DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ok duk yadda kace haka za’a yi.”

Wayar sa ce ta hau burari, duba wa yayi ganin KAMAL ne yasa ya dan tura hular sa baya

“Kamal ba zai barni na huta ba idan ban tashi tsaye akan case din nan ba.”

“Da gaskiyar sa, atleast he’s willing to help.”

“Haka ne.”

Yace yana bin kiran, magana sukayi kadan ya ajiye wayar ya cigaba da duba abubuwan da zai duba suna hira jefi jefi.


Duk motsin Farouk na kan idon Anty Safiyya, gani take kamar zata sake rasa babbar damar da take ganin ita kadai ce zata sata komawa ƙasar ta, ta gaji ainun, tana bukatar wani dangi a kusa da ita, ace rayuwa daga kai sai miji sai yaya. Tunanin da kachokam ya tafi akan Ja’afar, kullum kwanan duniya da tunanin sa take kwana take tashi, ba abu bane mai sauki a raba uwa da danta tun be san waye shi ba,tana bukatar ji daga gareshi, tasan matsalar sa, abinda yake so da wanda baya so.
Karatun Farouk ya kare, saboda haka uncle Aliyu ya shiga shirye shiryen dawowar su a boye ba tare da sanin kowa ba sai shi Farouk din.
Sai da komai ya kankama sannan ya sanar ma Anty Safiyya, ranar bata iya runtsawa ba kwana tayi tana duban ticket din tana hawayen farin ciki

Jirgin karfe sha biyun dare zasu hau, saboda haka sai bayan sun gabatar da sallar isha sannan suka fito, yaran duk basu da walwala idan ka cire mahaifiyar su da har nema take ta manta wasu abubuwan nata sai da Uncle Aliiyu ya ankarar da ita.
Duk da Farouk ba a wannan lokacin yaso ya koma ba, amma shima yana bukatar jin amsoshin dake dan kare a zuciyar sa.


Kuka nake na zuci na rasa wanda zan fadawa damuwa ta, yau tsawon mako guda kenan da kwanaki biyu babu labarin ta, Hajiyar su Anas sunzo sun duba ni ita da Ramlah da wata kanwarta sai dai yadda naga Hajiyar tayi min sai nake jin kamar akwai lauje cikin nad’i, ina kyautata zaton ba a son ranta ta amince wa Anas ba. Hakan kuwa be dame ni ba, dan ni yanzu ba ta aure nake ba, buri na daya shine naga yata na kuma san wanda yake kokarin kassara mana rayuwa ba tare da mun aikata masa komai ba.
    Duk da Kamal ya bani tabbacin maganar tana hannu manya amma na kasa aiwatar da komai, magana ma idan ba Baba Altine tayi da gaske ba sai na wuni bance komai ba, daga uhum sai um um.
    
Murmushi na saki me matukar ciwo, bayan na dawo daga dogon zangon dana tafi na tunanin rayuwa ta,tun daga lokacin dana budi ido na na ganni a wannan duniyar me cike da mutane marasa tausayi da imani.
    Mutane biyu masu matukar muhimmanci a rayuwa ta a yau na rasa su, ciwon da zuciya ta ke ciki ba zai misaltu ba, da kyar na mike daga kwanciyar da nayi,waya ta dake yashe a saman gado ta dau ruri a karo na uku, karamin tsaki naja kafin na mika hannu na dauka, kamar yadda na zata shi din ne kuwa, Kamal. Murmushi nayi daya fi kuka ciwo  na katse kiran ina jingina da jikin dan madaidaicin fridge din dake daura da kofar shigowa dakin.
   Sake shigowa kiran yayi na daidai ta zaman glass din ido na ina dagawa cikin muryar data fi kama da wadda bata da gata ko galihu nayi masa sallama cikakkiya kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu.

“Ina ta kiran ki tun dazu.”

Yace kai tsaye bayan ya amsa sallamar tawa.

“Sorry na tafi wani dogon tunani ne kamal.”

“Zaki fara ko? Gani nan zanzo na dauke ki muzo nan station din, Daddy ma sun kusa ƙaraso wa shida Uncle Kabir.”

