DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

Motoci biyu ne masu tsaron lafiyar Daddy sai motar da suke ciki su hudu wadda Farouk yake tukawa sai Uncle Aliiyu a gefen sa, Daddy da Alhaji Marwan na baya, tracker da Farouk ya sa mata a jikin jakar ta suke bi har zuwa sanda ta isa gaban building din da yake incomplete, saukowa tayi ta sallami me napep ɗin kai tsaye ta kutsa kanta ciki tana kokarin kiran number tasa.

A daidai lokacin ya saka Iman a gaba ta ƙatuwar wayar charger, ko ina na jikin ta duka ne beyi la’akari da kankantar shekarun ta ba, duk da yana bata abinci amma idan tayi mishi kuka dukan ta yake kamar ya samu babba, shigowar Amal wajen ya saki wayar hannun nasa yana dora hannun sa a saman bakin sa

“Shissh.” Da sauri ta hadiye kukan ta saka dukkan hannayen ta biyu ta rike saman bakin ta

“Daddy, yarinya ce fa.” Amal tace tana matsowa kusa da su

“Bani da time na tabbata by now Ali ya sanar dasu ina raye, ina so ki bawa Hajara wannan sakon, zata san yadda zatayi dashi.”

“Toh yarinyar fa?”

“Itace makamin da zan yi amfani na yaki Kabir da MD, ina bukatar dukiya ta, ina so komai ya dawo waje na, na maida su abin kwatance kamar yadda suka zalunce ni.”

“Idan har kana da damar hakan ba?”

Farouk ya shigo kai tsaye fuskar sa babu digon Rahma ko sassauci,kallon Amal gyatumin nata yayi cikin yanayi na tuhuma,

“Amal yaudara ta kikayi? Duk abinda nake ba saboda ke nake ba?”

“Bansan zai zo ba ai.” Tace tana matsawa gefe gami da riƙe hannun Iman

“Idan bake kika fada musu ba, ya akayi suka san nan?”

“Duk yadda kake kafkaf tsawon wannan lokaci baka taba tunani wannan ranar ba?”

Zai yi magana sai kuma hankalin sa ya kai kan jakar hannun ta

“You are good as nothing Amal.”

Yace ganin abinda ke jiki ba tare da ta sani ba.

Sosai hankalin sa ya tafi kan yar karamar kyakkyawar yarinyar dake tsaye tana raba ido, fuskar ta har dan tashi tayi saboda marin da take sha wajen Adam, babu tantama itace yar sa, yar da bata san mahaifin ta ba, very cute and innocent soul kamar Aminatun sa, takowa ya shiga yi yana zaro bindigar dake jikin gefen wandon sa daya karba wajen Daddy, kafin ya karasa Adam ya ciro tasa cikin zafin nama yayi kokarin riko hannun Iman, da sauri Amal ta hankad’a ta wajen Farouk yayi saurin riƙe ta yana sake dagowa.

“Amal!”

Ya ambaci sunan ta da dan karfi ganin abinda tayi masa, cikin zafin nama ya fizgota ya saita bindigar sosai a kanta

“Karka kuskura ka matso, idan ka matso zan saka bindiga na harbe ta har lahira.”

Kuka Amal ta saka cike da mamakin abinda mahaifin nata ke shirin aikatawa. Dariyar rainin hankali Farouk ya saka kafin yace

“Wa zakayi fooling? Yar ka ce fa. Idan ka ga dama ka kashe ta yanzu waya damu?”

“Ok.” Yace yana saita bindigar sosai yana kokarin jan kunamar bindigar Daddy ya dakatar dashi.

“Me kake bukata? Me kake so damu Adam? Me muka yi maka haka?”

“Ita tsohuwar bata fada muku abinda tayi min ba?”

“Yanzu me kake so?”

“Duk abinda kuka dade kuna tarawa, ina nufin dukiyar ka baki daya data MD, shine kadai zai fanshi duk abinda kukayi min .”

“Kazo muje gida a zauna sai a san yadda za’a bullo wa al’amarin, hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar Adam.”

“Ni na dade da sa gatari na yanke nawa, bani da alakar komai daku, babu abinda nake so fiye dana ga kun wulakanta, wulakanta mafi kaskanci.”

“Daddy wanda yayi nisa baya jin kira, koma me akayi masa ya kamata ya zama mai yafiya, ka daina lallaba shi ba zai taba fahimta ba.”

“Farouk kai yaro ne, Adam zaka karbi tayina kazo muje gida mu yi sulhu?”

“Har abadah.” Yace yana sake riƙe bindigar sa sosai akan Amal dake kuka sosai har da majina.

“Well then, bani da zabi face na yake ka.”

Yace yana nuna wa yaran sa hannu, kafin kace me sun zagaye Adam sun saka tsakiya,

“Retreat or die!”

Dariya ya saka

“Ka zata bani da cover, baka taba mamakin yadda na iya surviving this long years ba tare da na taba haduwa da wani ba, while I’m leaving right under ur noses? Ba kayi tunanin hakan ba? Adam bazai taba kamuwa cikin sauki ba, hatsibibine ni fiye da yadda kake tunani, sannan yanzu zamu fara wasa, best of luck Gen!”

