DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ina Farouk?”
Shiru babu wanda yayi magana, a fusace ya sake tambaya cikin daga murya sosai. Da sauri har suna hada baki suka ce
“Sun…sun fita da Dada da Amal.”
” Ina suka tafi da sassafe haka bayan kuma ku da alama ko dukkanku tashin ku kenan.”
“Asibiti suka tafi kai wata yarinyar.”
Dafe kansa yayi ganin zancen na fitowa.
“Da yaushe suka tafi?”
“Jiya da daddare.”
Zama Dada tayi tana jiran Amal ta idar da sallah, Farouk na zaune a kan kujerar dakin yayi nisa a tunani, shi kadai yasan me yake tunawa, alluran da ya kamata ayi mata duk anyi mata. Tana idar wa ta tashi ta je gaban gadon tana kallon ta
“Ya Farouk ta samu sauki ko?” Ta tambaya tana nuna masa ita. Daga mata kai yayi yana murmushi
“Amma mene sunan ta?”
Girgiza mata kai yayi alamar shima be sani ba, murmushi tayi tana sake kallon ta.
“Ina son ta da kawa, me kyau kamar ta cikin cartoon din nan.”
“Tashi zakiyi mu tafi ba surutu zaki tsaya yi ba.”
Sai kuma ta maida kallon ta wajen Farouk
“Kai ma tashi zakayi muje, idan yaso sai a nemi iyayen ta a sanar musu suzo dan yanzu nasan hankalin su a tashe yake.”
“Da wai sai na zauna da ita har suzo ɗin, kinga be kamata a bar ta ita Kadai ba.”
“Farouk!” Ta bude idon ta sosai
“Baka da hankali ko? Kasan abinda hakan zai haifar? Lallai kai yaro ne.”
“Dadah ki barmu anan nida Ya Farouk dan Allah, kinga idan ta tashi bata ga kowa ba zatayi kuka.”
“Toh uwar iya, wallahi tashi zakuyi mu tafi, ba zan iya da matsalar da zata taso ba, na riga nayi magana da wata nurse zasu shigo suna dubata har suzo iyayen nata.”
Kamar ya fashe da kuka haka yaji, shi be ga dalilin da zai sa Dada tace sai sun tafi ba, gashi idan ta kafe babu abinda zai sa ta hakura, tashi yayi tsam yana kallon gadon kafin ya juya ya fice da sauri. Kwafa tayi ta ja hannun Amal suka fito, a tsaye ta hango shi tare da Dr Iman suna magana, karasawa tayi wajen
“Dr Barka da safiya.”
“Yawwa Mama, ya me jiki?”
“Alhamdulillah, mungode Allah.”
“Allah ya kara sauki, zan shiga sai na duba jikin nata.”
“Ok Dr, nima zan dan je gida ne na dawo.”
“Ok yayi,ka same ni a office idan na gama round zan yi magana da kai, amma yanzu ka koma dakin karta farka taga babu kowa.”
Ta fada tana yin gaba,kallon Dada yayi yana marairaice fuska, ganin yadda tayi kicin kicin da fuska.
“Sai ka zauna ai dama abinda kake so kenan, amma wallahi Babana ina ji maka tsoron abinda zai je ya dawo, ba fata nake ma ba, amma baka san halin mutanen mu ba.”
“Babu abinda zai faru sai Alkhairi Dada.” Ya fada cikin gamsuwa.
“Shikenan, Allah yasa.”
“Amin.” Yace yana murmushi.
“Zan tsaya wajen ka Yah.”
Kama bakin sa yayi da sauri yana kallon Dadan, tsaki tayi ta juya tana mitar sun raina ta.
Ciki suka koma da sauri, har lokacin bata tashi ba tana sauke numfashi a hankali.
Zagaye da hannayen sa yake kaiwa da komowa, wani irin tashin hankali me matukar girma yake hasasowa idan har abinda yaji ya zama gaske, ya zaiyi? Da wacce fuskar zai kalli mutanen kauyen. Tabbas idan hakan ta kasan zai dauki mummunan mataki akan Farouk, baya fatan zargin sa ya zama gaskiya dan zai iya yafe shi ba ma a cikin yayansa ba, a cikin dukkan ahalinsa. Duk kuwa da dimbin soyayyar da yake masa duk cikin ya’yansa.
Jin tsayuwar mota yasa ya juyo da sauri yana kallon gate din da tun zuwan sa yake tsaye wajen ya rasa me zaiyi. Idanun sa akan gate din har aka gama budeshi. Ganin motar gidan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, duk da baya hango cikin motar amma yasan sune suka dawo, a yau da ace ba tare da mahaifiyar sa suka tafi ba be san abinda zai iya aikata mishi ba, sai dai dole ya saita kansa yaji komai a baƙin ta. Hannun sa ya harde a kirji yana jiran daidaituwar motar da yake ganin kamar da gangan driver yake lankan jin ajiye ta a mazaunin ta.
