DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

DAURIN GORO COMPLETE HAUSA NOVEL

“Da kamar wuya gaskiya, kaga an jima kuma mu ba wai muna da record bane cikin computer, manually ake komai dan haka gaskia ba zai yiwu ba.”

“Idris ina aka ajiye file din Samira ne?”

Maganar ta ta riga ta ƙarasowa wajen, babba ce a kalla zatayi kusan sa’ar Ammi, kallon kamal tayi kadan kafin ta maida hankalin ta wajen wanda ta kira da Idris din tana masa magana,

“Wallahi Sister Asibi bansan inda aka sashi ba, ko yana wajen Lawal a tambaye shi.”

“Sister Asibi?”

Sunan ya shiga masa yawo aka, idan har be manta ba shine sunan da ya gani akan file din Aminatu, sannan shine same sunan dake jikin nasa takardar, da sauri ya ciro ta ya duba, hakan kuwa ne, murmushi yayi ya bita da sauri ganin har ta kusa shiga wani office

“Dan Allah tambaya ce dani.”

Ja tayi ta tsaya tana duban sa

“Ya akayi ɗan saurayi?”

“Am nidai sunana Kamal Marwan Dikko…”

“Anan aka haife ni, ranar 5 ga watan February, 1996.”

“Kaga akwai ayyuka da yawa kaina, ina ganin ka nemi wani sai kayi masa bayani.”

Tayi gaba da sauri, shan gabanta yayi yana bata rai sosai ganin da gaske so take ta gujewa maganar dan tun sanda ya ambaci sunan sa ta nuna alamun tsoro a idon ta

“Ki tsaya muyi magana ta fahimta kafin na sanar da hukumar asibitin, kece kika karbi haihuwa ta ko? Dan sunan ki ne a rubuce jikin takardar haihuwa ta.”

“Shigo ciki.”

Tace tana yin gaba, bin bayan ta yayi har wani office, suna shiga ta rufe kofar tana kallon shi

“Me kake so?”

“Ina son sanin waye ni? Me yasa sunana yayi daidai da na wadda aka haife mu rana daya, lokaci daya da ita, me hakan ke nufi?”

“Kai zan tambaya dan ban gane me kake nufi ba.” Tace tana juya masa baya, murmushi yayi me ciwo kafin yace

“Ina bukatar sanin gaskiya, karki boye mun komai ki sanar dani, idan kuma ba haka ba…”

“Me kake so ka sani?”

“Waye ni? Wacece Aminatu? Ko ana so ace min mistake akayi wajen rubuta mana sunan mahaifi daya bayan an haife mu a lokaci daya a rana daya kuma asibiti daya? Ko ana so a cemin mu ɗin yan biyu ne, nasan ana iya samun suna iri daya, sai dai ba irin namu ba, hoton Daddy da Ammi dake jikin file dinta fa? Shima kuskure ne? Ba zai taɓa yiwuwav ba.”

Hadiye yawu tayi me kauri ganin yadda yaron yake so lallai sai ya tono abinda ya dade da shudewa, abinda ta aikata wanda ta jima tana dana sanin amincewa zuciyar ta da tayi, kwanakin baya Inno da kanta tazo mata da rokon ta sanar da ita ko da address din inda aka kai mata dane, amma ita kanta bata sani ba.
Idon sa ne yayi ja sosai, ya sake duban ta a karo na ba adadi

“Shirun ki na nufin wani mummunan al’amari ya faru a ranar da aka haife mu, shirun ki ya tabbatar min da…”

“Tabbas nayi kuskure wajen amincewa zuciya ta, nayi dana sani mara amfani, ban taba tunanin wannan ranar zata zo ba.”

“Kayi hakuri Kamal, tabbas mun zalunce ka zalunci me yawa, sai dai akan Aminatu kai gata mukayi maka, tun bayan lokacin ban sake haduwa dasu ba, sai dai har zuwa yanzu ina rayuwa ne da tunanin makomata.”

“Me kike nufi?” Yace cike da dauriya dan zuwa lokacin zuciyar sa ta fara shiga mawuyacin hali

“Nice na chanja ka da Aminatu, nice sanadiyyar zaman ka duk abinda ka zama a yanzu, kuma nice sanadiyyar saka Aminatu a cikin mawuyacin hali, ba tare da sanin mahaifanta ba,son zuciyar mahaifiyar ka shine mafarin komai, da bata amince ba babu yadda zatayi hakan ta yiwu tunda ita lafiya lau ta haife ka tasan me ta haifa.”

Dip ya daina ji kwata kwata, tsawon dakika biyar tana cigaba da jera masa bayanin da baya iya jin komai, a hankali jin sa ya soma dawowa, jiri ne ya kwashe shi yayi saurin dafa bangon office din, da sauri ta sa hannu zata tare shi ta dakatar da ita

“Menene kwatancen gidan?”