Daga sama aka rufe su da kasa, nan da nan idon su ya rufe ruf kowa ya hau kici-kicin yadda zai ya kare idon sa, a lokacin ya samu ya gudu ba tare da sun ankara ba, sai da komai ya lafa suka neme shi suka rasa ya gudu.


A mota Farouk be iya tuki ba dole daya daga cikin sojojin suka karbi tukin ya rike Iman da ta galabaita sosai, Amal na gefen sa ta cusa kanta tsakiyar kafar ta tana faman shassheka, haushi da bacin rai kukan nata ke kara masa,ji yake kamar ya ce su tsaya a sauke ta.

Kai tsaye asibiti suka wuce da ita, domin tana bukatar a duba lafiyar ta. Sosai ta galabaita da yawan kukan da take sai rashin abinci ne suka haɗar mata, gashi da alama sauro yayi mata mugun cizo da har ya saukar mata da zazzaɓi me zafin gaske. Drip aka daura mata da allurai sannan aka gyara mata wajen da duk taji ciwo. A gefe Amal ta rakube bayan su Daddy sun tafi, Farouk be sake bin ta kanta ba ya shige dakin da aka kwantar da Iman din yaja kujera ya zauna ya zuba mata ido, babu abu daya daya raba ta dashi har duhun fatar shi dauka, idanun ta ne kawai irin na Aminatu da dan karamin bakin da zakayi tunanin karamin chokalin tea ne kaɗai zai iya samun sukuni shiga ciki.

Sosai ya shagala da kallon ta yana jin farin ciki mara misaltuwa, da zarar ta dawo daidai zai kwashe su su bar kasar ba zai iya zama ba, dan ya lura fadan na su Daddy me karfi ne dan haka bazai yarda a kara involving rayuwar aaminatu ko Iman ba.
Wayar sa ya ciro ya lalubo number ta, tana bukatar sanin halin da ake ciki ko dan lafiyar ta ita ma.
A lokacin zaune Aminatu take ta kunna karatun suratul Bagra tana saurara, sau uku kenan tana kiran Kamal baya picking sai ta hakura ta bari ta sake gwadawa anjima, saboda haka data ji karatun ya tsaya alamun shigowar kira ta zata shine. Number data gani a saman screen din ta sakata komawa ta lafe sosai a jikin katitar kafin ta daga

“Ina miki albishir da na cika alkawari, gani ga Iman.”

A zabure ta mike

“Dan Aallah!”

“Allah.” Yace cike da gamsarwa

Sai ta saka kuka

“Kukan me? Ke da zaki gode wa Allah.”

Da sauri ta kai goshin ta k’asa cike da farin ciki tayi wa Allah godiya kafin tace

“Kuna ina yanzu? Lafiyar ta kalou? Me ya sameta?

“Duk wannan tambayoyin? Muna nan premier clinic an sa mata ruwa.”

“Owk gani nan.” Tace da sauri tana kashe wayar.

“Baba!” Ta kwala Kira

“An ga Iman.”

“Alhamdulillah, Alhamdulillah.”

“Dauko hijabin ki muje suna asibiti.”

“Ina jiran ku a mota.” Yace yana juyawa.

“Yaushe Ya Anas yazo?”

“Sanda kika fara waya, yana tsaye nace ma ya shigo falon yaki yace na miki magana.”

“Ok.” Tace tana yin gaba.


Da kallo yabi motar kafin ya kada kansa yana kara waya a kunnen sa

“Itace?”

“Ok done!”

Yaja motar ya bar layin.

***Kamar kurame babu wanda yayi wa wani magana har suka isa Asibitin, tambaya sukayi aka nuna musu dakin, da Amal suka fara gamuwa tana daga kofar dakin akan wani benci ta kasa shiga ciki, sallama sukayi mata ta dago tana kallon su, amsawa tayi ta maida kanta gefe.

Idon sa akan kofa yaji an turo, idanun su ne suka hadu waje daya, tayi saurin janye nata ta isa gaban gadon da sassarfa, kuka ne ya taso mata tayi kokarin tsaida shi sai dai duk da haka sai da ya zobo, Baba Altine ce ta karasa cike da jimami take kallon Iman din

“Allah sarki.”

Cikin takun kasaita ya shiga takowa har ya iso gaban su, kallon kallo sukayi wa juna kafin Farouk ya dauke kansa yana jan karamin tsaki, hannu Anas yasa ya dafa kan Iman din akayi saa kuwa ta bude idon ta,tana ganin shi ta saka kuka tana kiran Abba tana mika masa hannu.

“Yi shiru kinji my angel.” Yace yana shafa kanta

Riko hannun Aminatu tayi dana Anas tace

“Karku tafi ku barni kai da Ummi, kullum sai nayi kuka yayi ta min masifa kuka ki zuwa ku tafi dani.”

“Karki damu kinji? Ba zamu kuma barin ki ba.”

Sosai ran Farouk ya bci, ya hade girar sama data kasa ya shiga watsa ma Anas harara, ita kanta Aminatu bata bi ta kansa ba kamar ma ta manta dashi a wajen, murya ya shak’e yace

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button