DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Jin haka yasa shi sakin ta da sauri yana zama gefen gadon hannun sa rike gam da kansa, juyawa nayi na bar dakin da sauri, lokacin duk sun dawo suna zaune a falon, a gaban su Daddy na durkusa Ina share fuskata
“Zan tafi Daddy, dare yanayi.”
“Eh kuma haka ne, na manta shaf Aminatu, ina farouk sai ya maidake, duk da zanso ki dawo nan ɗin amma for now tunda munsan inda kike shikenan.”
“Aminatu.” Dadah ta kira sunana, matsawa nayi gaban ta ta kamo hannu na
“Naji abinda ya faru, in Sha Allah za’a ganta, ki cigaba da addu’a kinji, sannan zaki dawo waje na zanzo da kaina har inda kike, kiyi hakuri kinga abinda kika tarar karki ga ban baki lokaci ba.”
“Babu komai.” Nace ina musu sallama, har waje ta rako ni kafin ta koma ciki.
“Wai kinsan matsalar idon ki amma kike ta kuka haka, me yasa?”
“Kamal dole nayi kuka, yanzu muje kawai zan maka bayanin komai ko a waya ne, Baba Altine na chan na jira na.”
“Shikenan.” Yace yana bude min motar, shiga nayi ya tayar muka tafi. Muna zuwa kofar gida na ga motar Ya Anas a ajiye da alama yana ciki kenan, fitowa nayi na masa sallama ina shirin shiga gidan najii yace
“Kinyi mantawa fa a bayan mota.”
“Mantuwa?” Nace ina kallon shi
“Zo ki duba ki gani.”
“Ni da ba idon kirki ba, duba min menene?”
“Ki zo dai ki duba.” Yace yana kunshe dariyar sa, hararar sa nayi na dawo na bude bayan motar na zura jikina sosai a ciki, ji nayi an jawo ni gaba daya ciki, har glass din idona na nemam faduwa nayi saurin rike shi, fuskata daf da tashi har ina iya jin sautin fitar numfashin sa
“Kina tunanin zaki guje min ko?”
Kokarin kwace wa na hau yi ya rik’e ni gam, baki na bude zan sa kuka yayi saurin sa hannu a saman bakin nawa
“Kina kuka sai na baki mamaki wallahi.”
Da sauri na hadiye kukan, ya sake ni nayi saurin fita daga motar, fitowa yayi shima ya leka yace
“Kanina zaka iya wucewa ni sai gobe.”
Dariya Kamal ya saka yaja motar sa ya bar layin
“Muje ko?” Yace yana kallo na, kasa daga kafata nayi saboda tunowa da nayi Anas na ciki, ganin naki motsi yasa shi kama hannu na ya shiga jana har cikin zauren gidan
“Shiga zakayi?” Nace ina tsayawa ganin da gaske ciki yake son tura kansa
“I want to see my daughter dan jikina ya bani baby girl kika haifa min, baki da right na hanani ganin gudan jinina kuma.”
Ya cigaba da jana, da karfi nasa na fizge hannu na ina sa masa kuka
“Ohh shit.!” Ya dawo baya yana duba na
“Kina so idon ki ya kara ciwo? Naji kamal na miki maganar ido.”
Cikin shassheka nace
“Anyi kidnapping Iman, an kuma bata min ido na, bansan inda take ba.”
“Me!!!!!” Yace yana zaro ido waje, girgiza ni ya hau yi da karfi
“Tell me wasa kike min dan Allah.”
Sai kuma yasa hannu ya shiga shafa saman ido na
“Me yasa na tafi? Me yasa ban kara jira ba, menene amfanin rayuwa ta!”
Yace a rikice yana jawo ni jikin sa, da sauri na fada ya saka hannu ya rungume ni sosai yana kokarin boye hawayen sa.
“Waye Anan?” Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa.
Hello mutanen arziki, I’m sorry for yesterday duk da dama nace idan na samu chargy zaku jini.
Ga wata yar tambaya zuwa ga malaman zafafa
“Wai shin idan namiji ya saki matar sa ba tare da sanin sa ba, shin ta saku ko kuwa? Menene hukuncin sakin da Farouk yayi wa Aminatu a littafin DG? Shin ta saku tun da da kansa ya rubuta sakin duk da baya cikin hayyacin sa, kuma ba da gangan ya sha abinda ya gusar masa da hankalin ba, ko kuma bata saku ba?menene hukuncin hakan a musulunce. Nasan muna da manyan malamai cikin mu.
I ll be reading ur comments.
Nagodea: DG*
34
★★★★★
“Waye anan?”
Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa, da sauri nayi kokarin janye wa daga cikin sa amma sai yaki, ya sake kankame ni yana duban Ya Anas
“Baka iya sallama bane ko me?”
Wani banzan kallo Ya Anas yayi masa yana matsowa ransa na matukar suya da abinda ya gani, Aminatu rungume jikin wannan gardin, be taba tunanin ta a irin wannan yanayi ba, yana zuwa yasa hannu zai raba su Farouk ya nuna shi da yatsa yana maida ni gefe
“Karka kuskura kasa hannun ka jikin matata wallahi.”
“Matar ka? Idan naki fa? Iskancin ya kai har ka biyo ta cikin gida saboda tsabar rashin mutunci ko?”
“Waye wannan?” Yace cikin bacin rai
“Ya Anas ne!” Na furta a dan tsorace dan duk na gama tsorata da yanayin sa
“Ya Anas, me yake anan? Me ya kawo shi?”
“Baka da bukatar sanin abinda ya kawo ni.” Yace yana duban shi, sai kuma ya dube ni rai a bace yace
“Zo ki wuce ciki.”
Ina kokarin daga kafata naji Ya Farouk ya rike ni
“Don’t you dare, idan kika daga kafarki anan wallahi sai ranki yayi mugun ɓaci.”
“Idan kai ka haife ta ba? Sai ka hanata, zo ki wuce kafin kiga fushi na.”
A hasale na dakatar dasu ganin suna neman charja min kai, cikin kuka nace
“Dan Allah ku kyale ni da abinda yake damu na, ku dukka kuna da dama a kaina, dan haka babu wanda zan wa abun da yake so na bar daya.”
“Ya Farouk wannan shine Ya Anas, mutumin da ya tallafi rayuwa ta ya dubi maraici na ya rik’e ni tsakani da Allah dani da ‘yata.”
“Ya Anas wannan shine Ya Farouk, tsohon miji na kuma mahaifin Iman.”
Tana kaiwa nan tayi saurin fadawa ciki tana rufe kofar da zata sadaka da zauren gidan, da sauri Anas ya fice daga gidan ba tare da ya sake duban inda Farouk yake tsaye ba kamar an dasa shi.
Iska me matukar zafi ya furzar yana sake kallon gidan maganganun ta na masa yawo a tsakar ka, kenan tana nufin bata da alaka dashi a yanzu kenan? Da kyar ya iya jan kafafun sa ya kai kansa bakin titi ya tari abin hawa ya wuce gida.
A zaune ya tarar dasu dukan su, magana suke a tsakanin su, kai tsaye dakin daya saba sauka ya wuce yana jin kansa na matukar sarawa.
Har ya kwanta ya tuno da Kamal, dakin daya san zai same shi ya wuce kai tsaye, yana kwance yana kallon wani video a wayar sa yaji an turo,tashi yayi ganin Ya Farouk yasa shi dan sosa kai yana murmushi
“First time na kwanan ka gidan nan right?”
Daga mishi kai yayi yana dariya
“I see.”
Sai ya mika masa waya
“I need her number please.”
“An gama.” Yace yana dariya, karba yayi ya saka masa, yayi godia ya juya ya koma in da ya fito.
Sai daya fara duba jakar sa ya ɗan samu cookies yaci sannan ya kuskure bakin sa ya kwanta yana kashe komai na dakin.
Aminatu na kwance ta rasa me yake mata dadi kiran sa ya shigo, kamar kar ta tashi haka take ji saboda yadda ko ina na jikin ta ke mata ciwo, ga wani irin ciwon kai me tsanani daya addabe ta tun ranar da aka rasa iman, duk da tana ji a ranta yarinyar ta na nan da rai sai dai hankalin ta ya gaza kwanciya musamman data fuskanci kamar akwai wata rigima data shafi Daddy da wanda ya dauke tan, da tunanin ta masu garkuwa da mutane ne su nemi kudi, sai dai a yanzu ta tabbatar wani game ne ake so a buga da rayuwar yar ta.
Tun tana kuka da hawaye ta dawo na zuci, ta dukufa fadawa Allah dan shine kadai zai iya kawo mata dauki a cikin halin da take ciki.
Ganin me kiran da gaske yake yasa ta lallaba da kyar ta jawo wayar, bata iya ganin me kiran ba saboda babu glass a idon ta, saboda haka daga kawai tayi tana maida kanta saman filon data tashi.
“Assalamu alaikum.”
Tayi sallama a hankali, shiru ya biyo baya ta sake maimaita sallamar karo na biyu, jin babu alamun amsawa yasa tayi yunkurin kashe kiran yayi saurin katse ta