DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL


Ranar da za’a cire min abinda aka saka aka nannade idon dashi duk jikina yayi sanyi da tunanin abinda zan tarar. Dishi-dishi na soma ganin komai, nayi saurin runtse idon ina jin kamar sun sake kankancewa akan yadda suke a dah, a hankali na sake bude su ina duban mutanen da ke dakin daya bayan daya, har lokacin bana ganin su tar sai dai ina iya banbance komai da kowa, glass likitaan ya saka min hakan ya taimaka wajen kara karfin ganin nawa, sai dai babu kaso hamsin ciki dari na gani na adah.

     Kuka nake so nayi amma babu hawayen ma balle har na saka ran zasu zubo, da zuciya ta na shiga kokawa cikin yanayi mara misaltuwa, an cuce ni an lalata min rayuwa yanzu kuma an kashe min baban jigo na rayuwar mutum, idan aka taba maka ganin ka an gama da kai, makanta babbar musiba ce sai wanda ya sami kansa a ciki ne kawai zai gane. Kai tsaye na yanke wa kaina hukunci na kira kaina da Makauniya, eh makauniya mana tunda menene banbanci na da wanda basa gani gaba daya, illar ido daga ranar da ya riga ya tabu toh daga lokacin sai dai hakuri saboda yadda zai tayin gaba.


Kai tsaye gida muka wuce bayan an sallame ni, babu Anas babu Kamal sai keke napep muka samu ya kaimu dauke da kayan mu, waya ta dake saman cinyata tayi kara, na dauka ina duban screen din, bazan iya karanta rubutun ba, dole na jawo glass din na saka na shiga bin rubutun a hankali ina kokarin karantawa, ji nayi idon ya fara ruwa, dole na rufe na kira shi kai tsaye ina manna wayar da kunne na

” Kina ji? Gamu nan tare da Daddy da Uncle Kabir, zasu duba ki sai kuma yayi miki maganar Iman, ina tunanin zai iya taimakawa idan yasa baki a kara tsaro sosai wajen neman nata, sai mun ƙaraso.”

“Ai an sallame mu ma, muna gida.”

“Kash, shikenan bari na fada musu, zan kira ki.”

Kashe wayar yayi ya juyo baya

“Daddy Ashe an sallame su ma, wai suna gida.”

“Toh, babu damuwa sai muje station din da kace case din na hannun su, idan yaso sai muji yadda za’a yi.”

Kallon Daddyn su Farouk yayi yace

“Friend ban taba ganin Kamal ya zama so serious akan abu irin wannan lokacin ba, shiyasa nake so nayi supporting nasa with all I can.”

“Hakan nada kyau, ban taba tunanin yara na bukatar support dinmu ba sai bayan na rasa Farouk, ban taba bashi dama yayi wani abu da kansa ba, i always find fault a kansa bansan me yasa ba, sai da kuma ya matsa nake dana sani.”

“Suna bukata sosai, idan yaro yazo ma da abu ka fara bawa abun big thought,idan kaga akwai fault a ciki sai ka zaunar dashi ta cikin hikima ka fahimtar dashi illar abin, amma idan kace zaka zama tough toh yaran ka zasu na tsoron ka, ba kuma zaka taba sanin halin da suke ciki ba, komai a boye zasu dinga yin sa sai abu ya kwabe kuma sai kaji ana wallahi wallahi.”

“Haka ne.” Yace yana girgiza kansa.

Hirarrakin su suka cigaba har suka isa station din, waya Daddy ya daga ya kira commissioner of police na gaba daya Kano state ɗin ya sanar masa abinda yake so ayi, kai tsaye ya amince ya kuma hada su da head na station din da case din ke hannun su, a take aka chanja case din zuwa Babbar headquater su.

