DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ba’a wa yaro hayaniya aka musamman wanda ba lafiya ce dashi ba, tana bukatar hutu an gode da dubiya.”

Sarai Anas ya gane dashi yake, be kula shi ba ya sake shafa kan Iman din

“Baby Bari na dauko miki chocolate a mota ?”

“Uhum uhum..Karka ki dawowa.”

“Zan dawo yanzu kinji?”

Daga mishi kai tayi tana lumshe ido

“Ina so muyi magana.” Yace yana duban Aminatu, kallon Farouk tayi da sauri taga yadda yayi, fuskar nan tasa kamar wuta haka ya tamke ta.

“Baki ji bane Aminatu, yayanki Anas yana so kuyi magana.”

Baba Altine tayi tsagal, yaki Aminatu tayi ta tashi da nufin bin sa dan tuni yayi hanyar fita Farouk yasa hannu ya finciko ta da karfi har sai da glass din idon ta ya cire ta fado jikin sa. Da hannu ya nuna ta cikin bacin rai yace

“Karki manta akwai igiyar aure na akan ki, ke idan ma babu ban yarda ki kebe da wani gardi ba wallahi, zan baki mamaki idan kikayi gigin aikata haka.”

“Idan kai ne ka haife ta sai ka hana, dame kake takama ne wai?”

Anas ya katse shi a hasale, da hannu Farouk yayi masa nuni da Iman dake kwance

“Kaga abar da nake takama da, ba kuma zaka taba samun irin ta ba har abadah sai dai abi wani sarkin.”

Cikin bacin rai Anas ya bar dakin, ko motsi Aminatu batayi ba, ita mamakin yadda Farouk ya zama take, kamar ba Farouk dinta na baya ba me saukin kai da son mutane ba.


Duk tsare tsaren da zaiyi ya gama shi, hatta address din asibitin da komai ya gama haɗawa waje guda, baya so Ammi tasan shirinsa saboda haka sai yayi mata karyar Kano zashi akan wasu harkokin Daddy da yake so ya fara duba wa, sosai taji dadi ta bishi da addu’a.
Kai tsaye tasha ya nufa karo na farko a rayuwar sa daya shiga motar haya, kamar akan kaya haka yake jin sa, sai dai bashi da wata hanya sai hakan. Kano suka fara zuwa kafin ya kuma samun wata motar zuwa Katsina.

Madam Inno???? na zaune ta zabga uban tagumi tunanin rayuwar baki daya take, abubuwa da yawa sun faru, wasu ma nakan faruwa ciki har da yanayin da suke ciki yanzu na matsi da babu, duk jarin nata ya kare, ta dawo ta tsuguna sauran mazan gidan ne ke kokarin taimaka musu wani zubin da abinda zasu ci.
Nan da chan bata iya zuwa saboda yadda abinda ya faru ya gama zagaye ko ina na kauyen hatta ƙananan yara sau tari idan ta fita sai dai taji suna maganar hakan yasa ta tattara fitar baki daya ta watsar ta zauna ta fawwala Allah komai tana cigaba da jinyar Baba da ke cikin mawuyacin hali tsawon wannnan shekarun babu wani sauki sai godiyar Allah.


Yinin yau baki daya be duba wayar sa ba, aiki suke sosai akan wani kamfanin man gyada da yake son budewa a Niger, rabon da su hadu da Daddy yau kwana biyu kenan, shima ya zama busy sosai yana shirye shiryen ritaya ma saboda ya tattara hankalin sa waje guda, tun bayan abinda ya faru basu sake maganar Adam ba, sun barshi a matsayin ihu bayan hari ne kawai amma babu abinda zai iya, sun tuntubi Dadah da maganar tace su sake nata lokaci dole suka tattara suka ajiye komai.
Bayan ya gama duba komai ya tattare su waje guda, sakatariyar sa ya kira ya bawa ta kai office din Admin human resources sabida yana so komai ya kankama.
Babbar rigar dake jikin sa ya cire ya rataye ta a saman hanger kafin ya isa gaban dispenser ya tsiyayi ruwa ya sha sosai, sannan ya koma ya zauna yana jawo wayar tasa domin suba sakonni. Karon farko daya ji zuciyar sa tayi wani irin bugawa da karfin gaske, yasa hannu ya dafe ta yana kara bude idaon sa sosai akan sakon.

“50million na dan ka dake amsa sunan ka KAMAL MARWAN DIKKO , 100million kuma na yar da baka san tana rayuwa ba, wadda jinin ka ke yawo a cikin jijiyoyin jikin ta, bata san kanta ba, bata san wacece ita ba,tayi rayuwar kunci da bakin ciki duk ta sanadi na.”

