DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Daki ta shiga da sauri ta hau harhada kayan ta, har lokacin kuka take, yaran na tsaye bakin kofa kowa yayi shiru jiki a matukar sanyaye suke duban mahaifiyar tasu, idan da sabo sun saba duk lokacin da abin ya motsa sai anyi da gaske take hakura, sai dai yau zuwan wannan bakon ya so saka su a tunani, iya sanin su babu wanda yake zuwa musu da sunan dan uwa ko wani dangi, haka nan suke rayuwar su daga su sai iyayen nasu biyu.
Shigowar Abban nasu dakin hannun sa rike dana Farouk yasa suka matsa gefe suna jiran suji mai zai faru.
Anty Safiyya na ganin sun shigo tayi saurin rufe akwatin kayan ta tahau jan ta da sauri tana nufo su, kama hannun Farouk tayi cikin kuka tace
“Wuce mu tafi, ba zan sake zaman ko da awa biyu bane a garin nan na gaji!”
Gam ya rike hannun mata idanun sa na kadawa, duk da har lokacin ya kasa tunanin abubuwan da yadda suke sai dai tsantsar tashin hankalin da yake gani a idanun uncle Aliyu kadai ya isa ya gane akwai gagarumar matsala. Mai yasa tsawon wannan lokacin babu wanda ya nemu su?”
A gefen gadon ya zaunar da ita, ya rike mata hannu yana durkusawa a gaban ta, ganin taki daina kukan yasa hannu ya shiga share mata hawayen kafin yace
“Dan Aallah ki daina kuka, idan kina kuka mu fa? Dukkan mu zaki saka muyi kuka.”
“Ina Ja’afar?” Tace tana share hawayen nata
“Ja’afar yana nan cikin koshin lafiya.”
Girgiza kanta tayi
“An min adalci kenan? A rabani da d’ana tsawon wannan shekarun ba tare da ya ganni ba Farouk?”
“Kiyi hakuri.”
Uncle Aliyu ne ya matso jikin gadon yana rike mata hannu
“Safiyya… Nasan kina dauka ta a cikin mutane mara sa adalci da son kansu ko? Kina tunanin na rabo ki da kowa naki na kawo ki nan, ki sani bani da zaɓi da ya wuce hakan, ba’a son raina hakan ta faru ba.”
“Kullum magana daya kake, baka da zaɓi, baka taba zaunar dani ka sanar dani abinda ya kamata na sani ba, taya kake tunanin zan yadda da kai?”
“Bani da ikon sanar dake ne, sai dai a yanzu komai ya wuce, ni kaina ina bukatar ganin dangi na, dana kasa kare su na tsaya musu sanda suke da bukata ta, musamman Anty Abidah.”
Cikin zumudi tace
“Kana nufin zamu koma gida?”
Daga mata kai yayi
“Tsawon lokacin nan ina jiran wannan ranar ne, duk yayi min ikirarin ba zan taba ganin ranar ba, sai dai ban fitar da rai ba, ina ta addu’a Allah ya kawo min karshen halin da nake ciki, Safiyya ba haka kawai na zauna anan ba, akwai babban dalilin da ya rike ni har wannan lokacin.”
Juyawa yayi yana duban Farouk
“Ya akayi kazo nan, ga dukkan alamu ba yanzu kazo ba,yanayin ka ya nuna ka jima a kasar, menene ya faru?”
Ajiyar zuciya Farouk ya sauke yana jin an tabo masa tsohon mikin zuciyarsa, sai dai dole zai sanar musu komai saboda ga dukkan alamu Uncle Aliyu ya san wani abu dasu basu sani ba , sai dai kafin nan yana bukatar amsar tambayar dake nukurkusar zuciyar sa
“Ina da dalili babba na barin kowa na dawo nan da zama, sai dai na kasa auna fahimta ta a sanda na ganka, tun zuwa na farko kasar nan na fara haduwa dakai Allah be sa zamuyi magana ba, me yasa tun bayan tafiyar ku, babu wanda ya kuma neman ku, yasan inda kuke ko yayi maganar ku?”
Murmushi Uncle Aliiyu yayi ba tare da ya amsa ba ya jeho masa wata tambayar
“Tun tasowar ku ka taba ji ance maka yau ga Kawun ka Adam yazo?”
“Ina tunanin Uncle Adam ya rasu tun muna yara ai ko?”
“Eh ya rasu a idon duniya sai dai be rasu a idanun Aliyu ba, yana nan da rai yana yawo a doran kasa.”