Dan dum naji gaba na ya fadi nan da nan, dakewa nayi na amsa masa da toh na fito falon, Baba Altine na zaune tana tunani gefen ta karamar jikar tace data dauko ta tun zuwan da tayi ganin gida zaune tana barar gyada.
  Zama nayi a gefe ina juya wayar hannu na, tunanin haduwar da zanyi da mahaifin kamal nake, duk sai naji na damu, kasan zuciya ta cike take da tsoron haduwar mu, ina jin karar tsayawar mota a kofar gida duk sai naji kamar an tsaida gudun jinin jiki na, a kasalance na mike ina kallon kiran sa ba tare dana daga ba na yi hanyar wajen.
Yana zaune ya zuro kafuwan sa wajen motar ya dago jin fitowa ta, bai tsaye wata doguwar magana ba ya tada motar muka bar layin.
Mun riga su isa station din saboda haka muka samu waje muka zauna zaman jiran su, basu iso da wuri ba sai bayan mun dade da isa, a waje Daddy ya tsaya yana amsa waya baban su Kamal ne kawai ya shigo, kaina a kasa ina kara jin abu mai kamar tsoro tsoro na fizgata, wuce mu yayi kai tsaye ya shige office din DPo ɗin, a dan rada rada nace ma Kamal

“I’m nervous.”

Dariya ya saka yana duba na

“Kin cika tsoro.”

Shiru nayi ina tunanin abinda yasa nake jin hakan, takun tafiya muka ji nayi saurin sake nutsuwa har suka ƙaraso gaban mu, a hankali na dago yayi daidai da duba na, kura min ido yayi cikin wani irin yanayi me kama da kallon sani, da sauri na furta

“Ina wuni?”

Kada kansa yayi a kajarce ya amsa yana maida hankalin sa kan Kamal

“Itace?”

“Eh itace Daddy.”

“Ina iyayenki?” Ya wurgo min tambayar a bazata, da sauri Kamal yayi karaf yace

“Sun rasu ai Daddy.”

Boyayyiyar ajiyar zuciya na sauke, ina jin dadin yadda Kamal ya cece ni, bansan amsar da zan bayar ba hakan kuma na iya jefa shakku a zuciyar sa, ina ji suka cigaba da magana da Dpo akan yadda za’a yi.
Daidai lokacin Daddy ya gama wayar da yake ya shigo ciki, dukkan su suka mike cike da girmamawa suka sara masa, hannu ya daga musu ya ƙaraso inda muke yana kokarin fahimtar maganar da suke.

“Ina fatan akwai wani improvement akan batar yarinyar?”

Da sauri na dago jin irin maganar Farouk, sai dai wannan girma ya yi mata rufi sosai inda kai tsaye zaka gane mamallakin muryar Baba ne, yawun bakina ne ya kafe a diririce nace

“Daddy?!” Sai a lokacin ya lura dani, ware idanun sa sosai yayi akaina cikin tsananin mamaki yace

“Kamar Aminatu ko?”

Sai na fashe da kuka da karfi ina daga mishi kai

“Ikon Allah.” Ya furta yana dubana duban tsanaki

“Ko zuwan mu wajen Dadah sai data yi min maganar ki, ina kika shiga tsawon wannan lokaci?”

Ban iya bude baki nayi magana ba, sai kuka na daya karu sosai, ganin duk mutanen wajen sun juyo suna kallon mu yasa Dpo yace mu koma office din sa. Alhaji Marwan da Kamal sun shiga tunanin abinda ya hada mu, saboda haka muna shiga ciki Alhaji Marwan yace

“Me yake faruwa ne Kb? Ka santa ne? Ko shi yasa nake ji kamar na taba ganin ta tun shigowa ta wajen nan.”

“Matar Farouk fa, wadda muke maganar ta ranar da Dadah.”

“Ikon Allah.”

Yace yana bi na da kallon tausayi, kamar an mintsini Daddy yayi saurin cewa

“Yarinyar da ta bata… Menene alakar ki da ita?”

” ‘Yata ce!”

Na amsa kai tsaye ina sake sakin wani sabon kukan, tashi yayi yana zagaye dakin hankalin sa a matukar tashi, kenan da gaske bayan rabuwar su Da Farouk ta haifi abinda ke cikin ta har ma ta girma, idan haka ne yarinya ce wani tsani na warwarar wasu daurukan da har yanzu ya gaza warware su.
Da wani irin sauri ya mika hannu ya karbi wayar dake hannun Alhaji Marwan, kai tsaye ya shiga jerin sakonni ya fara dubawa, a kan sakon ya tsaya yana sake dubawa duban tsanaki, “abin da sukayi tarayya akai, ba tare da sanin su ba…”

“MD!” Ya kira shi da d’an karfi

“Yarinyar Farouk ce, ita ce ake magana a wannan text message ɗin, waye shi? Me mukayi masa da yake son ganin bayan mu?”

“Kana nufin abinda text ɗin ke nufi kenan?”

“Eh duba kaga, ya zama dole mu nemo shi ko waye, shine yake da amsar dukkannin tambayoyin mu.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button