DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Karki kuskura ki kashen waya wallahi.”
Zare wayar tayi daga kunnen ta, ta kalli saman screen din kafin, kafin ta maida kunne ta
“Tell me, me ya sami ‘yata,wanne progress aka samu neman ta “
“Ban sani ba nima, su Daddy ne akan case din.”
“Yasan yarmu ce?”
“Ya sani jiya.”
Ajiyar zuciya ya sauke da karfi
“Me yasa kika ki jin magana a gaban trash din nan, kinsan yadda maganganun ki sukayi hurting din na?”
“Uhum “
“Kiyi hakuri.” Yace murya a kasa, bata amsa ba ya sake cewa
“I’m sorry for everything.”
“Uhum.”
“Talk to me Dan Allah, ki min masifa ma if you like, in ma duka na zakiyi ki dake ni idan zai sa ki hakura.”
“Iman.” Tace muryar ta na rawa
“Taci abinci? An mata wanka? Lafiyar ta lau, She’s just a child ya kake tunanin zata iya coping without her mother,abinda ya damen kenan Please Farouk!”
Ta fadi sunan sa kai tsaye, tashi yayi zaune zuciyar sa na zafi yace
“Nayi miki alƙawarin dawo miki da ita sound and in a good health, karki manta ‘yata ce nima, responsibility nace ba tasu Daddy ba, zanyi duk yadda zanyi.”
Kukan ta na ya kara tsananta ya dafa kansa yana daidai ta zaman sa sosai
“Tell me anything da kike tunanin zai bani hint wajen neman yata, fada min komai.”
Shiru tayi tana nazari, chan Amal ta fado mata da wayar data ji tana yi dazu
“Adam, shine first suspect yanzu duk da bansan takamaimai alakar su da Daddy ba, Ina tunanin game ne yake so yayi playing da su, yasan wace ni yasan alaƙa ta daku tsawon lokaci yana bibiyata.”
“Sannan…” Sai kuma tayi shiru
“Sannan me?” Yace
“Amal, naji jiya tana waya, ban yarda da wayar da take ba.”
“Will you be my personal lawyer?” Yace yana murmushi
Murmushin tayi kadan tana runtse idon ta
“I love everything about Aminene ta.”
Yace yana jan numfashi, wani iri taji ta sake danna kanta sosai a saman filon data ke kai, tana jin sautin fitar numfashin sa a hankali.
“Goodnight, kiyi mafarki na da Iman mun saki a tsakiya kinji?.”
Daga kai tayi kamar yana ganin ta ta ajiye wayar tana lumshe idon ta.
File din ta dake kusa da ita ta daga filon tasa ba tare da ta buda shi ba kamar yadda tayi niyy.
Yana ajiye wayar ya shiga zagaye a dakin, badan dare ba sai yaje dakin Amal. System ɗin sa ya ciro cikin kayan sa ya kunna ta, e-mail ɗin da akayi masa wajen 3days back yaja hankalin sa sosai, a tsanake yake bin komai yana gid’a kansa cike da tsananin farin ciki
Kukan da take ne ya katse sakamakon wayar ta data dauki suwwa,da bayan hannun ta ta goge fuskar sannan ta daga tana karawa a kunnen ta.
“Baby kina jina? Karki bari asan muna waya dake, zan dan daina kiran ki kwana biyu amma ina so kizo address din da zan turo miki akwai abinda nake so na baki kiyi min wani aiki akai kinji?”
“Toh.” Ta amsa a cunkushe
“Me ya faru?” Yace jin muryar ta a shake
“Ba komai.”
Tace tana kashe wayar, ba’a jima ba text message ya shigo, bata bude ba ta cillar da wayar tana kwanciya a kasa, babu abinda yanzu take bukata face ace auren ta da Ya Farouk na nan, ganin Aminatu da tayi yau ya kara dagula mata lissafi. Kishin ta take sosai kamar zata mutu. Da kyar ta samu bacci barawo ya sace ta ba tare da ta shirya ba.
Da safe ta tashi a makare idon nan duk ya kumbure, tana jin maganganu a falon tayi tsaki ta fada toilet, wanka tayo tazo ta gyara fuskar ta kafin ta duba text message ɗin da yayi mata, duba address din tayi ta ajiye ta karasa shiryawa ta fito falon.
“Idon ki kenan Amal? Duk jiya baki ji alamun akwai baki gidan nan ba?”
Dadah ta tuhume ta cike da mamaki
“Na shigo da magriba kuna sallah, bacci nayi da wuri kinsan na kwaso gajiya.”
“Okey yayi kyau, baki ga bakuwa ba?”
“Ina kwana?” Tace a gajarce
“Lafiya lou.” Anty Safiyya ta amsa kafin tace
“Girma ba wuya Amal an zama yan mata.”
