DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Tsawon daren jiya ban runtsa ba ina tunanin abubuwan da suka faru, tunani na ya dawo nan take sanda nake tuna tabbas Amal ta kawo min abu nasha a ranar sannan munyi hira data shafi Aminatu tana min tambayoyi ina amsawa sannan tabbas ranar ina rubutu ne ta tarar dani, wannan abubuwan su aka juya aka sauya zuwa komai, ba dani aka yi waya ba sai dai tabbas murya ta ce,magana ta ce aka hada yayi daidai da abinda Daddy zaku tuhume ni akai.”
Murmushi yayi me ciwo yana janyo system ɗin sa ya tura ta gaban Daddy kafin ya dora
“Ina fatan wannan shaidar kadai ta isa ta wanke ni daga zargin da ake min sannan ina so ta fada a gaban kowa gaskiyar abinda yake faruwa. Me yasa lokacin dana tuhume ta ta nuna min tabbas na rubuta takardar kuma bana hayyacina, me yasa ta boye min gaskiya ta sake nisanta ni da matata da yata, me nayi mata haka mai zafi ta na chanchanci wannan?”
“Annamimiyar Allah!” Dadah tace tana saka kuka, kukan Amal take sosai itama ta kasa cewa komai, girgiza kai Daddy yayi cikin yanayi mara daɗi yace
“Adam yayi amfani da yarintar ta ya bata mata tunani.”
Wayar ta Alhaji Marwan ya duba kafin ya mika wa Daddy shima yaga text message ɗin
“Amal me yasa ki aikata haka?”
“Daddy kayi hakuri.”
“Tell me, zan saurare ki, me yasa? Saki yayi ko? Me yace miki?”
“Daddy ni tausayin sa nakeji, babana ne, ina son sa yace kuma kashe shi zakuyi tunda kai soja ne.”
“Haka yace miki?”
“Eh.”
“Shikenan daina kuka, mesa zamu kashe shi, ba haka bane kinji? Shiryawa zamuyi dashi mu nemi gafarar sa laifin da mukayi masa, can you help us?”
Shiru tayi tana tunani, kallon fuskar Daddy take, babu alamun karya a maganar sa, bayan haka ma be taba musu alkawari ya saba musu ba komai shi yake musu, sai ta samu kanta da daga mishi kai.
“That’s my girl, bata wayar ta MD, text him kice kina hanya kinji? Kije ki gan shi babu damuwa.”
Kallon sa tayi ya dage mata kai cike da gamsar wa
“Kije Allah yayi miki albarka, karki sanar dashi munyi maganar nan a waya sai kinje yanzu text kawai zakiyi masa.”
Tashi tayi tana goge fuskar ta ta wuce daki.
“Me hakan ke nufi?”
A cewar Uncle Aliyu
“Shine kawai mafita, bin ta zamuyi dole sai an kama Adam a hannu komai zai warware.”
“Lallai akwai banbanci, na kara tabbatar da kai din jami’in tsaro ne, kudos.”
Duk sukayi murmushi banda Farouk da yake kallon su kawai.
Kiran wayar ta ya fara yi bata daga ba, kai tsaye ya shiga gidan bakin sa dauke da sallama, shiru gidan lokacin Baba Altine ta shiga makota siyo koko, Aminatu na toilet tana wanka saboda haka bata ji shigowar sa ba, sakon da Ya Farouk ya bashi ya ajiye a gefe yana kallon falon, idon sa ne ya sauka akan file din dake yashe a kasa, garin sauri ta manta ta dauke filon bata dauke shi ba, kamar kar ya taba sai kuma yaji yana son ganin date of birth din ta ganin file ne na asibiti.
Kai tsaye yasa hannu ya dauka, sunan asibitin dake rubuce a saman file din dayayi daidai da irin sunan dake jikin birth certificate d’insa shi ya kara jan hankalin sa, murmushi ya saki yana jin dadin ganin ashe ma asibiti daya aka haife su,yana budewa yan kananun passport din dake ciki suka fado be bi takansu burin sa kawai ya ga date ɗin ta dan suna yawan musun ta girme shi sanda suna makaranta.
Mamaki ne ya kamashi ganin hatta date da time na haihuwar su daya ne, be kula da sunan ba yana dariya ya rufe ya tsuguna ya tattaro hotunan guda biyu, cikin tsananin mamaki yake kallon hoton yana sake kalla, hoton Ammi ne da Daddy, duk da dadewar da akayi da daukar hoton wanda idan ba sanin su kayi sosai ba ba lallai ka gane su ba, a birkice ya sake bude file din ya shiga bin sunan ta dake rubuce cikin babban harafi
“AMINATU MD”
Sakin file din yayi ya fadi a wajen daidai lokacin da Aminatu ta fito daga dakin a shirye tana kiran Baba Altine, ganin shi tsaye cikin wani irin yanayi yasa ta ƙaraso da sauri tana tambayar sa menene, be tsaya bata amsa ba ya juya da sauri ya fice daga gidan zuciyar sa na wani irin harbawa.