Zaro ido sukayi a tare da Anty Safiyya, ta tashi tsaye tana kallon mijin nata cikin rawar murya tace
“Ya akayi hakan ta kasance?”
“Babu amsar wannan tambayar taki sai a gaban mutanen da hakkin sanin hakan ya wajaba akan su, dole sai mun tabbatar da hakan ta hanya gamshashiya ba ta fatar baki ba, ƙaryata labarin mutuwar da ya dauki tsawon lokaci da wucewa ba abu bane me sauki. Musamman a wajen mutane irin su Adam wanda babu digo na imani a ransu.”
“Tabbas akwai rudani a cikin wannan maganar Uncle Aliiyu, sai dai hakan yasa na fara wani tunani da hasashen wasu abubuwa ciki har da abinda ya faru dani, ina so zan sanar maka da komai da ya faru bayan tafiyar ku, ina nufin abinda ni ɗin zan iya dorarwa akai ba wanda ban sani ba, daga nan zan baka labarin abinda ya sa na dawo nan ɗin, ina fatan hakan ya bani haske a abun da na jima ina tunani da hasashen wanda yake da hannu a ciki.”
“Madallah da kai, hakan ne zai taimaka mana kwarai wajen sanin ta ina zamu tabbatarwa da duniya abinda ya jima yana boye.”
“Ina fatan haduwar mu ta zama warwawar manyan daurukan da suka dade a daure, ina fatan ya zama silar wanzuwar farin ciki a zukatan mutane da suka dade da mantawa da yadda farin ciki yake.”
Madaidaicin study room din sa suka nufa, daga shi sai Farouk da Anty Safiyya, yaran na falo kowannen su ya samu abin tattaunawa da zuciyar sa, cikin gamsasshen bayani Farouk ya warware musu komai na abubuwa da zai iya sanar dasu, har zuwa lokacin da yayi bankwana da kowa.
Babu digon mamaki ko tashin hankali a tattare da uncle Aliyu bayan ya gama sanar dasu komai, a yadda ya nuna ma kamar dama yana da masaniya da dukkan abinda ya faru ɗin.
Da kyar suka barshi ya koma gida da niyyar zai dauko abubuwan bukatuwar sa ya dawo nan ɗin, sai a sannan ya tuna da maganar supervisor din sa daya ke kiran sa, a gaggauce ya tura masa mail na ban hakuri da bayanin uzurin daya riƙe shi, babu komai yace masa ya kuma sake bashi lokaci akan yazo ya ganshi gobe idan Allah ya kaimu.
Kwanan sa biyu ya gama tattare komai ya dawo gidan nasu, Anty Safiyya da duk ta tashi hankalin ta ta dauka ba zai dawo ba, sai data ganshi sannan hankalin ta ya kwanta.
Karatun sa daya zo gangara ya bada himma wajen hattama shi, shi kanshi a yanzu hankalin sa ya soma komawa gida, yana ji a ransa wannan lokacin zai hadu da Aminatu, duk da babu wani labari daya samu tun bayan zuwan sa game da komawar ta Shagari, amma kowanne lokaci cikin bibiya yake yana fatan Allah yasa ta koma.
Shirye shiryen komawar su ya kankama, gefe guda yana cigaba da zuwa shagon dan ba karamin sabo yayi da mutanen wajen ba, tun da suka ji zai tafi suka shiga tashin hankali, barin ma Mr John daya sakar masa kusan dukka ragamar wajen shi sai dai ya dan duba abinda yake ganin zai iya amma komai a wajen Farouk ke kula dashi cikin kwarewa da kaffa-kaffa.
Tsawon kwanaki hudu kenan tun bayan da akayi min aikin, sai dai ba’a cire ba sai zuwa karshen sati idan mai duka ya kaimu.
Kowacce uwa zata fuskanci yanayin tashin hankalin da nake ciki, batan d’a ba abu bane mai sauki, na rasa inda zan saka kaina, babu wani labari game da batan Iman, duk da kwantar min da hankalin da suke hakan bai saka hankalin nawa kwanciya ba, ji nake kamar na gudu daga asibitn na tafi neman ta da kaina,sai dai nasan daga Anas har Kamal suna iya kar kokarin su wajen ganin an samu ko da wani hint ne akan haka, kullum cikin jiran kiran su muke amma shiru kake ji kamar malam yaci shirwa, babu wani bayani gamsashe. Addu’a muka dukufa yi babu dare babu rana, ba ta kaina nake ba, buri na kawai naga yata, ita kadai ce dangin da nake dashi na kusa, duk wani da zai rabe mu da sunan kauna ba kamar ni da itan ba.