ime.
“Ammi ina Daddy?” Yace a rude yana kallon ta.
“Menene?” Tace tana tashi tunanin ta wani abun ne ya faru.
“Kano zan tafi, akwai matsala.”
Yayi hanyar fita daga falon, da sauri ta riko shi, tana kallon yanayin sa
“Kana da hankali kuwa? A daren nan? Wai menene ma ya faru?”
“Ban sani ba wallahi, kawai muna magana da Aminatun, naji ihu sai kuma na daina jin komai, ina ta kira kuma wayar bata shiga.”
“Yarinyar da ka bani labari? Har yanzu kuna tare kenan.”
“Ammi pleaseeeeee, suna bukatar taimako wallahi, bari kawai naje wajen Old Woman nasan ita zata fuskance ni.”
“Tsaya.” Tace tana daukar wayar ta, Alhaji Marwan ta kira, bai dauka ba har ta katse, ta sake kira sai ya biyo ta da text message suna wani meeting ne zai kira. Ajiye wayar tayi tana kallon dan nata
“Ka yi hakuri mahaifin ka ya dawo kamal, yanzu dare yayi.”
“Amma…”
“Dan Allah, I can’t risk loosing u, kasan dai yadda tafiyar dare take, ka bari kaje by flight idan Allah ya kaimu, yanzu ka duba available flight da time.”
Kamar zaiyi kuka amma dole ya hakura ya koma dakin sa, tsawon daren kiran wayar ta kawai yake amma bata amsawa, haka dai ya hakura yana ta Allah Allah gari ya waye ya je ya gani, ya rasa dalilin daya sa ya damu da ita sosai da al’amuran ta.
Idan nace muku na runtsa tsawon daren toh nayi karya, kafin safiya idanuwan sun haye sunyi suntum, bana ko iya bude su ga bakar azaba, duk da wannan tunani na na wajen yata, waye wannan da zai sace ta, wai me nayi wa mutane ne har haka da ba zasu barni nayi rayuwa ta ba, iya sani ba bani da wani abokin gaba ko fada, amma me yasa hakan ke kasancewa dani.
Shigowar Anas dakin tare da yan sanda yasa nayi shiru daga kukan da nake na zuci, dan likita ya hanani kuka saboda idon nawa zai kara rikicewa.
Tambayoyi sukayi min suka fita, kamshin turaren sa daya sake kusantoni yasa na gane ya matso sosai
“Sannu.” Yace yana dora hannun shi saman goshi na. Bance komai ba,zuciya ta ta riga ta karye, ina ji kamar numfashi na zai yanke na bar rayuwar baki daya. Shiru ne ya biyo baya, ina jin motsin sa yana taba abu a jikin gadon, kafin yace
“Ina zuwa.”
Yana fita Baba Altine ta shigo Kamal na biye da ita, kamar wadda wani dangi ko dan uwanta ne yazo haka naji, duk sai naji komai na sake bijiro min, mantawa nayi da kashe din likita na shiga rera kuka sosai suna bani baki, shigowar likitan ya katse min kukan da nake, tare suke da Anas, ganin Kamal a dakin ya dan sha jinin jikin sa kafin ya basar yana sauraron bayanin likitan.
Aiki za’a shiga dani na gaggawa, saboda haka aka wuce dakin gwaje gwaje, babu wanda ya matsa nan da can a cikin su har zuwa lokacin da sakamakon ya fito. Daga nan aka wuce dani zuwa dakin theatre domin gudanar da aikin.