DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sako nazo baka, ka tabbata kai da barin kasar nan sai bayan cikar buri na, duk ranar da ka hadu da wani cikin mutanen dake da kusanci dakai, a rana zaka iya komai, sai dai ina maka albishir kai da haduwa da wani sai bayan ranka, kamar yadda kaso ka tona min asiri haka zaka kare rayuwar ka cikin kunci da dana sani.”
Juyawa yayi ya bar wajen ban iya ce masa komai ba, kiran daya shigo wayata na maida hankali wajen dauka, kukan dana ji Safiyya nayi yasa jikina ya hau rawa, a nan take sanar min da an shigo an kwashe komai da zamu bukata wajen barin kasar, hatta yan kudaden da suka rage mana an kwashe komai, tun daga lokacin bamu sake samun damar barin kasar ba, haka muka cigaba da zama a kasar muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan musibar.
Toh kamar yadda kowa ya sani, Adam ya mutu a idon duniya, amma yana nan yana yawo a doran kasa yana aikata mugayen abubuwa, ina fatan wannan bayanin nawa zai saka Dadah ta sanar da kowa wani boyayyen sirri da ta sani, wanda sanin dana yi ya jefa ni a matsala, amma kafin nan ina neman alfarma ya zama a gaban Anty Abidah, domin a lokacin nake so komai ya warware, ina son na cika mata burin alkawarin dana yi mata na wanke ta daga zargin da ake mata.”
“Kana nufin Adam yana raye?”
Daddy ya jeho masa tambayar kansa a daure cike da mamakin abinda Aliyun yace,
“Yana nan da ransa.” Ya amsa kai tsaye
“Ikon Allah.”
Ya dora
“Sai dai nasan yarda da hakan ba mai yiwu wa bane lokaci daya, ina bukatar lokaci dan tabbatar da haka.”
“Me akayi masa haka mai zafi da yake kokarin ganin bayan mu?”
Yace yana duban Dadah data sauke kanta kasa, murmushi Uncle Aliiyu yayi, ya kalli Dadah ya kama hannun ta ya rike cikin nasa
“Ki taimaka ki sanar da kowa abinda kika sani, ke ce mahaifiyar mu dukka, ke kika haife mu saboda haka karki ji tsoron komai babu abinda ya isa yayi miki sai abinda Allah ya ƙaddara miki.”
Kuka ta saka tana tuna abubuwan da suka faru, wanda take ganin kamar a lokacin suke faruwa ko kuma taso da maganar na iya saka komai ya kara tabarbarewa.
“Zan neme ku, kuyi hakuri yanzu.” Tace tana goge fuskar ta
“Shikenan Allah ya kaimu.”
Suka hada baki a lokaci daya, kallon Farouk Daddy ke tayi ganin yayi biris da kowa na falon kamar be san da zaman su ba, idanun Dadah na kansa haka ma Uncle Aliiyu na lura dashi tun zuwan su.
“Farouk!” Ya kirashi
Dagowa yayi yana duban sa cikin girmamawa yace
“Na’am.”
“Baka gaida kowa a falon nan ba, ina fatan baka manta su waye a zaune a gaban ka ba ko?”
Kwarjini yaji yayi masa, idan ba haka ba bashi da niyyar tanka kowa a cikin su, musamman Daddy Da Dadah, wanda yake ganin sun fi kowa rashin son shi bayan yana da yakinin su suke fi kusanci dashi. Bai manta abinda Dadah tayi masa ba, ya kuma kasa tantance a wanne matsayi zai ajiye ta, ganin da yayi mata a yanzu kawai yaji yana bukatar tuntubar ta akan abinda ta aikata masa, yana so yaji dalilin ta na yin haka, a darare kamar wani bako yace
“Fatan na sami kowa lafiya.”
Tsananin mamaki ya kama Daddy, ya gaza cewa komai sai Dadah ce da Alhaji Marwan suka amsa masa.
****Kiran sallar magriba yasa kowa ya mike domin gabatar da sallah, daki Dadah ta nuna min tace naje na yi alwala nayi sallah, ban mata musu ba sai dai ina so na tafi gida, nasan duk inda hankalin Baba Altine yake ya tashi yanzu, dan ma na sanar da ita in da na tafi ne.
Tana kwance na shiga dakin, ta ɗora kanta a saman pillow da alama bacci take kuma tana jin dadin baccin nata, kofar dana gani dake nuna alamun toilet na wuce ina tuna ranar dana hadu da ita da abubuwan data fada min.