Dukkanin su a gajiye suke dan ba karamin yawo suka sha ba akan case din da kuma wasu harkoki na bussiness da suka shigo dasu garin na Kano, a gidan Dadah suka yada zango la’asar likis, zarewa Kamal yayi ya nufi gidan Aminatu dan tare zasu koma da Daddy sablda yadda ya ke kokarin ganin ya dora kamal ɗin akan komai na kasuwancin sa.
Har dare suna gidan sai da suka ci tuwo sannan suka tafi driver ya ajiye su a airport, abin ka da tafiyar manya cikin yan mintuna suka isa Abujan.
Dukkan abubuwan daya saba gabatar dasu sai daya kammala su kafin yayi shirin kwanciya, be iya zuwa ganin mahaifiyar sa ba yau kamar yadda ya saba idan ya dawo yakan je suyi hira yaji bukatar ta, har ya kwanta ya tuna da wani mail da wani abokin cinikayyar sa dake birnin London yayi masa tun rana, ya kuma kirashi akan lallai ya duba a yau din dan abin nada muhimmanci.
Tsam ya mike Ammi dake kwance ta bishi da ido tana gyara kwanciyar ta, hutun sa koda yaushe kadan ne, daren da yake samu ya huta ma sau tari yana kwanciya zai mike ya shiga wata sabgar kuma da na’ura mai ƙwaƙwalwa.
Shiyasa wani lokacin akan ce mara arziki yafi mai shi kwanciyar hankali da nutsuwa.
Zama yayi yana dora computer a saman dan karamin table din dake cike da tarkacen takardun sa, kunna tayi ya runtse idon sa yana jin kansa a cunkushe. Email ɗin sa ya shiga ya fara dubawa a hankali yana nazarin komai.
Tsawon lokaci ya dauka yana dubawa kafin ya kashe komai, wayar sa dake ajiye saman bedside drawaer ya dauka yana kokarin sata a flight mood sakon dake yawo a saman notification bar din sa yaja hankalin sa, budewa yayi ya soma karantawa

“Cikar buri shine samun abinda zuciya ta kwadaitu dashi. Haka ma abu mai matukar muhimmanci na faruwa na da mutane masu muhimmanci.Kunyi tarayya akan abu guda, ba tare da sanin ku ba, saboda ku ɗin wawaye ne mayaudara. A yau abinda yafi komai muhimmanci a gareku kai da wanda kake kira aminin ka na hannu na. Ina fatan ku samu karfin zuciyar iya fuskantar abinda ke tunkaro ku!”

Be fuskanci abu daya da sakon ke nufi ba, sake karantawa yayi ko zai samu wata amsa aciki, sai dai a yadda sakon yazo babu wani abu da zai iya fassarawaa ciki har ya gane inda maganganun suka dosa.

Menene sukayi tarayya da aminin sa akai? Abu kuma mai muhimmanci gare su? Dole yasa a bibiyar masa number sakon da safe idan Allah ya kaimu.
Gaba daya sai yaji dan guntun baccin dake idon sa ya kaurace masa, dole ya nufi toilet ya dauro alwala ya shiga nafilfili yana rokon ALLAH ya kare su daga sharrin masu sharri.

RanoDG

                       32

★★★
Da safe ya tashi yana shiryawa sakon na cigaba da yi masa yawo a kwakwalwa, be wani tsaya karya wa ba ya karasa ya gaida Hajiya Turai a tsaitsaye ya fita.
   Daddy shirye yake shima tun bayan da sukayi waya saboda haka yana fita suka hadu suka dau hanya, wayar sa ya ciro ya mika masa ya duba sakon, shi din ma bai wani gane komai ba, sai ya kashe ya mika masa yana kallon sa

“MD ban gane komai akan sakon nan ba.”

“Nima hakan ce, kuma iya tunani na na kasa gane waye zai tura dashi?”

“Shine, hanya mafi sauki ayi tracing sakon,daga nan sai mu san yadda zamuyi.”

“Shikenan.” Yace yana lumshe idon sa, daren jiya bai wani runtsa ba, ba wannan ne karo na farko daya fara cin karo da irin wannan sakwannin ba, sai dai na yanzu yasha banban da sauran, idan har ya fahimta komene yana da alaka da abokin sa, hakan ya kara saka shi a taraddadin waye zai masa wannan?

Lokacin da PA d’insa ya bashi statement din dake kan sim card din yayi mamaki kwarai, suna da duk wani information da akayi register sim din dashi bashi da alaka da wanda ya rubuto sakon, ga dukkan alamu ma irin sim card masu register akan su ne sai dai kawai ka siye su a haka.
Shafa kansa yayi ya mikawa Daddy result din yana sake resting sosai akan kujerar office din nasa, dogon nazari Daddy yayi kafin yace

“Ina ganin so ake ayi wasa da hankalin mu, a shagaltar damu da abinda yake mai muhimmanci, karka damu zan san yadda za’ayi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button