DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru nayi lokaci daya naji kukan ya dauke min, nauyin dake lullube a zuciya ta naji ya soma raguwa a hankali, sai dai ido na daya ke min wani irin zugi kamar na zuba masa yaji, su kadai yanzu suke maganar su sai Kamal daya zuba ido baya fuskantar komai, ni ɗin ma ba wani fuskanta nake ba, sai dai tabbas akwai wata kullaliya da ta saka aka sace min yata, kenan akwai me bibiyar rayuwa ta har bayan barin kauyanmu. Amal ce ta fado min, da ita kadai na taba haduwa har ta nuna min babu wata alaƙa tsakanin mu, ance zato zunubi sai dai a take zuciya ta ta shiga ayyana min ko tana da hannu a cikin batan Iman?
A kofar gidan Driver ya ajiye ta, fuskar ta sanye da bakin glass, ta sakala earpiece a kunnenta da alama waya take amsawa, sai data gama amsa wayar sannan taja jakar kayan ta ta shiga gidan, da mai aikin Dadah suka fara karo, bata ko bi ta kanta ba tayi hanyar falon tana yatsine, da gudu da fada jikin Dadah tayi saurin ture ta tana matsawa gefe
“Yar nema karki karya ni.”
“Nayi missing dinki ne Dadah.”
“Naji, tare kuke da Baban naku ne? Yayi min waya sun shigo garin tun dazu nake baza ido.”
“Wai Daddy, ban masan yana nan ba, sai anjima kila idan ya gama abubuwan da ya kawo shi.”
“Haka ne, ya mutanen gidan ya kowa da kowa?”
“Lafiya wallahi, bari n huta nazo naci abinci dan yunwa nake ji.”
Ta mike tana jan jakar ta ta nufi daki.
Sai da suka gama komai sannan muka fito, Daddy ne ya dubi Farouk yace
“Kasan gidan Dadah ko?”
Soso kai ya hau yi yana kallon Alhaji Marwan, da sauri yace
“Yanzu duk zaman ka garin nan baka taba zuwa ba?”
“I’m sorry Dad.” Yace yana matsawa dan yasan sauran bayanin
“Toh sai ku biyo mu a baya, chan zamu wuce Aminatu, ba zan iya bawa Dadah labarin da nake so na bata ba tare da ta ganki ba.”
Amsawa nayi da toh muka bi bayansu zuciya ta na wani irin bugawa ina jin tsoron abinda zan tarar.
Sanye yake da dogon wando da riga longsleeve ya nade wuyan sa da abu mai kauri, hannun sa rike da Amir karamin dan uncle Aliiyu, bayan sa rataye da Jacket ɗin sa daya zare tun da suka ido Nigeria, cikin kankanin lokaci suka gama komai a airport dib suka tari cab kai tsaye suka nufi gidan Dadah bisa umarnin Uncle Aliiyu.
Kallon ko ina yake babu abinda ya sauya a dan tafiyar da yayi, kai tsaye unguwar suka shigo daidai lokacin da motar su Daddy ta tsaya a kofar gidan, runtse idon sa Farouk yayi yana tuno abinda yasa shi barin kasar gashi ya dawo dashi ba tare da sanin yadda zai tunkari mutanen da suka zama masa wani jigo na rayuwa ba.
Two hearts are about to reunite????️????️????️????️????️????️????️????️
idan kun shirya nima na shirya, let the game begins ????????????????
Idan na samu chargy zaku jini anjima. Manage dis wayata 3%DG
33
★★★★★
Tun kafin su k’arasa suka fito, Daddy ne a gaba Alhaji Marwan na biye dashi, sai kuma motar Kamal da ke tsaye a bayan tasu Daddyn, wani irin farin ciki ne ya lullube Uncle Aliiyu ganin mutanen da yake da muradin gani tsawon lokaci.
Rufe ido Farouk yayi ya kwanta sosai a jikin kujerar motar, a daidai lokacin Kamal da Aminatu suka nufi cikin gidan, har suka gama fita daga motar be dago ba sai da Uncle Aliiyu ya tab’a shi, kamar ba zai sauko ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya fito yana kallon sararin samaniya.
Anty Safiyya ce a gaba yaran na binta sai Uncle Aliiyu da suka jera da Farouk yana mishi bayanin sauye-sauyen da ya gani.
A daidai lokacin Dadah na tsaye gaban fanfo tana daura alwala, da fara’a ta tarbe su maganar da take kokarin yi ta makale ganin wadda bata taba tunanin gani ba.
“Wa nake gani kamar Aminatu?”
Tace a dan kideme, tana matsowa inda nake tsaye kamar an dasa, tsananin farin cikin da nake ciki bazai misaltu ba.