“Dukkan wannan zabi ne ya rage naka ka zaba, idan kuma ba zaka iya sadaukar da million 150 ga yayanka ba, ina fatan zaka iya sadaukar da matar ka ba tare da sisin ka tayi kuka ba. Zabi ya rage ga shiga rijiya!” Adam

Rano ????????????DG*

               36

★★★★★

Number ya kira da sauri, ringing d’aya aka daga

“Adam, kana jina?” Yace jikin sa na rawa

“Ina jinka.” Ya amsa a gadarance

“Yawwa, me kake nufi da sakon nan? Ban gane komai ba, me hakan ke nufi.”

“Ina da tabbacin kai cikakken bahaushe ne ko? Lokacin boye boye ya kare ina so kaje kayi bitar abinda ka karanta da kyau zaka gane inda maganganun suka dosa, sai dai ka sani rayuwar Kamal na cikin hatsari, haka ma rayuwar yar ka da ni kadai zan iya tabbatar da hakan.”

“Ya…” Katse kiran yayi ba tare da ya jira abinda zai ce ba, hanyar fita daga office din Alhaji Marwan yayi yana kokarin neman number Kamal, a kashe take cikin tsananin tashin hankali ya juya akalar kiran zuwa ga Ammi, fitowar ta kenan daga banɗaki taji wayar ta dake saman mirror na neman agaji, karasa wa tayi ta dauka

“Ina Kamal?” Yace a kid’ime

“Be dade da tafiya ba ai, na zata kunyi magana dashi kafin ya tafi, wani aiki ka bashi?.”

“Ina ya tafi? Ban aike shi ko ina ba, be kuma fada min inda zashi ba, subhanallah!”

“Me ya faru?”

“Ina zuwa.” Yayi saurin katse kiran yana neman layin Daddy

Hankalin ta ne ya tashi ta hau kiran layin Kamal din sai dai duk a kashe, tunanin Aminatu ne ya fado mata, bata raba daya biyu yarinyar ce tasa shi tafiya ba tare da izinin mahaifin shi ba, sannan yayi mata karya akan aikin Daddy xai je yayi, take tsanar yarinyar ya shiga zuciyar ta, ta hau zagaye a dakin tana tunanin mafita, alk’awari tayi ma kanta idan wani abu ya samu danta ba zata taba barin ta ba.

Gaba daya Alhaji Marwan ya birkice wa Daddy, tunanin sa kar wani abu ya samu Kamal d’insa, dan be san yadda zai iya dauka ba, a gefe guda kuma tunanin wacce yar tashi Adam yake nufi, iya sanin sa bashi da wata ‘ya kawai Adam naso yayi wasa da hankalin sa ne tunda ya riga yasan tun bayan haihuwar Kamal din Ammi bata sake ko da batan wata bane, shiyasa kawai ya share maganar fatan sa kawai ya samu Kamal a waya yaji inda yake dan kwarai ya fara tsorata da lamarin Adam,ya soma tunanin komene akayi masa haka toh me girma ne a wajen sa.


Isar su Katsina ana ta kiraye kirayen sallar isha’i, hotel ya samu ya sauka da nufin da safe ya karasa garin na Shagari, baya jin dadin komai burin sa ya gano wani abu da yake da alaka dashi da Aminatu.
Be wani iya baccin kirki ba da sassafe ya shirya ya fita, asibitin ya fara zuwa da yake shi ba a cikin garin yake ba, ya tarar da wani mutum a reception, sallama yayi masa gami da mika masa hannu sukayi musabiha kafin yace

“Wani muhimmin abu ne ya kawo ni, takanas daga Abuja, ina fatan zan samu information din da nazo nema.”

“Ok me kake bukata?”

“A asibitin nan aka haife ni, ga date nan da komai a jikin birth certificate d’ina, idan babu damuwa ina so ka binciko min file din da mukayi amfani dashi sanda muke zuwa Asibitin.”

“Menene file number din?”

“0023.”

“Ok ka dan zauna mu binciko shi, an kwana biyu zai danyi wuya.”

“Owk.” Yace yana samun waje.

Yana zaune mutumin ya dawo, hannun sa ya kalla ganin babu file din yasa shi cewa

“Ba’a samu ba ko?”

“Wallahi ba’a samu ba, abin mamaki duk daadewa ba’a rasa file amma wannan babu shi kwata-kwata.”

“Dama nasan ba za’a samu ba. Amma dan Aallah ko zan iya sanin adadin mutanen da aka haifa a asibitin nan ranar da aka haife ni?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button