Mik’ewa tayi jin wayar ta dake gefen ta nata vibration, ba tare da sanin ina ciki ba ta daga,
“Kina jina? Tashi maza ki duba min bakin da akayi a gidan, ki gani idan akwai Namiji Babba da matar sa da yara uku, yi maza ina jiran ki.”
“Toh…” Tace tana mik’a, mikewa tayi ta tsaya tana duba fuskar ta a gaban mudubi kafin ta fita, babu kowa a falon sai Amir da Amrah babban yabi su Daddy masallaci, kallon su tayi kallon su waye ku kafin ta wuce dakin Dadah ta leka, Anty Safiyya na kan sallaya tana sallah dake gefe Dadah na gabatar da tata sallar ita ma, dan jim tayi kafin ta juya zuwa dakin nata, bata lura dani akan abin sallah ba, ta dauki wayar ta ta kira shi
“Na duba, naga yara biyu a falo sai wata mata a dakin Dadah tana sallah.”
“What!” Yace cikin k’araji
“Da gaske kenan Aliyu ya dawo, Amma how comes?”
“Waye shi?” Tace tana zama
“Shine wanda ya raba ki da mahaifin ki tun kina tsumma, yanzu ma kuma zai sake wargaza min aikin dana jima ina yi, Amal so yake ya kashe miki uba ki zama marainiya gaba da baya, will you allow that?”
Da sauri ta girgiza kai
“Ba zan taba barin shi ba, nima ina bukatar uba kamar kowacce ‘ya.”
“Then zaki yi yadda nace?”
“Zanyi.” Tace kai tsaye
“Good girl, zan kiraki anjima.”
“Ok.” Ta ajiye wayar, wayun bakin tane ya makale ta hau murza idon ta da sauri, kallo na tayi, nima na zuba mata ido babu ko daukewa bayan na gama sauraron wayar da tayi zan iya alakanta hakan da maganganun da naji anayi dazu.
“Me kike yi anan, yaushe kika zo gidan nan, waye ya kawo ki gidan nan?”
“Wanne kike so na amsa miki aciki?”
Nace mata ina murmushi
“Ni na kawo ta!” Ya shiga takowa cikin dakin yana kallon ta, sake shiga rudu tayi da sauri tace
“Ya Farouk!”
Daga mata hannu yayi
“Karki kuskura, kinji na fada miki.”
Kasa nayi da kaina, ya iso gaban sallayar ya zauna yana tankwashe kafar sa, leka fuskata ya shiga yi, ganin naki yarda na kalle shi yasa shi sa hannu ya daga min fuskar.
“Gudu na kike Aminene? Nine Farouk dinki fa.”
Gefe na kauda fuskata ina jin zafin abinda yayi min a baya, na farko saki na biyu ƙaryata abinda yake tsakani na dashi, wanda shine Ummul aba’isin jefa ni cikin gararin rayuwa.
“Please dan Allah kiyi min magana, shekara nawa? Kinsan yadda na azabtu da rashin ki? Kinsan wacce irin rayuwa nayi bayan na rasa ki? Dan Allah kiyi min magana.”
Kamar tatsuniya haka nake jin maganar tasa, idan har abinda yake fada gaskiya ne me yasa ya rabu dani, yunkurawa nayi da nufin tashi ya sa hannu ya maida ni baya
“Wallahi baki isa ba, duk tsawon lokacin nan dana yi ba tare dake ba amma kiki cewa komai, haushi na kike ji? Me nayi miki?”
A zafafe nace
“Baka san abinda kayi min ba Ya Farouk? Baka sani ba? All this while ni kasan irin rayuwar da nayi? Why are you selfish? Shikenan nice me laifi saboda bani da gata balle galihu, daka tafi ka barni da ciki ka taba tunanin halin da zan shiga? Ka taba? Ka sake ni bayan ka koya min sonka, na shaku da kai na soka,amma nice abar tuhuma ko…”
Kuka ne ya taso min, na sake shi ina saka fuskata cikin cinyoyi na, be hanani ba, ina jin yadda numfashin sa yake kai kawo a saman kaina, tashi naji yayi, ya isa wajen da Amal ke zaune tana sharar kwalla yasa hannu ya fizgota ya dire ta a gabana
“Ki faɗa mata, ki faɗa mata komai da kula kulla ke da munafukan da suka tayaki, kin fi kowa sanin bani da laifi akan abinda take tuhuma ta, ki faɗa mata ko na kakkaryaki a wajen nan wallahi Allah.”
“Ni…ni bansan komai ba.” Tace cikin kuka, shaka ya kai mata ta shiga kakari, da sauri na shiga tsakani ina masa kallon mamaki
“Me kake yi haka? Dukan mace ya Farouk!”