“Idan kaje ka tambayi gidan Inno babu wanda be santa ba.”

“Waye ya saki aikata mana wannan mummunan aiki?”

“Bansan shi ba, sai dai na san sunan sa a lokacin da naji matar ta fada masa, Adam idan har ban manta ba, shi ya bamu kudi domin mu yi masa wannan aiki, ni, harira da mahaifiyar ka sai mace daya da suka zo tare, wadda ta zama wakiliyar sa dan ita muka sani bashi ba .”

Girgiza kansa yayi cikin sarkewar murya wanda yake jin numfashin shi na kokawa da gangar jikin shi ya soma magana

“Allah ya isa tsakanin mu daku, bazamu taba yafe muku abinda kukayi mana ba, ina rokon Allah ya wulakanta ku tun a duniya, ya bi mana hakkin zaluncin da kukayi mana.”

Kofa ya nufa yana layi, kafin ya juyo yace

“Ki jira abinda zai biyo baya dan ba zan yafe miki ba, Shari’a ce zata raba mu.”

“Dan girman Allah ka tsaya ka saurare ni.”

Bugo kofar yayi da karfi, ta zauna dabas a kasa tana rike kanta, ina zata kama? Shari’a da Marwan Dikko ba abu ne me sauki ba tasan tabbas zai iya sakawa a rufe kaf dangin ta. Da sauri ta mike ta zari jakar ta ta fita da kofar baya.

***Da taimakon wani direbab mota daya dauka shata suka isa cikin garin, duk da dauriya kawai yake yi amma bashi da karfi da kuzarin tunkarar abinda yake tunkaro shi din. Tambaya sukayi aka nuna musu gidan, da ido ya shiga duban gidan da ya sake lalacewa ainun, yanzu mutane ne ke rayuwa a ciki? Ya tambayi zuciyar sa, a take ta bashi amsa da mutanen ma iyayen da suka kawo ka duniya, chije bakin sa ya yi ya fitar da iska mai zafi yana tuna girma da kyawun gidan su na Abuja, tabbas Aminatu ita aka cuta, aka sata rayuwa a muhallin da har ta bar duniya ba zata taba rayuwa a cikin sa ba, kwalla ce ta zubo masa yasa hannu ya goge.

“Sannu da zuwa.”

Nura yace yana fitowa daga cikin gidan, saurin daidai ta kansa yayi ya mika masa hannu,tunanin Abinda zai ce mishi yake, sai yaji yace

“Wa ake nema?”

“Nan ne gidan su Aminatu?” Yace

“Nan ne, kana da labarin inda take ne dan Allah?” Ya amsa cike da zumudi,

“Zan iya ganin mahaifiyar ta?” Yace yana dauke wanchan maganar

“Bismillah shigo ciki.” Yayi gaba da sauri, dan jim yayi kadan kafin ya kutsa kansa cikin makeken zauren gidan daya cika da yana.

“Inna, inna fito ga wani yazo ganin ki kuma da alama yasan inda Aminatu take.”

“Yana ina?”

Ta tashi a zabure, tsaye yayi a bakin kofar ya kasa karasowa ciki, wannan itace mahaifiyar sa data zabi kudi akan sa, mahaifiyar data raini Aminatu a cikin kaskanci da tozarci bayan nata dan na cikin gata da jin dadi

Sararo tayi tana kallon sa, cikin sakannin da basu gaza biyar ba, ta kare masa kallo, kallon daya tabbatar mata da zargin ta, da sauri tayi kansa tana duban damtsen hannun sa dake bude cikin riga me gajeren hannun daya sa, katon tabon da aka haife shi dashi wanda shine abu na farko data fara gani sanda yazo duniya ta shiga bi da kallo, da hannu ta shiga nuna shi sai dai ta gaza furta kalma daya, tana kokarin riko hannun nasa yaja baya da sauri

“Kamal MD kamar yadda kike hasashe! Ina fatan kina cikin koshin lafiya bayan abinda kika aikata.”

“Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, shine dana wallahi shine, wallahi shine.”

“Inno me kike fad’a, ni ban fahimci komai ba fa.”

Cigaba da matsowa tayi tana kokarin riko shi yayi saurin ja baya yana bata fuska sosai

“Karki taba ni, karki fara! Ba abinda ya kawo ni kenan ba, ina so naga kalar rayuwar da kike yi, alhamdulillah na gani, yanzu zan koma inda na fito.”

Yana kaiwa nan yayi waje da sauri, biyo bayan shi tayi tana kwala kiran sunan shi amma ko waiwayowa bai yi ba, motar ya fada da sauri ya umarci me motar su tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83Next page

Leave a Reply

Back to top button