Masha Allah…
Duk naga bayanan ku, kuma zanzo insha Allah da hukuncin hakan a musulunce, Nagode kwarai Allah saka da Alkhairi. Allah ya taimaka ya bamu Sa’a baki daya.
Rano DG*
35
★★★★★
Tsaye tayi cikin tarardadin abinda ya faru, sai kuma ta bi file din nata dake yashe kasa da kallo kafin ta tsuguna ta tattara komai tana sake dubawa.
Ledar daya ajiye gefe me tambarin Shoprite ta dauka ta bubbbude breakfast ne me rai da lafiya sai yar karamar red rose me kyau sosai, dan karamin note din dake ciki ya fado, murmushi ta saka
“I love you”
Aka rubuta da wani irin rubuth me matukar birgewa, wato ya zama baturen karfi da yaji kenan, wani iri ta dinga ji kamar tana tafiya akan gajimare.
***Yana fita ya shiga motar sa ya kifa kansa saman sitiyari, fuskar Aminatu da bata da maraba da ta Ammin sa ta shiga yi masa yawo a saman ƙwaƙwalwar sa, tsawon wannan lokaci ashe da Ammi take masa kama ya kasa ganewa sai yanzu, hoton fuskokin iyayen nasa ya dinga kokarin haɗawa da nasa dana Aminatu sai dai ko kusa babu digon kama da sukayi dashi, sau tari yakan tambaya kansa da wa yake kama cikin iyayen nasa ganin babu yasa ya bawa kansa amsar kila wasu ya biyo a cikin dangin nasu tunda dama hakan na faruwa.
Tunanin sa ne ya tsaya chak, idan har Aminatu diyar Daddy da Ammin sa ce, shi kuma fa da yake da shekaru da komai irin nata ballantana yace ko kanwar sa ce, ji yayi zuciyr shi ta sake karaya da kyar ya lallaba ya bar kofar gidan ba tare da sanin kowa ba ya bar garin domin yana da bukatar sanin komai.
Ammi na zaune tana kallon talabijin cikin daya daga cikin jerin kujerun alfarmar dake zagaye da babban falon nata, rashin yara na matukar damun ta, tun tana yawon asibiti har ta hakura ta daina, babu wata matsala ta kai tsaye da za’a kira ta dashi daya hanata haihuwa.
Yanayin yadda ya shigo mata a firgice yasa tayi saurin ta tashi zaune tana kallon sa.
“Kamal!” Ta Kira sunan sa, kallon ta yayi sai kuma yayi saurin tattaro nutsuwar, tunowa da yayi bazai bari kowa ya san komai ba har sai ya gano ainihin abinda yake faruwa yasa shi sakin fuskar sa sosai ya zauna kusa da ita yana dora kansa a saman kafadar ta
“Ammi nah.”
“Karka cemin dogon tuki kayi, ina Daddyn ya na ganka kai kadai?”
“Ammi ji nayi ina so nazo gida, ga Old Woman ta matsa shisa kawai na gudo gida Daddy ma be san na taho ba.”
“Maganar yarinyar ce har yanzu Kamal?”
“Ki taya mu da addu’a Ammi, komai zai daidaita.”
“Shikenan, amma gaskiya na soma gajiya da zaryar da kake tsakanin nan da chan, hanyar nan da babu kyau akwai risky.”
“Babu abinda zai faru In Sha Allah.”
“Allah yasa.” Ta amsa ba don taso ba.
Bedroom d’inta ya shiga, ya dubo dukkan takardun sa masu muhimmanci, ciki har da birth certificate d’insa original din, da address din asibitin da aka haife shi ya wuce dasu dakin sa.
Be zauna ba ya tafi wajen Hajiya Turai, har dare yana chan suna hirar su gwanin sha’awa sai dai rabi da kwatan hankalin sa baya wajen yana tunanin yadda zai soma binciken kansa ba tare da sanin kowa ba.
Sai data fara sauya shigar jikin ta sannan tayi masa text message gata nan ta fito, handbag dinta dake ajiye saman drawaer tayi nufin dauka bata ganta ba, dubawa ta hau yi kafin da kyar ta gano ta, ta kusa shigewa karkashin gado, ba tare da tunanin abinda ya kai jakar wajen ba ta tura wayar ta fito, duk basa falon hakan yasa tayi ficewar ta kai tsaye, bata bi takan driver dake gidan ba ta fita titi ta tari abin hawa ta fada masa inda zai kaita.