Murmushi Daddy yayi
“Yau sai a bani tukwuici na ga Aminatu na kawo miki har gida.”
Kukan farin ciki ta saka ta rungume ni jikin ta, kukan da nake kokarin rikewa ya kwace min muka shiga yi a tare, a yau na kara tabbatar da kaunar da matar take min, kenan sun koma nema na bayan na bar kauyanmu, wannan shine soyayya ta gaskiya ba tare da wani abu ba.
Sallamar Anty Safiyya ta katse dukkan me shirin magana, duk suka zuba mata ido cike da tsantsar mamaki, takawa take kamar wadda take tsoron yadda zasu karbe ta. Har ta tsaya a gaban Dadah babu wanda ya iya furta komai, shigowar Uncle Aliyu, Farouk biye dashi kansa a kasa kamar baya son ganin kowa ya kara jefa su cikin rudani, saki na Dadah tayi tayi wajen Anty Safiyya bakin ta a bude, yaran dake gefen ta, ta shiga bi da kallo daya bayan ɗaya tana kallon fuskar mahaifiyar tasu.
“Kabiru me yake faruwa, wa nake gani kamar Aliyu, Safiyya da Babana? Ban gama dawowa daga mamakin ganin Aminatu…”
A rikice Farouk ya dago jin an ambaci Aminatu, a lokaci daya ya dira a gabana, idon sa cikin nawa yake duba na, cikin wani irin yanayi da bazan iya misalta shi ba, rawa bakin sa ya soma kafin da kyar ya samu nasarar furta kalmomin a rarrabe,
“De..s…ti..ny.”
Sai ya rike hannu na da sauri ya shiga jana yana kokarin barin gidan, Alhaji Marwan ne ya dakatar dashi ta hanyar rike shi, ya kuma bata rai sosai yana nuna masa ciki, daya bayan daya ya shiga bin mutanen dake tsaye a wajen kowa da kalar kallon da yake mana, sai kuma ya sauke idon sa akan Dadah dake kuka sosai, kukan daya sanyaya jikin kowa har aka rasa wanda zai iya cewa komai.
“Mu shiga ciki.”
Alhaji Marwan daya fi kowa karfin hali yace yana nuna masa hanyar falon, mai aikin Dadah ce ta rike ta muka dunguma zuwa cikin falon har lokacin hannun sa sarke yake da nawa, kaina a kasa na gaza kallon sa, wani irin yanayi ne ke shiga ta yana bin kowanne lungu da sako na magudanar jinin jikina.
A kasa muka zube tare yaki saki na kuma, idon sa akaina baya tuna duk mutanen dake falon da matsayin su gareshi.
Kan Uncle Aliiyu na saman cinyar Dadah yana share hawayen dake faman reto a saman fuskar sa, girma da shekarun sa basu hanashi zubar da hawaye a wannnan lokacin ba, domin yana bukatar hakan. Saboda haka babu wanda yayi yunkurin tsaida shi sai daya gaji dan kanshi ya zauna sosai yana duban dukkan yan falon.
“Na tabbata duk wanda yake gurin nan yayi mamaki ganin mu, bayan shudewar lokaci da ina kyautata zaton babu wanda ya sake tunawa da Aliyu da matar sa Safiyya, sai dai mu bamu taba kwana ba tare da mun tuna da ku ba, duk da ba wai ina tuhumar ku bane, hakan ya faru ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, haduwar mu da Farouk shine silar dawowar mu, wanda dama abinda muke jira kenan tsawon wannan lokaci da muka kasa dawowa din.”
“Kamar yadda kuka sani, ni Aliyu na bar gida ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, sai dai bani da zabi illa na tafi, dan a lokacin da na tafi bana cikin hayyaci na, ji nayi ba zan iya zama ba dole sai na tafi, da fari jihar fatakwal na fara yada zango duk da ba a bisa son raina ba, so nake kawai na bar kasar a lokacin, daga bisani Allah ya taimake ni na nemi gurbin karatu a jami’ar Cranfield dake birnin London, na samu, hakan ya saka na tattara na bar kasar ba tare da tunanin sake waiwayar kowa ba.
“Tafiyar da nayi da Safiyya ita ta taimaka min wajen tuna wanene ni, sanda na dawo hayyaci na hankali na yayi matukar tashi naji bana son sake kwana a kasar, bayan mun gama shirye shiryen komai ranar da zamu tawo na dan fita ina karasa siyan abinda zamu bukata na hadu da Adam, nayi mamakin ganin sa a kasar kuma ga dukkan alamu ba bakon kasar bane, take abinda ya faru ya dawo min, rai bace na tare shi zan soma magana yace