Dada ce ta fito tana me kallon harabar gidan cikin tarardadin abinda yake faruwa, farko mutanen da ke waje tsaye kamar masu jiran a fito musu da gawa su kaita kushewa, sunyi kungiya kungiya suna tattaunawa, yanzu kuma tsayuwar Janar a harabar gidan ya kara tabbatar mata da abinda take tsoro take gudu ne ya faru. Jiki a sabule irin na wanda yayi fama a filin daga ya isa gareta kafin ta ƙaraso.
“Dadah.!
Ya furta muryar sa a bude sosai me nuna yanayin da yake ciki.
“Muje ciki.” Ta fada tana kallon sojojin da sukayi dafifi a wajen suna tsaye cikin jiran cika umarnin uban gidan na su. Be musa ba, sai jan kafar sa da yayi da tayi matukar sanyi yabi bayanta.
Ajiye mayafin ta tayi ta zauna tana daidata nutsuwar ta, dan tabbas ta hango tsananin tashin hankali da firgici a idon yaron nata, kasancewar sa babban soja hakan be sashi zamaar mata tamkar yaron goye a duk sanda yake tare da ita ba. Tabbas haka Farouk yake, a duk yayansa shine ya biyo shi, babu abu daya daya bari nasan tun daga dabi’a da yanayin yadda yake daukar a’alamri, abu daya tasani shine Farouk yana da sanyin zuciya da saurin yarda da komai, banbancin sa da mahaifinsa kenan wanda ya kasance mutum me tsauri sosai da rashin yarda a duk sanda abu ya gifta tsakanin ku, duk yadda kake dashi zai bar ka, barwa ta har abadah kamar yadda suka rabu da mata mafi soyuwa a gareshi bisa babban kuskuren data aikata masa.
Ruwan da aka ajiye a gaban ta ta kalla tana kallon Ja’afar daya kawo ruwan. Dauka tayi ta zuba ta mika masa.
“Sha ruwa Muhammadu, ko zaka ji saukin zuciyar ka.”
Karba yayi ba tare da yayi magana ba ya kafa kai ya shanye tas yana ajiye kofin.
“Me yake faruwa?” Ta wurgo masa tambayar tana nakaltar nazarin sa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi magana cikin dakiya
“Ni kaina na rasa me yake faruwa, zuwa na kenan, na tarar da wannan tashin hankalin, shin da gaske ne abinda mutanen garin nan ke tuhumar Farouk?.”
“Me suke tuhumar shi akai? Maganar yarinya ne ko?”
Ta fada kai tsaye dan tasan kwanan maganar kenan.
“Eh ita Dada, suna zargin Farouk da yi wa yarinyar su fyade sannan kuma ya sace ta, wannan wanne irin tashin hankali ne Dada.”
Shiru tayi tana maimaita innalillah wa inna ilaihi raji’un a ranta, abinda take gudar wa Farouk kenan, ya kasa ganewa.
“Dadah dan Allah, ina ya kai yarinyar, kuma shin da gaske abinda suke zargin sa akai ya aikata?”
“Yarinya dai tana asibiti dan yanzu ma daga chan nake, kuma tabbas yazo da yarinya a cikin mayuwacin hali, kuma nayi magana dashi na tambaye shi idan shine ya aikata mata, yayi mun rantsuwar dan musulmi bashi bane.”
“Shikenan, Farouk ya gama dani.”
“A ah kar kayi saurin yanke hukunci, ka tsaya kaji ta bakin nasa.”
“Haba Dadah, yaran yanzu fa sun wuce tunanin mutum, kuma ba’a shaidar su sam, dan wanda kake ganin ba zai aikata abu ba yafi aikatawa.”
“Yanzu menene abinyi?”
“Tashi zanyi naje asibitin, gani gashi ga iyayen yarinyar, harda maigari ma.”
“Shikenan, amma kabi komai a sannu.”
Shigar su dakin yayi daidai da sake farkawar ta, a dan tsorace take kallon su, kafin ta maida idon ta da sauri ta kulle su gam. Amal ce tayi saurin karasawa wajen gadon ta rik’e hannun ta, jin an rik’e ta yasa ta bude ido ta sauke su akan ta.
“Ya sunan ki?” Amal ta tambaya dan ta matsu tasan sunan ta.
“AMINATU!”
Da sauri ya juyo, sosai yaji sunan nata har cikin ransa, sauti da amon muryarta ya shiga masa amsa kuwwa, yana jin Amal na fada masa sunan su daya tana murna ya kasa amsa mata, sai ma binsu da ido kawai da yake yi kamar be san me yake faruwa ba.