Haushi ne ya kama Amal ta tashi ta koma daki ta zauna tana tunanin yadda zata fita ba tare da kowa ya gane ba.
Duk tunanin ta ya tsaya ta rasa ya zatayi gashi daga ganin alamun zaman da Dadah tayi a falon babu ranar tashi.
Curtains ta yaye jin alamun za’a ta da mota, Kamal ne tsaye suna magana da Farouk, jingina tayi da bangon tana kare masa kallon tsaf, zuciyar ta bata san komai ba sai soyayyar sa, yayi kyau ya sake mirjewa kamar bashi ba. Ganin ya juyo yasa tayi saurin sakin labulen tana sauke ajiyar zuciya.
Cigaba tayi da tunanin mafita har zuwa sanda ta sake jin maganganu sun sake karuwa a falon
Alamun taba kofar dakin taji kafin tace wani abu ya budo ya shigo kai tsaye.
“Come out!”
Yace daga bakin kofar kafin ya juya, hadiye yawu tayi da k’yar ta tashi kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta fito falon. Daya bayan daya ta shiga raba idanun ta tana binsu d kallo, kafin ta shiga jan kafar ta isa gaban su tana zama kasa. Daya Daya ta gaishe dasu Daddy zuciyarta na cike da tsoron kiran da aka mata
“Ina wayar ki?”
Ya Farouk ya mika mata hannu alamun ta bashi, gaban tane ya fadi ta hau rawar jiki. Daka mata tsawa yayi data firgita ta tayi saurin miƙa masa wayar, kai tsaye call log dinta ya fara shiga ya duba numbers din datayi waya da call duration kafin ya fita ya shiga messages, da sakon shi ya fara cin karo ya yi shiru yana karanta sakon, tabbas hasashen da Aminatu take gaskiya ne, Amal nada masaniya akan komai, number ya dauka akan wayar shi da message ɗin ya isa gaban Alhaji Marwan ya mika masa wayar yana komawa wajen zaman sa.
“Menene dalilin tara mu da kayi anan Farouk?”
Alhaji Marwan yace yana kallon wayar Amal din ba tare da ya duba ba.
“Daddy ka rike wayar ko da za’a kira, ina da maganar da zanyi kafin a gangaro maganar wayar.”
“Toh muna jinka.”
“Da farko dai ina neman yafiya a bisa laifin dana aikata na tafiya na bar kasar,hakan ya faru ne a bisa dalilai na da nake ganin sun kai na zartar da komai. Sai dai ni kaina bani da masaniyar takamaimai abinda ya faru, tun bayan da ƙaddara ta haɗa ni da Aminatu har aure ya shiga tsakanin mu zuwa sanda na bar gari zuwa wani aiki da dawowar da nayi na tarar da mugun labari da bani da masaniya akai.”
“Naso kwarai Daddy ya bani dama ko sau daya na kare kaina amma hakan be samu ba, a dole na tsananta bincike anan ne na gano akwai hannun Amal a cikin abinda ya faru daya jawo rabuwa ta da Aminatu.”
“Na kirata na tuhume ta da laifin dana kamata dumu dumu na kuma bukaci na ji wanda ya sakataa, to my surprise sai gashi ta kira sunan mutanen da nafi kusanci dasu, Dadah da Ja’afar wanda duk duniya ina ganin idan akwai wanda na yarda dasu toh su biyo bayan su,wannan dalilin shi yasa ni tafiyar dole dan bazan iya zama ina kallon su da abun ba.”
“Innalillah wa inna ilaihi raji’un.”
Dada tace tana kallon Amal kallon tsantsar mamaki.
“Muna sauraron ka.” Uncle Aliiyu yace
“Na tafi da clip din da aka dauka lokacin da nake rubuta sakin da kuma voice recording din da akayi lokacin da aka kirani a gaban kowa dan a tambaye ni dalilin abinda na aikata. Da fari na shiga rudani sosai dan bani da hujja da zan ƙaryata hakan, na farko dai murya ta ce gata nan, na biyu ni ne zaune ina rike da takarda da biro.”
“Tsawon lokacin nan nayi shi ne cikin binciken yadda akayi hakan ta faru, ban samu ba, haka na hakura na bar wa Allah komai. Sai gashi jiya cikin hukuncin Ubangiji mutumin da ya taimaka min kwarai wajen bincike na yayi min e-mail inda yake tabbatar min da duk abin da yake cikin clip din da kuma abinda yake a recording din nan shiryayye ne anyi amfani da lastest technology da wasu set of intelligent agencies dake ƙasar Amurika ke amfani dashi wajen sauya abin, yana so na tsananta tunani na gano abinda ya faru a rana makamanciyar da abin ya faru.”